Saturday, 22 December 2012
Thursday, 20 December 2012
♥♥♥أَسْتَغْفِرُ اللَّهَ الَّذِي لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ الْحَيَّ الْقَيُّومَ وَأَتُوبِ إِلَيْهِ♥ ♥♥

And all of you beg Allah to forgive you all, O believers, that you may be successful
24:31
ا
Tuesday, 18 December 2012
It has been confirmed in Sahih Muslim from Jabir that the Messenger of Allah recited this Surah (Al-Kafirun) and
﴿قُلْ هُوَ اللَّهُ
أَحَدٌ ﴾
(Say: "He is Allah One.'') (112:1) in the two Rak`ahs of Tawaf. It is also
recorded in Sahih Muslim in a Hadith of Abu Hurayrah that the Messenger of Allah
recited these two Surahs in the two Rak`ahs (optional prayer) of the Morning
prayer. Imam Ahmad recorded from Ibn `Umar that the Messenger of Allah recited
in the two Rak`ahs before the Morning prayer and the two Rak`ahs after the
Sunset prayer on approximately ten or twenty different occasions,
﴿قُلْ يأَيُّهَا
الْكَـفِرُونَ ﴾
(Say: "O Al-Kafirun!'') and
﴿قُلْ هُوَ اللَّهُ
أَحَدٌ ﴾
(Say: " He is Allah One.'') (112:1) Ahmad also recorded that Ibn `Umar said,
"I watched the Prophet twenty-four or twenty-five times reciting in the two
Rak`ahs before the Morning prayer and the two Rak`ahs after the Sunset prayer,
﴿قُلْ يأَيُّهَا
الْكَـفِرُونَ ﴾
(Say: "O Al-Kafirun!'') and
﴿قُلْ هُوَ اللَّهُ
أَحَدٌ ﴾
(Say: "He is Allah One.'') (112:1)'' Ahmad recorded that Ibn `Umar said, "I
watched the Prophet for a month and he would recite in the two Rak`ahs before
the Morning prayer,
﴿قُلْ يأَيُّهَا
الْكَـفِرُونَ ﴾
(Say: "O Al-Kafirun.'') and
﴿قُلْ هُوَ اللَّهُ
أَحَدٌ ﴾
(Say: "He is Allah One.'') (112:1)'' This was also recor- ded by At-Tirmidhi,
Ibn Majah and An-Nasa'i. At-Tirmidhi said, "Hasan.'' It has already been
mentioned previously in a Hadith that it (Surat Al-Kafirun) is equivalent to a
fourth of the Qur'an and Az-Zalzalah is equivalent to a fourth of the Qur'an.
﴿بِسْمِ اللَّهِ
الرَّحْمَـنِ الرَّحِيمِ﴾
In the Name of Allah, the Most Gracious, the Most Merciful.
﴿قُلْ يأَيُّهَا
الْكَـفِرُونَ- لاَ أَعْبُدُ مَا تَعْبُدُونَ- وَلاَ أَنتُمْ عَـبِدُونَ مَآ
أَعْبُدُ- وَلا أَنَآ عَابِدٌ مَّا عَبَدتُّمْ- وَلاَ أَنتُمْ عَـبِدُونَ مَآ
أَعْبُدُ- لَكُمْ دِينُكُمْ وَلِىَ دِينِ-﴾
(1. Say: "O disbelievers!'') (2. "I worship not that which you worship.'')
(3. "Nor will you worship whom I worship.'') (4. "And I shall not worship that
which you are worshipping.'') (5. "Nor will you worship that which I worship.'')
(6. "To you be your religion, and to me my religion.'')
Sunday, 16 December 2012
Sunday, 9 December 2012
INCIN WANNAN RANA KAMAR
YADDA SALAFUS SAA'LIH SUKA YI BAYANI:
Kafin mu shiga bayanin wannan mas'alah ya kamata 'yan'uwa su san abubuwa kamar haka:-
Na farko: Shi dai bukin kirsimeti wata bidi'ah ce da kiristoci suka kirkira sannan suka maida ita wata ibada da ake samun lada ta hanyar yin ta -kamar dai yadda wasu karkatattu cikin Musulmi suka kirkiri bidi'ar idin mauludi- Kiristoci sun kirkiri wannan bidi'ar ne kuwa a shekarar miladiyyah ta 360, watau a cikin karni na hudu bayan haifuwar Annabi Isa alaihis salam.
Na biyu: babu wanda ya isa ya bugi kirji a duniyan nan ya ce: ga tabbatacciyar wata da rana da aka haifi Annabi Isa alaihis salam a cikin su, sai dai kowa ya fadi abin da yake zato kawai, wannan shi ya sa ma Kiristoci masu yin bukin ranar Kirsimeti watau ranar haifuwar Annabi Isa suka yi sabani game da ranar da za a yi wannan bukin, har mazhabobi biyu:-
Mazhabar farko: Za a yi bukin Kirsimeti ne a ran 25 ga watan December, wannan ita ce mazhabar da Catholic, da Protestant, da kuma mafi yawan darikokin Kiristoci suke bi.
Mazhaba ta biyu: Za a yi bukin Kirsimeti ne a ran 7 ga watan January, wannan ita ce mazhabar da darikokin Orthodox suke bi.
Na uku: Kiristoci kafurai ne kamar yadda Yahudawa, da Majusawa, da kuma sauran masu bautar gumaka suke kafurai.
Na hudu: Ya kamata a san cewa akwai wasu kafurai da Musulunci ya kebanta su da wani hukunci saboda tabbatar wa Musulmi wata maslaha, wadannan kuwa su ne: Yahudawa, da Kiristoci, su wannan nau'i na kafurai Musulunci ya halatta wa Musulmi cin yankansu, da kuma auren matansu, sabanin mabiya addinin majusu, ko mabiya addinin indiyawa, ko mabiya addinin Budha, ko mabiya sauran addinai na bautan gumaka. Idan an fahimci wannan sai mu shiga bayanin mas'alarmu da muke son yi wa jama'a bayaninta. Allah Madaukakin Sarki Ya taimake mu.
HUKUNCIN KARBAN KYAUTUTTUKAN KAFURAI A RANAR IDINSU:
Su kyaututtukan da kafurai -Ahlul kitabi ko wasun Ahlul kitabi- ke ba wa Musulmi a ranakun idinsu na kafurci da bidi'ah sun kasu kashi biyu ne:-
Na farko: Kyaututtukan da suke ba nama ba ne da ake bukatar yankawa, watau kamar irinsu: halawa, da tufafi, da kayan marmari, sa sauransu.
Na biyu: Kyaututtukan da suke nama ne da ke bukatar a yi masa yanka irin ta Shari'ah.
To shi na farkon, watau kyaututtukan da suke ba nama ba ne da ke bukatar yanka irin ta Shari'ah, babu sabani tsakanin Salafus Salih a iya saninmu cikin halaccin karbarsu, saboda dalilai kamar haka:-
1- Imamul Baihaqii ya ruwaito athari na 18,644 daga Muhammad Dan Siiriin cewa:-
((أتي علي رضي الله بهدية النيروز، فقال: ما هذه؟ قالوا: يا امير المؤمنين هذا يوم النيروز. قال: فاصنعوا كل يوم فيروز)). انتهى.
Ma'ana: ((An zo wa Sayyidina Aliyyu Dan Abii Taa'lib Allah Ya kara masa yarda da kyautar (idin) Nairuuz, sai ya ce: mene ne wannan? Sai suka ce: Ya Amirar Muu'miniin! Wannan ranar Nairuuz ce. Sai ya ce: (in haka abin yake) ku rika yin Fairuuz a ko wace rana)). Intaha.
2- Imam Ibnu Abii Shaibah ya ruwaito cikin Musannaf athari na 24,371, da Imam Ishaq Ibnu Raa'huyyah cikin Musnad athari na 1,606 daga Qaa'bus Dan Zibyaan daga shi mahaifin nasa cewa wata mace ta tambayi Nana A'isha Allah Ya kara mata yarda ta ce:-
((ان لنا اكارا من المجوس وانه يكون لهم العيد فيهدون لنا، فقالت: اما ما ذبح لذلك اليوم فلا تأكلوا ولكن كلوا من أشجارهم)). انتهى
Ma'ana: ((Muna da 'yan kodago daga cikin Majusawa, sannan kuma suna da ranar idin da suke aika mana da kyaututtuka. Sai ta ce: Amma abin da aka yanka saboda wannan ranar to kada ku ci, to amma ku ci daga 'ya'yan itatuwansu)). Intaha.
3- Imam Ibnu Abii Shaibah ya ruwaito a cikin Musannaf athari na 24,372 daga Abuu Barzah cewa:-
((كان له سكان مجوس فكانوا يهدون له في النيروز والمهرجان فكان يقول لأهله: ما كان من فاكهة فكلوا وما كان من غير ذلك فردوه)). انتهى.
Ma'ana: ((Yana da wasu mazauna Majusawa, kuma sun kasance suna aika masa da kyautuka a lokacin Nairuuz da Mihrajan, sannan ya kasance yana gaya wa iyalansa cewa: Kyautar da ta kasance ta kayan marmari ne to ku ci, wacce kuma ta kasance ba hakan ba, to ku mayar da ita)). Intaha.
Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya yi taliki a kan wadannan hujjojin a cikin littafinsa mai suna Iqtidhaa'us Siraa'til Mustaqiim 2/554-555 ya ce:-
((فهذا يدل على انه لا تأثير للعيد في المنع من قبول هديتهم، بل حكمها في العيد وغيره سواء؛ لانه ليس في ذلك إعانة لهم على شعائر كفرهم)). انتهى.
Ma'ana: ((Wannan duka yana nuni ne a kan cewa: Idi ba yi da wani tasiri a kan hana karban kyautarsu, a'a hukuncin karban kyautarsu ba yi da wani bambanci tsakanin lokacin Idi da kuma lokacin da ba na Idi ba, saboda babu wani abu na taimakon addininsu a cikin karban kyautarsu)). Intaha.
TALIKI:
Da wannan ne za mu fahimci cewa: Maluman Musulunci sun hana cin yankan da Majusawa suka yi domin bukukuwan idinsu, to amma fa ba wai sun hana cin yankan ba ne saboda kasancewarsa yankan da aka yi domin bukin idin kafurai ba, a'a an hana cin yankan ne saboda kasancewarsa yankan Majusawan da ba sa cikin mutanen nan ne da ake kira Yahudawa ko ake kira Kiristoci, dukkan kuma kafurin da ba ya cikin abin da ake kira Yahudawa ko ake kira Kiristoci to ba cin yankansa.
HUKUNCIN CIN NAMAN DABBAR DA YAHUDAWA KO KIRISTOCI SUKA YANKA DA HANNAYENSU SABODA YIN BUKUKUWAN IDINSU:
Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya yi bayani game da cin abin da Yahudawa ko Kiristoci suka yanka saboda bukukuwan idinsu, a cikin littafinsa mai suna Iqtidhaa'us Siraa'til Mustaqim 2/555,558 ya ce:-
((وانما يجوز ان يؤكل من طعام اهل الكتاب في عيدهم بابتياع او هدية او غير ذلك مما لم يذبحوه للعيد. فأما ذبح المجوس فالحكم فيها معلوم فإنها حرام عند العامة. وأما ما ذبحه اهل الكتاب لاعيادهم وما يتقربون بذبحه الى غير الله نظير ما يذبح المسلمون من هداياهم وضحاياهم متقربين بها الى الله تعالى، وذلك مثل ما يذبحون للمسيح والزهرة، فعن احمد روايتان: اشهرهما في نصوصه: انه لا يباح اكله وان لم يسم غير الله تعالى. ونقل النهي عن ذلك عن عائشة وعبد الله بن عمر)). انتهى.
Ma'ana: (Cin abincin Ahlul Kitabi a lokacin idinsu ga abin da dama ba su yanka shi saboda Idi ba, yana halatta ne ta hanyar saye da kudi, ko kuwa kyauta, ko wanin haka. Amma abin da Majusawa suka yanka hukuncinsa sananne ne, watau haramun ne a wurin dukkan malamai, to amma abin da Ahlul Kitabi suka yanka saboda idinsu, da kuma abin da suke yin ibada ta hanyar yanka shi ga wanin Allah' kamar abin da suke yankawa saboda Almasihu, da Zahrah, irin dai abin da Musulmi suke yankawa na Hadaya, da Layya, domin neman kusantar Allah da shi, to, Imam Ahmad yana da fatawowi biyu game da hakan, fatawar farko wacce ita ce ta fi shahara: Wannan ba ya halatta a ci shi koda kuwa ba a ambaci sunan wanin Allah a kansa ba. An nakalto hana cin wannan yankan ma daga Nana A'isha, da Abdullahi Dan Umar.. Fatawa ta biyu ita ce: Cin wannan yankan makruuhi ne ba haramun ba. Wannan ita ce mazhabar Malikiyyah, Imam Malik ya kyamaci cin abin da Ahlul Kitabi suka yanka saboda Coci-Cocinsu, ko saboda idinsu amma ba tare da ya haramta hakan ba)). Intaha.
Sannan har yanzu Sahikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya ce a cikin Iqtidhaa'us Siraa'til Mustaqim 2/559 :-
((ونقلت الرخصة في ذبائح الأعياد ونحوها عن طائفة من الصحابة رضي الله عنهم، وهذا فيما اذا لم يسموا غير الله، فان سموا غير الله في عيدهم او غير عيدهم حرم في اشهر الروايتين، وهو مذهب الجمهور، وهو مذهب الفقهاء الثلاثة فيما نقله غير واحد، وهو قول علي بن ابي طالب وغيره من الصحابة، وهو قول اكثر فقهاء الشام وغيرهم. والثانية: لا يحرم وان سموا غير الله، وهذا قول عطاء ومجاهد ومكحول والاوزاعي والليث)). انتهى.
Ma'ana: ((An ciro yin sauki a kan cin yanke-yanken idodin (Yahudawa da Kiristoci) da makamantansu (su yanke-yanken) daga wani sashi na Sahabbai Allah Ya kara musu yarda amma fa wannan sai idan ba su ambaci wanin Allah a lokacin yankan ba, in kuma har sun ambaci wanin Allah a lokacin yankan to cin sa ya haramta a cikin fatawa mafi shahara daga cikin fatawowi biyu da Imam Ahmada yake da su a cikin mas'alar, wannan kuwa shi ne mazhabar jumhur, kuma shi ne mazhabar Fuqaha'un nan guda uku, kamar yadda mutane da yawa suka ruwaito, kuma shi ne maganar Aliyyu Dan zabii Taa'lib da waninsa a cikin Sahabbai, daga cikinsu ma akwai Abud Dardaa, da Abu Umamah, da Irbadh Dan Saa'riyah, da Ubaa'dah Dan Saa'mit, kuma shi ne maganar maluman Sham da wasunsu. Fatawar Imam Ahmad ta biyu ita ce: Cin wannan yankan ba haramun ba ne koda kuwa sun ambaci sunan wanin Allah a lokacin yankan, wannan kuwa shi ne maganar Ataa'u, da Mujaa'hid, da Makhuul, da Auzaa'ii, da kuma Laith)). Intaha.
TALIKI NA FARKO:-
Za mu fahimta daga maganganun malaman da suka gabata cewa: Abin da Yahudawa da Kiristoci suke yankawa saboda bukukuwan idinsu yana kasuwa ne zuwa kashi biyu:-
Na farko: Abin da suka ambaci sunan Allah yayin yanka shi.
Na biyu: Abin da suka ambaci sunan wanin Allah yayin yanka shi.
To ita tabbar da aka ambaci sunan Allah lokacin yanka ta, Malamai sun kasu kashi biyu game da hukuncin cinta.
Mazhabar farko: Sahabbai da yawa sun ba da damar cin wannan nama. Maluman Malikiyyah, da Imam Ahmad cikin ruwayah sun halattar da cinsa amma tare da nuna kyama.
Mazhaba ta biyu: Nana A'isha, da Abdullahi Dan Umar, da kuma Maluman Hanaa'bilah sun ce cin wannan nama haramun ne.
Sannan ita kuma dabbar da aka ambaci sunan wanin Allah lokacin yanka ta, watau kamar wacce aka ambaci sunan Yesu Almasihu lokacin yanka ta, wannan ma Malamai sun kasu kashi biyu game da hukuncin cin wannan dabbar:-
Mazhabar farko: Cin wannan dabba bai halatta ba, wannan shi ne abin da Aliyyu Dan Abii Taa'lib, da Abud Dardaa'u, da Abuu Umamah, da Irbadh Da Saa'riyah, da Ubaa'dah Dan Saa'mit, da Hanafiyyah, da Malikiyyah, da Shafi'iyyah, da Hanaa'bilah, da mafi yawan maluman kasar Sham, suk fada.
mazhaba ta biyu: Cin wannan dabba halal ne, wannan shi ne abin da Ataa'u, da Mhjaa'hid, da Makhul, da Auzaa'ii, da Laithu Dan Sa'ad, da kuma Imam Ahmad cikin ruwaya suka fada.
TALIKI NA BIYU:-
Za mu iya fahimta daga maganganun da suka gabata cewa: Naman kasuwa da Musulmi ke yankawa da hannayensu idan Kiristoci suka saya suka dafa a matsayin abincin Kirsimeti, to wannan abincin halal yake ga dukkan wanda suka ba da shi gare shi. Wallahu A'alam.
Mun kawo maganganun Salafus Saa'lih ne cikin wannan mas'alah, saboda kwaranye wa 'Yan'uwa Musulmi mushikilar da ke cikinta. Muna rokon Allah Madaukakin Sarki ya nuna mana gaskiya gaskiya ce ya ba mu ikon bin ta, ya nuna mana karya karya ce ya ba mu ikon guje mata.

Monday, 3 December 2012
Subscribe to:
Posts (Atom)