Ya ku Al‘ummar musulmai! Lalle ne ku san cewa: musulunci ya haramta dukkan wani zalunci, Allah madaukakin sarki yace, cikin suratul baqarah aya ta 231(idan ku sake mata sanna sukayi kusan gama iddarsu sai ku rikesu da alheri, ko kuma ku sallamesu da alheri kada ku rikesu akan cutarwa domin zalunci wanda duk yayi haka hakika ya zalunci kansa) kuma annabi mai rahma yace babu cuta babu cutarwa. Sanna Allah yace cikin hadisi qudusi (yaku bayina lallene na haramata wa kaina yin zalunci, kuma na haramta muku yin zalunci a tsakaninku saboda haka kadaku zalunci juna) sannan annabi mai rahma yace (yace musulmi dan uwan musulmine,bazai zalunceshiba bazai mikashi ga zalunci ba) ya ku al‘uman musulmai zalunci a idanun shari‘a ya kasu kashi uku (3) KASHI NA FARKO(1) zalunci da bawa zaiyi wa ubangijinsa, ta hanyar yi masa tarayya cikin ibaba ko shakka babu zalunci mafi girma shine mutun ya sanya wa Allah kiciya cikin ibadarsa alhali shine wanda ya halliceshi kamar yanda Allah madaukakin sarki yace ciki suratul luqman aya ta sha uku(13) (lalle shirka zaluncine babba) wanna shi yasa ma yace cikin suratul an‘am aya ta (82) (wadanna da suka yi imani sannan basu chakuda imaninsu da zalunciba wadanna su ke da amintuwa kuma sune shiryayyu). Abisa wanna ma‘ana kenwn duk kafiri da kuma dukkan mushiriki da kuma dukkan munafiki, azzalumine a musulunci. KASHI NA BIYU(2) zalunci da bawa zaiyi wa dan uwansa bawa, da wannan kashi ne Allah ke nufin cikin suratul SHURA aya ta (40) inda yace (sakamakon cuta shine wata cuta kamarta, sai dai wanda yafi kuma ya kyautata, to, ladarsa na ga Alla. Lallene shi Allah bayason azzalumai.). Abisa wannar ma‘ana kenan dukkan wani mutun mai zaluntar wani mutun cikin dukiyarsa ko cikin mutuncinsa, ko cikin lafiyar jikinsa sannan shi a shari‘ar musulunci shi azzalumine. KASHI NA UKU (3) zalunci da mutun zaiyi wa kansa da kansa wato dukkan wani irin sabo da zaiyi fito daga gareishi, to irin wanna nau‘in na zaluncine Allah madaukakin sarki yake nufi cikin suratul FADIR aya ta (32).
No comments:
Post a Comment