Tuesday, 11 September 2012

HUKUNCE-HUKUNCE AZUMI

WASU HUKUNCE-HUKUNCE NA AZUMI DA IDI **** IBRAHEEM MUSA بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ الْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ، وَأَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، وَأَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّداً عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَعَلَى آلِهِ وَأَصْحَابِهِ، وَمَنْ تَبِعَهُمْ بِإِحْسَانٍ إِلَى يَوْمِ الدِّينِ. MAUDU'I SHAFI KAN ME SHARI'A TA RATAYA DAUKAN AZUMI DA AJIYE SHI? ……… 2 KO WACE KASA ZA TA YI AMFANI NE DA GANIN WATANTA BA WAI DA GANIN WATAN SAUDIYYA BA …………………………………………... 2 WA KE DA HAKKIN BAYYANAR DA RANAR FARA AZUMI KO AJIYE SHI? ……………………………………………………………………………….. 2 SHUGABA BA YI DA DAMAR YA CE: DAGA LOKACI KAZA NA RUFE KARBAN LABARIN GANIN WATA ………………………………………….... 3 MENE NE AZUMI? ……………………………………………………………….. 4 MENE NE HUKUNCIN AZUMI? ……………………………………………….. 4 WACE SHEKARA CE AKA FARLANTA AZUMIN RAMADAN? ……………4 FALALAR DA TAKE CIKIN SHAR'ANTA AZUMI …………………………... 4 SHARADIN WAJIBCIN AZUMI ……………………………………………….. 5 LADUBBAN AZUMI ……………………………………………………………. 5 ABUBUWAN DA SUKE BATA AZUMI …………………………….. …………. 6 HUKUNCE-HUKUNCEN ZAKKAR FIDDA-KAI …………………………….. 6 HUKUNCE-HUKUNCEN RANAR IDI …………………………………………. 6 KAN ME SHARI'A TA RATAYA DAUKAN AZUMI DA AJIYE SHI? Shari'a ta rataya daukan azumi da ajiye shi, da yin idin Azumi da idin Layya a kan ganin jinjirin watan Ramadan da Shawwal da Zul hijja. Imamul Bukharii ya ruwaito hadithi na 1,909, da Imam Muslim a hadithi na 1,081 daga Abu Huraira ya ce: Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce: ((Ku yi azumi saboda ganinsa, ku ajiye azumi saboda ganinsa, in ya boyu gare ku, ku cika adadi)). Sannan Imam Ahmad ya ruwaito na hadithi na 18,895 cikin Musnad, da Imamun Nasa'I hadithi na 2,426 cikin Sunan daga Abdurrahman Bin Zaid Bin Khattab ya ce: ((Ni na zauna da sahabban Manzon Allah mai tsira da amincin Allah, kuma na tambaye su, sannan sun gaya mini cewa: Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce: ku yi azumi saboda ganinsa (shi watan Ramadan) sannan ku sha ruwa saboda ganinsa (shi watan Shawwal) sannan ku yi yankan (layya da hadaya) saboda ganinsa (shi watan Zul hijja) in kuma ya boyu gare ku sai ku cika kwana talatin, in kuma masu shaida biyu suka ba da shaida, sai ku yi azumi kuma ku sha ruwa)). Intaha. Sheik Albanii ya inganta hadithin cikin Irwa'ul Galiil 4/16. KO WACE KASA ZA TA YI AMFANI NE DA GANIN WATANTA BA WAI DA GANIN WATAN SAUDIYYA BA: Ko wace kasa za ta yi amfani ne da ganinta ba wai da ganin mutanen Saudiyya ba, saboda hadithin Kuraib da ya zo cikin Sahihu Muslim hadithi na 1,087 cewa: ((Kuraib ya ce: Ummul khair 'Yar Harith ta aike ni zuwa Sham wurin Mu'awiya, Kuraib ya ce: sai na je Sham na biya bukatarta, watan Ramadan ya tsaya alhali ina Sham na ga jinjirin wata a daren juma'a, sannan da na dawo Madina a karshen watan, sai Abdullahi Dan Abbas ya tambaye ni ya ambaci jinjirin wata ya ce: yaushe ne kuka ga jinjirin wata? Sai na ce: daren juma'a, sai ya ce: kai ka gan shi? Sai na ce: na'am, mutane kuma sun gan shi, kuma sun yi azumi, Mu'awiya ma ya yi azumi. Sai ya ce: mu kam mun gan shi ne a daren asabar, ba za mu gushe ba muna yin azumi har sai mun cika talatin ko kuwa mu gan shi. Sai na ce: ba za ka wadatu da ganin Mu'awiya da kuma azuminsa ba? Sai ya ce: a'a haka dai Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya umurce mu)). Sheik Abdul Aziz Bin Baz ya ce cikin littafin Majmu'ul fatawa 15/85 ((Majalisar manyan Malaman Saudiyya ta fidda matsayar cewa: ko wace kasa ta yi amfani da ganin watanta, saboda hadithin da Abdullahi Dan Abbas ya ruwaito, da kuma hadithan da suke karfafa ma'anarsa)). Intaha. WA KE DA HAKKIN BAYYANAR DA RANAR FARA AZUMI KO AJIYE SHI? Abin da aka sani a cikin Shari'ar Musulunci ahi ne: Sarkin Musulmi watau أَمِيرُ الْمُؤْمِنِينَ ko wakilinsa shi yake da hakkin bayyanar da ranar Idi a kasarsa, a duk lokacin da ganin wata ya tabbata a wurinsa ta daya daga cikin hanyoyin tabbatar tsayuwar wata a cikin addinin Musulunci. Wannan kuwa saboda abin da ya zo ne cikin hadithan Annabi mai tsira da amincin Allah kamar hadithi na 2,342 cikin Sunani Abi Dawud, da na 1,691 cikin Sunanid Darimii, da kuma Sunanud Dara Qudnii 2/156 sannan Albanii ya inganta shi cikin Irwa'ul Galiil 4/16 daga Abdullahi Dan Umar cewa: ((Mutane sun dubi jinjirin wata sai na ba wa Manzon Allah labarin cewa na gan shi, sai ya yi azumi, ya kuma umurci mutane da su azumce shi)). Da kuma hadithi na 1,339 cikin Sunanu Abi Dawud, na 8,447 cikin Sunanul Baihaqii, kuma Albanii ya inganta shi cikin Sahihu Sunani Abi Dawud 2/54 daga Rib'ii Dan Hirash daga wani cikin Sahabbabn Manzon Allah cewa: ((Mutane sun yi ta sassabawa a karshen Ramadan sai wasu kauyawa biyu suka zo suka ba da shaida a gaban Annabi mai tsira da amincin Allah cewa: wallahi wata ta tsaya jiya da yamma, sai Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya umurci mutane da su sha ruwa)). Intaha. Kun ga a nan Annabi ne a matsayinsa na shugaban jama'a yake ba da umurnin daukan azumi da ajiye shi. Sannan Abdullahi Dan Imam Ahmad ya ce cikin littafin Masa'ailu Ahmad bi riwayati Abdillah 2/610-611: ((Na tambayi babana game da ganin jinjirin wata idan mutum daya ya ba da shaidar ganinsa? Sai ya ce: Sarkin Musulmi sai ya umurci mutane da yin azumi)). Intaha. Sannan Ibnu Rushd Al-jad ya ce cikin littafin Almuqaddimat 1/251: ((Idan ganin jinjirin wata ya tabbata a wurin Sarkin musulmi da shaidar adilai biyu to, sai ya umurci mutane da yin azumi da yin idin azumi, kuma ya tilasta wa mutane yin hakan)). Intaha. Sannan Ibnul Qayyim ya ce cikin littafin Zadul Ma'ad 2/49 ((Yana daga cikin al'adar Annabi mai tsira da amincin Allah umurtan mutane da yin azumi idan Musulmi daya ya ba da shaidar ganin watan Azumi, da kuma umurtansu da yin sallar Idi idan Musulmi biyu suka ba da shaidar ganin watan Shawwal)). Intaha. Sannan Ibnu Abidiin ya ce cikin littafin Hashiyatu Raddil Muhtar 2/388: ((Ingantacciyar magana ita ce: harkar tabbatar jinjirin wata abu ne da ake jingina shi zuwa ga Sarkin musulmi, duk lokacin da ganin wata ya inganta a wurinsa, kuma shaidu suka yawaita to sai ya yi umurni da a yi azumi)). Intaha. Sannan Sheik Bin Baz ya ce cikin littafin Majmu'ul Fatawa 15/97: ((Amma su daidaikun musulmi wajibi ne a kan su, su yi azumi ko su sha ruwa a lokacin da shugabanninsu suka ce a yi haka, saboda hadithin Manzon Allah mai tsira da amincin Allah: "Azumi shi ne ranar da kuke azumi, Idin karamar salla ranar da kuke Idin karamar salla, Idin layya ranar da kuke Idin layya")). SHUGABA BA YI DA DAMAR YA CE DAGA LOKACI KAZA NA RUFE KARBAN LABARIN GANIN WATA: Kamar yadda shari'ar Musulunci ta fawwala wa Sarakunan Musulmi tabbatar da ganin jira-jiran wata a cikin kasashensu kuma ta ba su damar umurtan kowa da kowa cikin jama'arsu da yin Azumi ko Idi, kuma ta wajabta wa jama'a su yi musu biyayya. To haka nan ita Shari'a ta wajabta wa Sarakunan kasashe su zamanto masu aiki da ilmin shari'a cikin wannan hakki da Shari'a ta ba su, su zamanto masu koyi da Annabi mai tsira da amincin Allah, idan sun yi hakan to, babu abin da zai cutar da su Duniya da Lahira. Lalle Annabi ya kasance kofofinsa a bude suke ga dukkan mai ba da labarin ganin wata ba yi da wani lokaci da zai ce yanzu ya rufe karban labarin ganin wata matukar ganin watan bai riga ya tabbata a wurinsa ba. Kuma da zarar shaidar ganin wata irin ta shari'a ta tabbata a gaban Sarkin musulmi, to ya gaggauta aiki da ita kada ya damu da yabon mai yabo ko zargin mai zargi. Wannan shi ne hanyar Annabi mai tsira da amincin Allah, sabanin wannan shi ne rudu da rashin sanin inda Shari'a ta sa gaba, Allah Ya tsare. MENE NE AZUMI? Azumi yana nufin: Barin cin abinci, da shan ruwa, da jima'I tun daga bullowar alfijir har zuwa faduwar rana, da niyyar yin ibada. MENE NE HUKUNCIN AZUMI? Azumin Ramadan farilla ne saboda shi daya ne daga cikin rukunan nan biyar na addinin Musulunci, sobda fadar Allah Madaukakin Sarki cikin Surar Baqara aya ta 183 ((Ya ku wadanda suka yi imani! An wajabta muku azumi kamar yadda aka wajabta (shi) a kan wadanda suke daga gabaninku, saboda tsmmanin za ku tsare)). Da kuma fadar Manzon Allah mai tsira da amincin Allah cikin Bukhari hadithi na 8 da Muslim hadithi na 16 daga Abdullahi Dan Umar cewa: ((An gina Musulunci a kan abu biyar: Shaidar babu abin bauta bisa cancanta sai Allah sannan Muhammad manzon Allah ne, da kuma tsaida Salla, da ba da Zakka, da Hajji, da kuma Azumi)). WACE SHEKARA CE AKA FARLANTA AZUMIN RAMADAN? An farlanta azumin Ramadan ne a shekarar hijira ta biyu, kamar yadda ya zo cikin littafin Assiratun Nabawiyya na Ibnu Katheer 2/546, da littafin Arrahiqul Makhtuum shafi na 194. FALALAR DA TAKE CIKIN SHAR'ANTA AZUMI: Lalle Watan Ramadan wata ne mai yawan falala, daga cikin abin da yake nuna falalar wannan wata, akwai fadar Allah Madaukakin Sarki cikin Surar Baqara aya ta 185 ((Watan Ramadan ne wanda aka saukar da Qur'ani a cikinsa yana shiriya ga mutane da hujjoji bayyanannu daga shiriya da rarrabewa. To wanda ya halarta daga gare ku a watan sai ya azumce shi, kuma wanda ya kasance majinyaci ko kuwa a kan tafiya to sai ya biya adadi daga wasu kwanuka na dabam. Allah Yana nufin sauki gare ku, kuma ba Ya nufin tsanani gare ku, kuma domin ku cika adadi, kuma domin ku girmama Allah a kan Ya shiryar da ku, kuma tsammaninku za ku gode)). Yana daga cikin falalar azumi ganin irin yadda yake kankare zunubban da suka gabata: Imamul Bukharii ya ruwaito hadithi na 2,014 da Imamu Muslim hadithi na 760 daga Abu Hurairah cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce: ((Duk wanda ya yi azumin Ramadan saboda imani da neman lada to, an gafarta masa abin da ya gabata na zunubinsa)). Yana daga cikin falalar azumi ganin yadda Allah Madaukakin Sarki Ya ce Shi da kansa ne zai biya mai yin azumi ba tare da Ya iyakance ladan da zai ba shi ba: Imamul Bukharii ya ruwaito hadithi na 7,492 da Imamu Muslim hadithi na 1,151 daga Abu Hurairah cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce: ((Dukkan aikin dan adam ana ribanya kyakkyawansa har sau goma, har zuwa sau dari bakwai, amma Allah Mai buwaya da girma Ya ce: banda Azumi lalle shi nawa ne, kuma Ni zan yi sakayya a kansa, yana barin sha'awarsa, da abincinsa, saboda Ni, mai azumi yana da farin ciki biyu: farin ciki lokacin buda-baki, da farin ciki lokacin gamuwa da Ubangijinsa, wallahi! Warin baki a cikinsa (azumi) ya fi almiski kamshi a wurin Allah)). Yana daga cikin falalar azumi ganin yadda Allah Madaukakin Sarki Ya kebe wata kofa ta musamman cikin Aljanna saboda shigar masu azumi ta cikinta: Imamul Bukharii ya ruwaito hadithi na 1,896 da Imamu Muslim hadithi na 1,152 daga Sahal cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce: ((Lalle, a cikin Aljanna akwai wata kofa da ake kira "Ar-rayyan" a ta cikinta ne masu azumi ke shiga ranar Kiyama, babu mai shiga ta cikinta sai su, ana cewa: ina masu azumi? Sai su tashi, babu wani mai shiga ta cikinta in ba su ba, idan suka shiga sai a kulle, babu wani mai shiga ta cikinta)). SHARADIN WAJIBCIN AZUMI: Dukkan maluman Musulunci sun yi ijma'I a kan cewa azumi yana wajaba ne kawai a kan Musulmi, baligi, mai cikakken hankali, mai lafiya, wanda yake ba matafiyi ba, haka nan yana zama wajibi a kan mace wacce ba ta cikin jinin haila ko jinin biki. LADUBBAN AZUMI: Yana daga cikin ladubban azumi, nisantar rada da annamimanci da makamantansu: Imamul Bukharii ya ruwaito hadithi na 1,903 daga Abu Hurairah cewa Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce: ((Wanda duk bai bar maganar karya ba, da kuma aiki da ita, to, Allah ba ya bukatar ya bar abincinsa da abinshansa)). Yana daga cikin ladubban azumi, cin abincin sahur, saboda shi sahur ya kan taimaki mai yin azumi a kan tafiyar da azuminsa ba tare da tagayyara ba, wannan shi ya sa ma Annabi mai tsira da amincin Allah ya ja hankulan Musulmi da suka rika yin sahur, Imam Ahmad ya ruwaito hadithi na 11,414 daga Abu Sa'id Al-khudrii cewa Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce: ((Sahur abincin albarka ne, kada ku bar yin shi, koda kuwa dayanku kwankwada daya ne na ruwa zai yi, lalle, Allah Mai buwaya da girma da mala'ikunSa suna yin salati ga masu yin sahur)). Albanii ya hassana shi cikin Sahihul Jami'is Sagiir lamba na 1,844. Yana daga cikin ladubban azumi, mai yin azumi ya yi buda baki da danyen dabino ko kuma busashshensa, Imam Abu Dawud ya ruwaito hadithi na 2,358, da Imamut Tirmithi a hadithi na 696, da Imam Ahmad a hadithi na 12,676 daga Anas Dan Malik ya ce ((Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya kasance yana yin buda baki da wasu danyen dabino kafin ya yi salla, in kuma babu danyen dabino, to, sai ya yi buda baki da busashshen dabino, in kuma hakan bai samu ba, to sai ya kamfaci wasu kamfata na ruwa)). Albanii ya inganta wannan hadithin. Yana daga cikin ladubban azumi, mai yin azumi ya rika yawaita karatun Qur'ani, da sadaka, da kyauta, da sallar nafila, da kuma ambaton Allah Madaukakin Sarki a bisa hanyar Sunna, saboda hadithi na 6 da Imamul Bukharii ya ruwaito, da hadithi na 2,308 da Imam Muslim ya ruwaito daga Abdullahi Dan Abbas cewa: ((Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya kasance wanda ya fi kowa kyautar alheri, kuma ya fi yawan kyautan ne a cikin Ramadan a lokacin da Jibirilu yake zuwa masa, Jibirilu ya kasance yana zuwa masa ne a ko wane dare na Ramadan yana masa bitar Qur'ani, wallahi lokacin da Jibirilu yake zuwa masa ya fi iskar da take kadawa kyautar alheri)). ABUBUWAN DA SUKE BATA AZUMI: Abubuwan da suke bata azumi su ne: yin jima'I, ko cin abinci, ko shan ruwa, ko hadiye magani ta baki, ko dura wa mutum abinci ta hanyar allura da makamcin haka, ko fidda maniyyi ta hanyar sumbantar mace, ko rungumarta, ko fidda maniyyi da hannu, ko jawo amai da gangan. Dukkan wadanan in aka yi dayansu cikin yinin azumi to azumi ya baci, in kuma cikin dare aka yi, to, wannan babu kome. Amma fitan jinin haila ko jinin biki daga mace, shi wannan zai karya mata azuminta, koda kuwa cikin dare ne ya fito. HUKUNCE-HUKUNCEN ZAKKAR FIDDA-KAI: Imamul Bukhari ya ruwaito hadithi na 1503 da Imamu Muslim a hadithi na 984 daga Abdullahi Dan Umar cewa: ((Manzon Allah Mai tsira da amincin Allah ya farlanta zakkar fidda-kai sa'I daya na dabino, ko sa'I daya na sha'ir, a kan bawa, da da, da namiji, da ta-mace, da karami, da babba, daga cikin Musulmi, ya yi umurni a fidda zakkar kafin fitar mutane zuwa sallar idi)). Sannan ita Zakkar fidda-kai tana zama wajibi ne a kan Musulmi a lokacin faduwar rana a yinin karshe na watan Ramadhan, saboda haka dukkan wanda ya musulunta ko aka yi masa haifuwa kafin faduwar ranar wannan yini, to, zakkar fidda-kai ta zama wajibi a kansa, wanda kuma ya musulunta ko aka yi masa haifuwa bayan faduwar ranar wannan yini, to, zakkar fidda-kai ba ta zama wajibi ba a kansa. Mutumin da ya zamanto bai mallaki abin da zai bayar na zakka ba a lokacin da zakkar ta zama wajibi, to, zakkar ta fadi a kan sa ke nan har abada. Wannan shi ne mazhabar Shafi'iyya, da Hambaliyya, da Malikiyya cikin wata riwaya. Amma a wurin Hanafiyya, da kuma Malikiyya cikin wata riwayar, Zakkar tana zama wajibi ne a lokacin hudowar alfijir na yinin Idi. HUKUNCE-HUKUNCEN RANAR IDI: Abu ne da yake mustahabbi; al'ummar Musulmi su rika yin kabbarori a bayyane a daren Idin karamar salla da Idin babbar salla, su yi kabbarorin a kan hanyoyinsu, da cikin masallatansu, da gidajensu, haka nan za su ci-gaba da yin su a safiyar Idi har zuwa masallaci, har zuwa lokacin da liman zai fara yin huduba. Sannan in gari ya waye sai su yi wanka, su sanya tufafi masu kyau, su sanya turare, su tafi masallacin idi suna kabbara kamar yadda muka fada, idan Idin karamar salla ne, to, mustahabbi ne su karya da dabino daya, ko uku, ko fiye da haka a bisa adadi mara, kafin su tafi Idi, in kuma idin Layya ne to, kada su karya sai bayan Sallar Idi. Kuma Sunna ce mai karfi; dukkan mata su fita zuwa masallacin Idi, Imamul Bukhari ya ruwaito hadithi na 351 da Imamu Muslim hadithi na 890 daga Ummu Atiyya ta ce: ((Manzon Allah Mai tsira da amincin Allah ya umurce mu da mu fidda mata zuwa Idin karamar salla, da Idin babbar salla; 'yan mata, da masu haila, da ma'abuta khuduri (matan aure), to, amma su masu haila sai su nisanci salla, su halarci alkhairi da addu'ar musulmi. (ta ce: Sai) na ce: Ya Manzon Allah! Daya daga cikimmu ta yiwu ba ta mallaki mayafi ba. Sai ya ce: Sai 'yar uwarta ta ba ta aron mayafi)). Kuma yana da kyau idan aka gama sauraron huduba za a koma gida a sake hanya, Imamut Tirmithi ya ruwaito hadithi na 542 da Imam Ibnu Maja hadithi na 1317, kuma Albani ya inganta shi cikin Sahihu Sunani Ibnu Majah 1/390 daga Abu Huraira cewa ((Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya kasance idan ya tafi idi ta wata hanya, to, ya kan dawo ta wata hanya daban)). هذا، وصلى الله وسلم على نبينا محمد وعلى آله واصحابه ومن تبعهم بإحسان إلى يوم الدين.

definition of righteousness

It is not righteousness that ye turn your faces Towards east or West; but it is righteousness- to believe in Allah and the Last Day, and the Angels, and the Book, and the Messengers; to spend of your substance, out of love for Him, for your kin, for orphans, for the needy, for the wayfarer, for those who ask, and for the ransom of slaves; to be steadfast in prayer, and practice regular charity; to fulfil the contracts which ye have made; and to be firm and patient, in pain (or suffering) and adversity, and throughout all periods of panic. Such are the people of truth, the Allah-fearing. — AL QUR'AN 2:117

Friday, 7 September 2012