Monday, 26 November 2012

BANDA BIDI'AR 'YAN SHI'AH, BANDA KUMA BIDI'AR NAWAASIB A RANAR AA'SHUU'RAA, ABIN DA KE WAJIBI SHI NE LAZIMTAR SUNNAH WATAU AZUMCE WANNAN RANA TA GOMA GA WATAN MUHARRAM:

Yau muna litinin 5/1/1434 H 19/11/2012 M ke nan ranar juma'a Mai zuwa ita ce ranar Aa'shuu'raa Ranar da yin azumi cikinta Sunnah ce ta Annabi mai tsira da amincin Allah.

Sannan wannan rana ta Aa'shuu'raa ranar goma ga watan Muharram ita ce ranar da Allah Madukakin Sarki ya girmama Sayyidina Husain Dan Sayyidina Aliyyu Bin Abi Talib Allah Ya kara musu yarda da yin shahada a cikinta, a shekarar hijira ta settin, saboda shahadarsa ta kasance wani abu da Allah Ya kara daukaka darajarsa da ita.

IYA YAWAN DARAJARKA IYA GIRMAN MUSIBAR DA ZA TA SAME KA

Imamut Tirmizii ya ruwaito hadithi na 2,398 da isnadi sahihi daga Sa'ad Dan Abi Waqqas cewa ya ce: Ya Manzon Allah! Wane ne daga cikin mutane masifa ta fi auka masa? Sai ya ce: ((Annabawa ne, sai kuma wanda ya fi daraja, sai kuma wanda yake biye a daraja, a kan jarrabi mutum ne a bisa gwargwadon addininsa, idan addininsa mai karfi ne sai Bala'insa ya zamanto mai karfi, idan addininsa laga-laga ne, sai a jarrabe shi gwargwadon addininsa, bala'i ba zai gushe ba yana ta samun bawa, har sai ya ga cewa yana tafiya bayan kasa ba tare da wani zunubi ba)). Intaha. 

TAKAITACCEN KISSAR KASHE HUSAIN ALLAH YA KARA MASA YARDA:

Shi dai Sayyidina Husain da yayansa Sayyidina Hasan Allah Ya ba su darajoji masu yawa, sai dai kuma bala'o'in da suka same su ba su kai bala'o'in da suka sami magabatansu ba, saboda kasancewarsu an haife su ne a lokacin da Musulunci yake cikin bunkasa, sun kuma tashi cikin izza da karama, Musulmi na girmama su, Annabi mai tsira da amincin Allah ya mutu ko shekarun rarrabewa ba su kai ba, saboda haka wata irin ni'ima ce a gare su da Allah Madaukakin Sarki ya jarrabe su da irin bala'in da ya jarrabe su da shi, kamar yadda ya jarrabi wadanda suka fi su daraja, kamar mahaifinsu Sayyidina Ali wanda yake ya fi su daraja nesa ba kusa ba, amma kuma shi ma an kashe shi a bisa zalunci yana matsayin shahidi.

Ko shakka babu kashe Sayyidina Husain ya tada fitina tsakanin mutane, kamar yadda kashe Sayyidina Uthman Dan Affan ya kawo fitinu masu yawa wadanda a dalilinsu ne ma aka samu rabuwar da har yanzun nan akwai tasirinta cikin Al'ummah.

Ya tabbata cikin tarihi cewa lokacin da Bin Muljam ya kashe Sayyidina Ali kuma Sahabbai suka yi mubaya'ah ga dan shi Sayyidina Hasan wanda Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce game da shi: ((lalle Dan nan nawa shugaba ne, Ina fata Allah zai yi sulhu tsakanin wasu manyan kungiyoyin Musulmi biyu ta hanyar shi)). Intaha. (Sahihul Bukharii hadithi na 2,704). Bayan wani dan lokaci kadan sai Sayyidina Hasan ya sauka daga kan mulki, aka kuma sami yin sulhu tsakanin manyan kungiyoyin musulmi biyun kamar yadda Annabi mai tsira da amincin Allah ya ba da labari, to bayan mutuwar shi Sayyidina Hasan sai aka sami wasu karkatattun mutane masu mugun aniya da suka rubuta wa Sayyidina Husain wasika -bayan -wasika suna masu neman shi da ya bar garin Madinah ya taho garin Kufah, suna masu masa alkawarin cewa za su taimake shi domin ya zama khalifa! Alhali su wadannan mutane ba su da damar nada wani ya zama khalifah ta hanyar mubaya'ah da za su yi masa.

Shi Sayyidina Husain ya yi tsammanin cewa abin da wadannan mutanen ke cewa abu ne da ya kai har zuciyarsu, alhali kuwa lamarin ba haka yake ba. Duk kuwa cewa manyan Sahabbai cikin masoyansa kamar su Abdullahi Dan Abbas, da Abdullahi Dan Umar, da wasunsu sun ba shi shawarar cewa kada ya karbi maganar wadancan mutanen, kada ya ce zai bar Madinah zuwa Kufah da zimmar wadancan za su yi masa mubaya'ah domin zama khalifah, suka nuna masa cewa babu maslahar Musulmi cikin wannan lamari, abin bakin cikin dukkan abin nan da suka ji tsoron faruwarsa shi ne dai a karshe ya faru.

To, lokacin da Sayyidina Husain ya fita daga Madina zuwa Kufah sannan ya fahimci cewa dukkan abin nan da karkatattun nan suka gaya masa babu gaskiya a cikinsa, sai ya nemi rundunar da ta tsare shi da ta bar shi ya komo Madinah, ko kuwa ya tafi can kasar Sham inda dan baffansa Yazidu Dan Mu'aawiyah yake, amma ba su ba shi damar yin hakan ba, suka ce sai dai ya yadda su kama shi a matsayin fursunan yaki shi kuwa ya ki ba su kai, saboda haka dai yaki ya kaure tsakaninsu abin da ya kai ga kashe shi a bisa zalunci, ya mutu yana shahidin da Allah Ya girmama shi da samun shahada, kuma Ya riskar da shi danginsa masu tsarki da daraja, sannan Ya wulakanta wadanda suka kashe shi.

Wannan ya sa Al'ummah suka fada cikin sharri, Shi'ah Rafidha wadanda suke son nuna wa duniya cewa su masu goyon bayansa ne da goyon bayan danginsa suka riki wannan rana ta goma ga watan Muharram watau ranar Aa'shuu'raa a matsayin ranar makoki da juyayi, da kururuwa irin ta mata da bayyanar da halayen jahiliyyah wadanda Musulunci ya hana, kamar marin kumatu da yayyaga tufafi saboda nuna bakin ciki.

BIDI'AR YAN SHI'AH A RANAR AA'SHUU'RAA 

Yan Shi'ah a wannan zamani namu su kan tarbi watan Muharram da nuna bakin ciki da alhini, da ayyukan shirme da yi wa wasu bayin Allah kage, su kan ware wasu mutane a kwanukan goman farko na wannan watan domin su rika karanta wa mutane kyawawan dabi'un Husain da kuma munanan dabi'un da suka kago suka jingina wa Mu'aawiyah da Dansa Yazid tare zaginsu, sannan idan ranar Aa'shuu'raa ta shigo sai su shirya wani kabari na Katako suna kiran shi kabarin Husain ko kuma Karbalaa su yi ta dawagi gefen shi suna kada ganguna, idan rana ta fadi sai su binne wannan kabarin ko kuwa su jefa shi cikin ruwa, sannan kowa ya koma gidan shi.
Kuma a ranar farko ga Muharram su kan share gidajensu su shirya abinci su karanta Fatiha da surar Kulya da Kulhuwa, da Kula'uuzai, da kuma ayoyin farko a surar Bakarah, da kuma salatin Annabi sannan su ba da kyautar ladan abincin ga matattu!! 
Har yanzu suka hana yin ado cikin watan Muharram, su kan daina cin nama, su kan daina shirya dukkan wasu walimomi na farin ciki!!
Su kan kuma yawaita kururuwa da dukan kirji da fiska, da yayyaga tufa, da tsine wa Sayyidina Mu'awiyah da Dansa Yazid, da sauran Sahhabai.
Bayan kuma kwana arba'in daga ranar Aa'shuu'raa su kan shirya wani bukin kuma saboda tara kudi da kuma yin abubuwan wauta iri-iri!!

Abin bakin ciki da takaici suna yin dukkan abin nan da suke yi ne a matsayin ayyukan addini da ake neman lada da yin su tare kuwa da cewa babu hujjar yin haka daga Alkur'ani Mai girma ko sunnar Annabi Mai tsira da amincin Allah, ko aikin Sahabban Manzon Allah wadanda Allah Ya yarda da su!!! Allah Madaukakin Sarki Ya ce cikin Suratu Faatir aya ta 8: ((Yanzu Wanda aka kawata masa munanan aikinsa yana ta ganinsa abu mai kyau -yana daidai da waninsa-? Lalle Allah Yana batar da wanda yake so kuma Ya shiryar da wanda yake so, saboda haka kada ranka ya halaka a kansu saboda bakin ciki. Lalle Allah Masani ne ga abin da suke aikatawa)). Intaha. 
Sannan Ya ce cikin Suratul Khaf aya ta 103-104 ((Ka ce: ko mu ba ku labarin mafiya hasara ga ayyuka? Su ne wadanda aikinsu ya baci cikin rayuwar duniya alhalin suna zaton cewa suna kyautata aiki)). 

WAUTAR YAN SHI'AH CIKIN BIDI'O'I NASU:

Lalle yana daga cikin abin da yake nuna wautar Yan Shi'ah da kuma batar basirarsu: irin abin da suke cewa wai ya faru a lokacin da aka kashe Sayyidina Husain, suna cewa wai an yi ruwan sama na jini a wannan rana, kuma babu wani dutse da za a daga a wannan rana face sai an sami danyen jini a karkashinsa, da dai tatsuniyoyi mara iyaka masu kama da wadannan.

Ko shakka babu kisan Sayyidina Husain yana daga cikin manyan zunubbai kuma duk wanda ya yi wannan kisan ko ya taimaka aka yi shi to ya cancanci ukubar Ubangiji wacce irinsa yake cancanta, sai dai kuma abin da ya kamata masu hankali su fahimta shi ne: Kisan Sayyidina Husain bai kai girman kisan da aka yi wa wadanda suka fi shi daraja ba, kamar Annabawa, da Manyan Sahabban da suka riga shi shiga Musulunci, da kuma Sahabban da aka kashe a yakin da aka yi da Musailamatul Kazzab, da kisan da aka yi wa Sayyidina Hamza da sauran Shahidan Uhdu, da kisan da aka yi aw Shahidai talatin da tara (39) a yakin Bi'iru Ma'uuna, da kisan da aka yi Sayyidina Uthman, da kisan da aka yi wa Sayyidina Ali, musamman ma da yake mutanen da suka kashe Sayyidina Ali suna daukansa ne a matsayin kafiri murtaddi wanda ake samun lada ta hanyar kashe shi!! Sabanin wadanda suka kashe Sayyidina Husain su wadannan suna daukan sa a matsayin Musulmi ne kuma da yawa daga cikinsu ko ma mafi yawansu suna kyamar kashe shi, sai dai kuma sun kashe shi saboda kawai son zuciya, kamar yadda sashin mutane ke kashe sashi a kan neman mulki. 

Ke nan, da 'Yan Shi'ah na da hankali mai amfani da sai su san cewa: Abin nan da ya hana su yin bukukuwan nuna bakin cikin kashe manyan mutane da suka fi Sayyidina Husain daraja, kamar su Sayyidina Hamza da Sayyidina Aliyu Dan Abi Daalib, da sauransu shi ne kuma ya kamata ya hana su yin bukukuwan nuna bakin cikin kashe Sayyidina Husain!!

Idan kuma wani Dan Shi'ah ya ce: saboda kasancewar Sayyidina Husain jikan Annabi ne to fa lalle ne mutuwarsa ta sabbaba wani irin bakin cikin da tilas ne a shirya masa bukukuwa irin wannan!!

To sai a ba shi amsa a ce da shi: Kowa ya san cewa Annabi Mai tsira da amincin Allah shi ne ya fi dukkan halitta daraja, kuma shi ne ya fi dukkan Annbawa falala, kuma shi ne shugaban dukkan 'yan Adam, Domin haka lalle bakin cikin da zai sami Musulmi saboda mutuwarsa shi ne bakin cikin da ya zarce dukkan wani bakin cikin da zai samu Musulmi a wannan duniya tamu. Wannan magana kuwa ingantaccen hadithi ya zo da ita, saboda Imamut Tabaraanii ya ruwaito hadithi na 6,579, da Imamud Darimii cikin sunan dinsa hadithi na 84, da Imamul Baihaqii cikin Shu'abul Iman hadithi na 10,153 daga Ibnu Saabid daga mahaifinsa ya ce Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce:-
((من أصيب بمصيبة فليذكر مصيبته بي فإنها اعظم المصائب)). انتهى.
Ma'ana: ((Wanda duk aka shafe shi da wata musiba to ya tuna da musibar ta same shi saboda (mutuwata) lalle ita ce mafi girman musibobi)). Intaha. Imam Albaanii ya inganta wannan hadithi cikin Silsilah Sahihah 3/97, da kuma Sahihu da Dha'ifu na Al-Jaaami'us Sagiir lamba na 348. 

Ke nan da masu addinin shi'anci suna da wani abu na hankali mai amfani to da bukukuwan nuna bakin cikin mutuwar Annabi mai tsira da amincin Allah ne ya kamata su rika shiryawa, ba wai bukukuwan nuna bakin cikin mutuwar Sayyidina Husain ba, kamar yadda suke yi. Allah Ya tsare mu halakarwar Shaidan.

ABUBUWAN DA 'YAN SHI'AH KE YI A RANAR AA'SHUU'RAA WADANDA SUKA SABA WA NASSOSHIN ANNABI MAI TSIRA DA AMINCI ALLAH A CIKIN LITTATTAFAN SUNNAH HAR MA DA LITTATTAFAN HADITHI NA SHI'AH MA:

A matsayinmu na Musulmi mun san cewa: Abin da Allah Madukakin Sarki Ya neme mu da yin shi a lokacin da wata musiba da samu shi ne yin Istirja'i kamar yadda Ya ce cikin Suratul Bakara aya ta 155-157 ((Ka yi bushara wa masu hakuri. Wadanda idan wata masifa ta same su sai su ce: lalle mu ga Allah muke, kuma lalle mu zuwa gare Shi masu komawa ne. Wadannan akwai albarka a kansu daga Ubangijinsu da wata rahama. Kuma wadannan su ne shiryayyu)). Intaha. Yana daga cikin siffar mumini ya yi istirja'i a duk lokacin da wata musiba ta fada masa, ba wai ya yi ta kururuwa yana jiwa kansa rauni ba.

Hana yin kururuwa da marin kumatu da yaga tufafi saboda nuna bakin ciki a kan wata musiba da ta faru a bu ne da Annabi mai tsira da amincin Allah ya hana cikin Sunnarsa. Imamul Bukharii ya ruwaito hadithi na 1,296, da Imamu Muslim hadithi na 104 daga Abu Musal Ash'arii cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce: ((Ni babu ruwana da wacce take kururuwa saboda wata masifa, da kuma wacce take aske kanta saboda wata masifa, da kuma wacce take kaykkyace tufarta saboda wata masifa)). Intaha. 
Har yanzu Imamul Bukharii ya ruwaito hadithi na 1,294 daga Abdullahi Dan Mas'ud cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce: ((Ba ya daga cikinmu mutumin nan da ya mari kumatu, sannan ya kaykkyace tufafi, kuma ya yi kira da irin kiran jahiliyyah)). Intaha.
Har yanzu Imamu Muslim ya ruwaito hadithi na 934 daga Abu Malik Al-Ash'arii cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce: ((Akwai abu hudu cikin al'ummata na lamarin jahiliyyah da za su bar yin su ba: Alfahari da asali, da sukar asalin wani, da ganin tasirin taurari cikin saukar ruwa sama, da kuma kururuwa a lokacin mutuwa)). Sannan ya ce: ((Mai kururuwa a lokacin mutuwa idan har bata tuba ba kafin mutuwarta, to za a tsaida ita a ranar Kiyamah tana sanye da tufar narkakken dalma ko man petur da kuma wata irin rigar annobar kazuwa)). Intaha.

Sannan wannan hani ya tabbata hatta cikin littattafan hadithi na Shi'ah misali:-
Saduuqii ya ruwaito cikin littafin Man La Yahdhuruhul Faqiih 4/271-272, haka nan Al- Hurrul Aa'milii cikin littafin Wasaa'ilush Shi'ah 2/915, da Yusuful Bahraanii cikin Hadaa'iqun Naadhirah 4/167, da Al- Hajj Husain cikin Jaami'u Ahaadithush Shi'ah 3/488 cewa Manzon Allah Mai tsira da amincin Allah ya ce:-
((النياحة من عمل الجاهلية)). انتهى.
Ma'ana: ((Kururuwa saboda mutuwa na daga cikin aikin Jahiliyyah)). Intaha.
Sannan ya zo cikin littafin Bihaarul Anwar 82/103 kamar haka:-
((النياحة من الجاهلية)). انتهى.
Ma'ana: ((Kururuwa saboda mutuwa na daga jahiliyyah)). Intaha.
Sannan ya zo cikin Bihaarul Anwar 82/101, da Mustadrakul Wasaa'il 1/143-144, da Jaami'u Ahaadithish Shi'ah 3/488 cewa Sayyidina Ali ya ce:-
((ثلاث من اعمال الجاهلية لا يزال فيها الناس حتى تقوم الساعة: الاستسقاء بالنجوم والطعن في الأنساب والنياحة على الموتى)). انتهى.
Ma'ana: ((Abubuwa uku na daga cikin ayyukan jahiliyyah mutane kuwa ba za su gushe suna cikinsu ba har Sa'ah ta tsaya: Neman ruwan sama ta hanyar taurari, da soke-soke game da dangantaka, da kuma yin kururuwar mutuwa a kan mamata)). Intaha.

Sai dai abin mamaki duk da wadannan hujjoji da ba sa daukan wani shakka sai ga shi yan Shi'ah sun taka su sun gina wannan bidi'ah tasu ta Aa'shuu'raa, Allah Ya sawwaka!!!

BIDI'AR DA NAWAASIB KE YI A RANAR AA'SHUU'RAA

Kamar yadda 'Yan Shi'ah ke yin bidi'o'in da kuka ji a baya, saboda ranar aa'shuu'raa, to haka nan kuma akwai wasu masu yi wata bidi'ar da ta yi hannun riga ta bidi'ar 'yan Shi'ah, wannan kuwa ita ce bidi'ar da Nawaasib suke yi, watau bidi'ar cika-ciki wacce ake yin ta a ranar Aa'shuu'raa ta hanyar caba ado da dafe-dafen abinci domin yalwata wa iyali da abokan arziki. 
Shaikhul Islam IbnunTaimiyya ya ce cikin littafinsa Mihaajus Sunnah 4/554: ((Shaidan ya kirkira wa mutane bidi'o'i biyu ta dalilin kashe Husain Allah Ya kara masa yarda: Bidi'ar nuna bakin ciki a ranar Aa'shuu'raa ta hanyar kuka da kururuwa, da marin kumatu, da hana sa kai ruwan sha, da rera wake-waken tunawa da mamaci, da abin da yake biyo bayan hakan na zagin Salaf da tsine musu, da sanya mara laifi a Shaun masu laifi, har ma a kai ga zagin manyan Sahabbai, sannan a yi ta karanta labarun mutuwarsa wanda da yawa daga cikin labarun karairayi ne kawai. Ko shakka babu manufar wanda ya kirkiro wannan bidi'ar shi ne bude kofar fitina, da raba kawunan Al'ummah, domin yin hakan ba wajiba ne, ba kuma mustahabbi ba ne a bisa ittifakin Musulmi, a gaskiya ma bidi'ar kururuwa, da rashin nuna wa Allah hakuri a kan tsofaffin musibu yana daga cikin abin da Allah da ManzonSa suka haramta. Haka nan kuma bidi'ar nuna farin ciki a ranar Aa'shuu'raa shi ma haramun ne)). Intaha.

ABIN DA YAKE YIN SA SHI NE SUNNAH A WANNAN RANA TA AA'SHUU'RAA 

Abin da Musulmi zai yi na Sunnah a wannan rana ta Aa'shuu'raa shi ne ya azumce shi. Imamut Tirmizii ya ruwaito hadithi na 755, da isnadi sahihi daga Abdullahi Dan Abbas ya ce: ((Nanzon Allah mai tsira da amincin Allah ya yi umurnin azumin Aa'shuu'raa, watau ranar goma)). Intaha. 
Sannan mustahabbi ne a yi azumin ranar tara ga watan ma, saboda hadithi na 1,134 da Imamu Muslim ya ruwaito daga Abdullahi Dan Abbas ya ce: ((Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce: Da zan rayu zuwa shekara mai zuwa to da zan yi azumin tara ga wata am)). Intaha. 

Ibnu Muflih ya ce cikin littafinsa mai suna Al-Furuu 3/111 ((Mafi falalarsa Aa'shuu'raa, shi ne kuma ranar goma bisa dacewa da abin da mafi yawan Malamai suka ce, sannan sai Taa,suu'aa shi ne kuma ranar tara)). Intaha.

Muna fata Allah Ya taimake mu Ya nuna mana gaskiya gaskiya ce Ya ba mu ikon bin ta Ya kuma nuna mana karya karya ce ya ba mu ikon guje mata. Ameen.

No comments: