Monday, 26 November 2012

FATAWOWIN MALUMANMU NA DA'AWAH DA AQIDAH NA DUNIYA A KAN MAS'ALAR MAIDA BUDE TARO KO RUFE SHI DA YIN ADDU'A CIKIN JAM'I WATA AL'ADA:


A
[Type the document title]



[Type the phone number]
[Type the fax number]
[Pick the date]
MUSA IBRAHEEM

 



FATAWOWIN MALUMANMU NA DA'AWAH DA AQIDAH NA DUNIYA
A KAN MAS'ALAR MAIDA BUDE TARO KO RUFE SHI DA YIN ADDU'A CIKIN JAM'I WATA AL'ADA:

'Yan'uwa Musulmi! Mun rubuta a cikin takardar seminarmu ta garin Abuju seminar da Kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunnah ta kasa ta yi a ranakun 26-28/7/1433. 15-17/6/2012 cewa: ((Dukkan wani aikin Annabi mai tsira da animcin Allah da ya zo bisa wata siffa, sannan malumanmu na Sunnah suka bayyana mana wannan siffar cikin littattafansu, to dukkan abin da zai canja wannan siffar, ko ya bata wannan siffar da sunan neman wata falalar Ubangiji Madaukakin Sarki, to lalle wannan ya zama bidi'ah cikin Addini)).

Mun bada misali da taron da Annabi mai tsira da aminci ya sa babban Sahabi Sa'ad Dan Ubadah ya kira, a inda shi Annabi ya halarci taron, kuma aka yi taron har aka gama kowa ya koma inda ya fito ba tare da yin addu'ar bude taro ko rufe shi ba cikin jam'i kamar yadda mu muke yi kullum a yanzu!! Mun kuma bada misalin irin yadda Umar Dan Khattab yake yin tarurruka da gwamnoninsa a lokacin aikin Hajji ba tare yin addu'ar bude taro, ko addu'ar rufe taro ba.

A cikin wannan rubutu namu na yau muna so ne mu kawo wa jama'ar musulmi masu kaunar Sunna daga baki har zuciya fatawowin da Malumanmu na da'awah da aqidah na duniya suka yi game da wannan mas'alar da kuma mas'aloli masu kama da ita. Amma kafin hakan ga shimfida:-

NA FARKO:
Lalle, a matsayinmu na Al'ummar musulmi, ba mu da wani abu na alheri da ya wuce yin koyi da Annabi mai tsira da mincin Allah cikin dukkan aqidarmu, da dukkan ibadarmu, da kuma dukkan mu'amalarmu. Allah Madaukakin Sarki Ya ce cikin Suratul Ahzaab Aya ta 21:-
((لقد كان لكم في رسول الله أسوة حسنة لمن كان يرجو الله واليوم الاخر)).
Ma'ana: ((Hakika' akwai koyi mai kyau gare ku game da Manzon Allah ga duk Wanda ke tsammanin Allah da kuma Ranar Lahira)). Intaha.

Sannan Annabi mai tsira da aminci ya ce cikin hadithin Irbadh Dan Sariyah wanda Abu Dawud ya ruwaito hadithi na 4609' da Tizrmizi hadthi na 2676' da Ibnu Majah hadithi na 42' da Ahmad hadithi na 26,182 sannan Sheik Albani ya inganta shi.
((فعليكم بسنتي وسنة الخلفاء الراشدين)).
Ma'ana: ((Ina horon ku da yin riko da sunnata da kuma sunnar Khalifofina shiryayyu..)). Intaha.

Sannan Imam Malik ya ruwaito cikin Muwattaa atharii na 783 cewa:-
((كان وهب بن كيسان يقعد الينا ثم لا يقول ابدا حتى يقول لنا لا يصلح اخر هذه الامة الا ما اصلح اوله)).
Ma'ana: ((Wahb Dan Kaisaan ya kasance yana zama gurinmu, sannan ba ya cewa komi har sai ya ce: Babu abin da zai gyara karshen wannan Al'umma sai abin nan da ya gyara farkonta)). Intaha.

NA BIYU:
Akwai wasu mutanen da saboda hamayyar da suke yi da wasu masu wa'azi sai ka rika ganin cewa idanunsu sun rufe ta yadda hakan zai hana su yin aiki da ka'idodin ilmi cikin bayanan da suke yi wa jama'a, sai ka rika ganin suna cewa: Annabi ya ce abu kaza! Amma kuma ba za su kawo muku nassin Annabin ba, saboda sun san cewa karya suke yi Annabin bai fadi abin da suke son su gaya wa mutane ya fadan ba!! Ko kuma ka rika ganin cewa sun kafa hujja da wani hadithi dha'ifi ba kuma tare da sun bayyana wa mutane raunin hadithin ba!!
Lalle irin wannan tasarrufi daga masu bijire wa gaskiya saboda kawai nuna ta'assubanci ga wani ra'ayi, ko ga wani malami, ko ga wani bangare, ko ga wata darika abin takaici ne matuka.

Saboda haka ina rokon Al'ummar musulmi musamman ma mu 'yan izala da su bude zukatansu ga maganganun maluman Sunnah da fatawowinsu, mun sani barin mutum ga abin da ya saba da shi abu ne mai wahalar gaske, musamman ma in da ya dauki abin a matsayin wata hanyar samun wata falalar Duniya ko Lahira ne, to amma duk da haka in har bawan Allah ya taro hankalinsa wuri guda sai ka ga karban gaskiya ya zo masa da sauki. Allah Ya taimake mu Ya yi mana jagora cikin dukkan lamuranmu. Ameen.

FATAWOWIN MALAMAN DA'AWAH DA AQIDAH

Ya zo cikin littafin Fataawal Lajnatid Daa'imah 24/189-190 lambar fatawa ta: 20,451 kamar haka:-
((س: شخص كانت عادته ان يطعم الطعام لطائفة من الناس في كل يوم جمعة، وبعد قضاء الطعام لا يتركون أماكنهم ومجالسهم، بل ينتظرون الدعاء لأحد منهم الذي عينه صاحب الطعام ان يدعو الله ان يصل ثواب ذلك الطعام الى أهاليهم الموتى وأقاربهم، وفي اثناء ذلك الدعاء يرفع السائل يده مع الحاضرين وهم يقولون: امين. فهل هذا الدعاء الذي ترفع فيه الأيدي جماعة بعد الطعام جائز ام لا؟
ج: الدعاء الجماعي بعد الطعام بالكيفية المذكورة لا اصل له في الشرع المطهر، فالواجب تركه؛ لانه بدعة والاكتفاء بما جاءت به السنة من الدعاء لصاحب الطعام بالبركة ونحو ذلك، كل شخص يقوله بمفرده، ومما جاء في السنة قول: "اللهم بارك لهم فيما رزقتهم واغفر لهم وارحمهم" وقول: "أفطر عندكم الصائمون وأكل طعامكم الأبرار وصلت عليكم الملائكة)).
Ma'ana: ((Tambaya: Mutum ne da al'adarsa ta kasance ya ciyar da wasu jama'a abinci a ko wace ranar juma'a, bayan an gama cin abincin ba sa barin guraren zamansu, a'a su kan jira addu'a ne daga wani cikinsu da mai abincin ya ayyana shi domin ya roki Allah ladan abincin ya kai ga 'yan'uwansu da iyalansu mamatan, kuma a lokacin wannan addu'ar shi mai addu'ar yana daga hannunsa tare da mahalarta suna cewa: amin. Ko wannan addu'ar da ake daga hannaye cikinta a cikin jam'i bayan cin abinci halal ce, ko kuwa a'a?
Jawabi: Aduu'ar jam'i bayan abinci a bisa yanayin da aka ambata ba yi da asali cikin Shari'ah Mai tsarki. Abin da ke wajibi shi ne barin shi, saboda shi bidi'ah ce, da kuma wadatuwa da abin da Sunnah ta zo da shi na yi wa mai abincin addu'ar karin albarka da makamcin haka. Ko wane mutum ya yi addu'ar shi kadan shi. Yana daga cikin abin da ya zo cikin Sunnah, fadar: "Ya Allah Ka yi musu albarka cikin abin da Ka azurta su, Ka gafarta musu, Ka yi musu rahama" da kuma fadar: "Masu azumi sun yi buda baki a gurinku, mutanen kirki sun ci abincinku, Mala'iku sun nema muku gafara)).

Sannan ya zo cikin littafin Mujallatul Buhuuthil Islamiyyah 21/52 -mujallar da babban majalisar malaman kasar Saudiyya take fitarwa- kamar haka:-
((ولم يثبت عن النبي صلى الله عليه وسلم قولا او فعلا او تقريرا الدعاء الجماعي عقب الصلوات او قراءة القران مباشرة او عقب كل درس، سواء كان ذلك بدعاء الامام وتامين المامومين على دعائه ام كان بدعائهم كلهم جماعة ولم يعرف ذلك أيضاً عن الخلفاء الراشدين وسائر الصحابة رضي الله عنهم، فمن التزم بالدعاء الجماعي عقب الصلوات او بعد كل قراءة للقران او بعد كل درس فقد ابتدع في الدين)).
Ma'ana: ((Bai tabbata ba daga Annabi mai tsira da mincin Allah ta hanyar magana, ko ta hanyar aiki, ko ta hanyar tabbatar da abin da wani Sahabi ya yi ko ya fada: yin addu'a cikin jam'i bayan salloli, ko bayan karatun Kur'ani kai tsaye, ko bayan dukkan darasi, babu wani bambanci hakan ya kasance ne ta hanyar addu'ar liman su kuwa mamu su rika yin amin a kan addu'arsa, ko kuwa addu'arsu gaba daya cikin jam'i. Haka nan ba a san hakan ba daga Khulafa'urrashiduun, da sauran Sahabbai, Allah Ya kara musu yarda. Saboda haka wanda ya lazimci addu'ar jam'i bayan salloli, ko bayan ko wane karatun Kur'ani, ko bayan ko wane darasi, to lalle wannan ya kirkiri bidi'ah cikin Addini)). Intaha.

Sannan ya sake zuwa cikin Fataawal Lajnatid Da'imah 28/242 lambar tambaya ta: 19,772 kamar haka:-
((س: نحن جماعة في السودان نجلس في حلقة في المسجد لتلاوة القران الكريم يوميا بعد صلاة الفجر، وفي نهاية التلاوة يدعو رجل مخصص ويرفع يديه، ونحن نرفع ايدينا معه ونؤمن على ذلك. هل يجوز هذا العمل ام لا يجوز؟
ج: هذا الدعاء الجماعي بعد انتهاء الحلقة المذكورة من قراءة القران بدعة يجب تركها، ولا مانع ان كل انسان يدعو لنفسه منفردا بعد فراغه من قراءة القران الكريم، او في غير ذلك من الأحوال؛ لان الدعاء عبادة، وهو مطلوب كل وقت لا سيما بعد الفراغ من العبادة)).
Ma'ana: ((Tambaya: Mu wasu jama'a ne a Sudan, muna zama cikin halaka a cikin masallaci saboda karatun Kur'ani ko wace rana bayan sallar Asuba, sannan a karshen tilawar wani mutum na musamman zai yi addu'a ya daga hannayensa mu ma mu daga hannayenmu tare da shi muna yin amin a kan hakan. Ko wannan aiki yana halatta, ko kuwa ba ya halatta?
Amsa: Wannan addu'ar jam'i bayan gama halkar da aka ambata ta karatun Kur'ani wajibi ne a bar shi, amma babu laifi ko wane mutum ya yi tasa addu'ar ga kansa shi kadansa bayan gama karatun Kur'ani Mai girma, ko ma cikin wasu halayen koma bayan hakan, saboda Addu'ah ibada ce, kuma ita addu'ah ana son yin ta a ko wane lokaci, musamman ma bayan kare Ibadah)). Intaha.
Muna fata za a dubi fatawowin nan da idanun basira, da kuma jingine dukkan wani nau'i na ta'assubanci.

FA'IDAH:
Idan wani ya ce don me za ku hana bude tare ko rufe taro da addu'a kullum-kullum? Alhali kuwa Imamut Tabaraanii ya ruwaito hadithi na 3,456 cikin Almu'ujamul Kabiir daga Habiib Dan Maslamah ya ce:-
((سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: لا يجتمع ملا فيدعو بعضهم ويؤمن سائرهم الا أجابهم الله)).
Ma'ana: ((Na ji Manzon Allah mai tsira da amincin Allah yana cewa: Wasu mutane ba za su hadu ba sashinsu yana addu'a sauran kuma na cewa amiin face sai Allah Ya karba msu)). Intaha.

Amsa a kan wannan sai a ce: 
Na farko dai: wannan hadithi dha'ifi ne ba zai yiwu a kafa hujja da shi ba. Albani ya raunana shi cikin Silsilah Dha'ifah 12/940, da kuma cikin Dha'ifut Targibi wat Tarhib1/70. 
Na biyu kuma da ma hadithin zai inganta to da sai a ce hadithin yana nufin guraren da Shari'ah ta zo da yin addu'a cikin jam'i ne kawai, watau kamar addu'ar da ake yi a cikin kuniti, ko kuwa addu'ar da ake yi cikin sallar neman ruwan sama, da makamcin hakan. 

Allah Ka taimake mu Ka nuna mana gaskiya gaskiya ce, Ka ba mu ikon bin ta, sannan Ka nuna mana karya karya ce Ka ba mu ikon kin ta. Am

No comments: