Friday, 18 January 2013

BAYANI A KAN BUKIN MAULIDI KASHI NA DAYA: (1)

BAYANI A KAN BUKIN MAULIDI KASHI NA DAYA: (1)

Yau alhamis 5/3/1434 H 17/1/2013 M tsakaninmu da ranar goma sha biyu ga watan Rabii'ul Awwal kwana 7 ne kacal, sannan kamar yadda aka sani ne cewa wannan rana ta 12/3/ ita ce ranar da wasu daga cikin masu ikirarin Musulunci ke bukin ranar haifuwar Annabi Muhammad mai tsira da amincin Allah, saboda neman lada da falala a wurin Allah, duk kuwa da cewa rikon wannan rana a matsayin Idi bidi'a ne wurin dukkan Maluman Musulunci! Allah Sarki! Haka dai Haidan yake badda mutane cikin mamaki wani lokaci! Allah Madaukakin Sarki yana cewa cikin Suratu Faatir aya ta 8:-
((أفمن زين له سوء عمله فراه حسنا فان الله يضل من يشاء ويهدي من يشاء فلا تذهب نفسك عليهم حسرات ان الله عليم بما يصنعون)).
Ma'ana: ((yanzu wanda aka kawata masa mummunan aikinsa har ya gan shi wani abu Mai kyau "yana daidai da waninsa?" saboda haka lalle Allah yana batar da wanda yake so, kuma ya shiryar da wanda yake so, kada ranka ya halaka a kansu saboda bakin ciki. Lalle Allah Masani ne ga abin da suke sana'antawa)). Intaha.

Ni a nan, a bisa dogara da ayah ta 104 a cikin Suratu Aali inda Allah Madaukakin Sarki Ya ce:-
((ولتكن منكم أمة يدعون الى الخير ويأمرون بالمعروف وينهون عن المنكر وأولئك هم المفلحون)). 
Ma'ana: ((A samu wata al'umma daga cikinku da za ta yi kira zuwa ga alheri, sannan ta umurni da abin da Shari'ah ta sani, kuma ta yi hani ga abin da Shari'ah bata sani ba. To su wadannan Al'umma sune masu rabauta)). Intaha. Da kuma dogara kan aya ta 78, da 79 cikin Suratul Maa'idah inda Allah Madaukaki ya yi maga a kan Banuu Isaraa'iil ya ce:-
((لعن الذين كفروا من بني اسرائيل على لسان داود وعيسى ابن مريم ذلك بما عصوا وكانوا يعتدون. كانوا لا يتناهون عن منكر فعلوه لبئس ما كانوا يفعلون)).
Ma'ana: ((An la'anci wadanda suka kafirta daga Banu Isaa'iil a bisa harshen Daawuuda da Isa Dan Maryam, saboda irin yadda suka yi sabo, suka kasance suna ketare iyaka. Suka kasance ba sa hana juna yin mummunan aikin da suke aikatawa. Wallahi abin da suka kasance suna aikatawa ya yi muni)). Intaha. Da kuma dogara kan hadithin da Imam Muslim ya ruwaito hadithi na 49 inda Annabi mai tsira da amincin Allah yake cewa:-
((من رأى منكم منكرا فليغيره بيده فان لم يستطع فبلسانه فان لم يستطع فبقلبه وذلك اضعف الايمان)). 
Ma'ana: ((Wanda duk ya ga munkari daga cikinku sai ya jirkita shi da hannunsa, in kuma ba zai iya ba, sai ya jirkita shi da harshensa, in kuma ba zai iya ba sai ya jirkita shi da zuciyarsa, wannan shi ne mafi raunin Imani)). Intaha. Da kuma dogara kan maganar Sahabin Annabi Abdullahi Dan Mas'ud Allah ya kara masa yarda, wacce ta zo cikin littafin Ibnu Wadh,dhah shafi na 11 da littafin Ali'itisaam na Imamush Shaatibii 1/107 inda ya ce:-
((اتبعوا ولا تبتدعوا فقد كفيتم)).
Ma'ana: ((Ku bi -abin da Annabi ya zo da shi- kada ku kirkiri bidi'ah, domin an gama muku kome -na addini-)). Dankuma dogara har yanzu a kan maganar shi Sahabi Abdullahi Dan Mas'uud wacce ta zo cikin littafin Ibnu Wadh'dhah shafi na 11 da kuma Sunanud Daarami 1/68-69 a inda ya ce lokacin da ya wuce wani mai wa'azi a cikin masallaci yana ce wa mutane: ku yi Subhanallah kafa goma, ku yi la'laha illalah kafa goma, sai ya ce da su:-
((ويحكم يا أمة محمد ما اسرع هلكتكم ! هؤلاء صحابة نبيكم صلى الله عليه وسلم متوافرون وهذه ثيابه لم تبل وأتيته لم تكسر والذي نفسي بيده انكم لعلى ملة هي أهدى من ملة محمد او مفتتحوا باب ضلالة. قالوا يا أبا عبد الرحمن ما اردنا الا الخير قال وكم مريد للخير لن يصيبه ان رسول الله صلى الله عليه وسلم حدثنا ان قوما يقرءون القران لا يجاوز تراقيهم وايم الله ما ادري لعل اكثرهم منكم ثم ولى عنهم)).
Ma'ana: ((kaitonku ya ku al'ummar Muhammad mamakin saurin halakarku! Wadannan Sahabban annabinku ne mai tsira da amincin Allah ga su nan da yawa, wadannan tufafinsa ne ba su gama yagewa ba, wadannan butocinsa ne ba su gama fashewa ba. Ina rantsuwa da Wanda raina yake hannunsa lalle ne ku ko dai kuna kan wani addini ne da ya fi addinin Muhammad shiriya ko kuwa ku masu bude kofar bata ne. Sai suka ce wallahi baban Abdurrahman babu abin da muke nufi sai alheri. Sai ya ce ai da yawa mai son alheri ba zai taba samun sa ba. Lalle Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya gaya mana cewa akwai wasu mutane da za su rika karanta Alkur'ani amma kuma ba zai wuce makogoronsu ba, Ina rantsuwa da Allah watakila mafi yawansu daga cikinku suke. Daga nan sai ya juya ya bar su)). Intaha. Da kuma dogara kan maganar babban Taabi'ii Hasanul Basarii wacce ta zo cikin littafin Ibnu Wadh'dhah, da littafin Alitisam na Shaatibii 1/111 inda ya ce: ((Mai yin bidi'ah ba zai Kara kokari cikin azuminsa na bidi'ah ba, ko sallarsa ta bidi'ah ba, face hakan ya nisantar da shi daga Allah)). Intaha.

Dogara kan wadannan ayoyi da hadithai da maganganun Sahabbai da Taabi'ai da kuka ji su yanzu ne ya sa muke gargadin Al'ummar Musulmi, muke hana su rikon ranar haihuwar Manzon Allah Mai tsira da amincin Allah a matsayin ranar Idi, muke musu gargadin rikon bukin maulidi a matsayin wani abu na addini da ake neman lada da shi a wurin Allah Madaukakin Sarki! 

Saboda abu ne tabbatacce wurin Maluman Musulunci cewa Annabi Mai tsira da amincin Allah bai yi bukin maulidi ba, Sahabbai ba su yi bukin maulidi ba, Taabi'ai ba su yi bukin maulidi ba, Taabi'ut Taabi'in ba su yi bukin maulidi ba. Duk kuwa abin da ba zama addini ba a zamanin Sahabbai, da Taabi'ai, da Taabi'ut Taabi'in tare da kasancewar sababin yin sa a lokacin nasu' da kuma ikon yin sa daga gare su yana nan' amma kuma babu Wanda ya yi shi daga cikinsu, to lalle wannan abin babu ta yadda za a yi ya zamanto addini karbabbe a wurin na bayansu har zuwa tashin Kiyama.

Yan'uwa Musulmi! Lalle shi rikon ranar maulidi a matsayin Idi, da maida shi ranar buki, ba a fara yin shi ba cikin wannan Al'umma sai cikin karni na hudu na hijirar Annabi Mai tsira da amincin Allah' watau sai a cikin shekara ta dari uku da settin da biyu (362). Sannan mutumin da ya fara yin wannan buki na maulidi shi ne wani sarki dan Shi'ah Fadimiyyah Mai suna Almu'izzu li Dininl Lah a garin Alkahira' kamar yadda yake rubuce cikin littattafan Musulunci da tarihi, da wasunsu, kuna iya duba wadannan littattafan:-
المواعظ والاعتبار بذكر الخطط والاثار للمقريزي ١/ ٤٩٠، وصبح الأعشى في صناعة الإنشاء للقلقشندي ٣/ ٤٩٨، وتاريخ الاحتفال بالمولد النبوي للسندوبي ص٦٩، وأحسن الكلام فيما يتعلق بالسنة والبدعة من الأحكام لمحمد بخيت ص٤٤، ٤٥، والمحاضرات الفكرية للشيخ علي فكري ص٨٤، والإبداع في مضار الابتداع للشيخ علي محفوظ ص١٢٦، والتاريخ العباسي والفاطمي للشيخ احمد مختار العبادي ص٢٦١، ٢٦٢.
Almawaa'izu wa Litibaar na Maqriizii 1/490, da Subhul A'ashaa na Qalqashandii 3/498, da Taariikhu Lihtifaali Bil Maulidin Nabawii na Sanduubii shafi na 69, da Ahsanul Kalam fi ma yataallaqu bis Sunnati wal Bidi'ati minal Ahkam na Muhammad Bakhiit shafi na 44,45, da Almuhadharaatul Fikriyyah na Ali Fikrii shafi na 84, da Al'ibdaa fi Madharri Libtidaa na Ali Mahfuuz shafi na 126, da Taarikhul Abbaasii wal Faatimii na Ahmad Mukhtaar Al'abbadii shafi na 261,262.

MALUMAN MUSULUNCI DABAN DABAN SUN HANA YIN BUKIN MAULIDI:

Yan'uwa Musulmi! Lalle da yawa daga cikin maluman Musulunci sun gargadi Al'umma sun hana su yin bukin maulidi da rikon shi a matsayin wata ibadah da za a nemi lada wurin Allah da ita, kuma sun bayyanar da cewa yin bukin maulidi bidi'a ce kuma bata.
Daga cikin wadannan malamai akwai manya manyan malumanmu na mazhabar Malikiyyah, kamar Ibnul Hajj wanda ya rasu a shekarar hijira ta 732 watau yau da rasuwarsa shekaru 702 ke nan da suka wuce, da kuma Umarul Faakihaanii wanda ya rasu a shekarar hijira ta 734 watau yau da mutuwarsa shekara 700 ke nan da suka wuce, da kuma Ibraahimush Shaatibii wanda ya rasu a shekarar hijira ta 690 watau yau da rasuwarsa shekara 744 ke nan da suka wuce, da kuma uwa-uba Sheik Uthmanu Dan Fodiyo wanda ya rasu a shekarar hijira ta 1234 watau yau shekara 201 ke nan da rasuwarsa.

Amma Sheik Ibnul Hajj ga abin da yake cewa cikin littafin Almudkhal 2/2, da 2/10-11 :-
((ومن جملة ما احدثوه من البدع مع اعتقادهم ان ذلك من اكبر العبادات واظهر الشعائر ما يفعلونه في شهر ربيع الاول من المولد وقد احتوى على بدع ومحرمات جملة فمن ذلك استعمالهم المغاني ومعهم آلات الطرب)) الى ان قال: ((وان خلا منه وعمل طعاما فقط ونوى به المولد ودعا اليه الاخوان وسلم من كل ما تقدم ذكره فهو بدعة بنفس نيته فقط إذ ان ذلك زيادة في الدين وليس من عمل السلف الماضين واتباع السلف اولى بل أوجب من ان يزيد نية مخالفة لما كانوا عليه لأنهم اشد اتباعا لسنة رسول الله صلى الله عليه وسلم وتعظيما له وسنته صلى الله عليه وسلم ولهم قدم السبق في المبادرة الى ذلك ولم ينقل عن احد منهم انه نوى المولد ونحن لهم تبع فيسعنا ما وسعهم)). 
Ma'ana: ((Yana daga cikin jumlar abin da suka kirkira na bidi'o'i tare da akidar cewa hakan yana daga cikin manyan ibadodi, kuma yana daga cikin alamomin Musulunci mafi fita fili: abin nan da suke aikatawa cikin watan Rabii'ul Awwal na bukin maulidi. Shi dai maulidi ya tattari abubuwan haramun da yawa a dunkule, daga cikinsu akwai wake-wake da suke yi tare da Kayan kade-kade .... To amma idan yin maulidi ya wifinta daga yin wake-wake tare da kayan kade-kade mai yin maulidin ya yi abinci kawai ya yi nufin maulidi da shi ya kira yan'uwa zuwa cin abincin, to, yin hakan ya zama bidi'ah saboda niyyar maulidin da ya yi, domin niyyar maulidin kari ne a cikin Addini ba ya kuma daga cikin ayyukan Salaf Magabata ba, bin Magabata kuwa shi ne ya fi dacewa, kai shi ne ma wajibi da a ce mutum zai kara wani abu sabanin abin da suka kasance a kansa, domin su Magabata su ne suka fi kowa yin koyi da Manzon Allah, kuma su ne suka fi kowa girmama shi da girmama sunnarsa, kuma su suke da kafar rigaya wajen takawa zuwa ga abin da yake alheri ne, babu kuma mutum daya da ya ciro yin niyyar maulidi daga dayansu, mu kuwa sauran Musulmi mabiya ne gare su, dukkan abin da ya wadatar da su na addini shi ne zai wadatar da mu)). Intaha.

Sannan Imamul Faakihaanii ya ce cikin Risalarsa ta maulidi mai suna Almurid fil Kalaami alaa Hukmil Maulid :-
((لا اعلم لهذا المولد اصلا في كتاب ولا سنة ولا ينقل عمله عن احد من علماء الامة الذين هم القدوة في الدين المتمسكون بآثار المتقدمين بل هو بدعة احدثها البطالون وشهوة نفس اعتنى بها الاكالون بدليل انا اذا أدرنا عليه الأحكام الخمسة قلنا اما ان يكون واجبا او مندوبا او مباحا او مكروها او محرما وهو ليس بواجب إجماعا ولا بمندوب لان حقيقة المندوب ما طلبه الشرع من غير ذم على تركه وهذا لم يأذن فيه الشرع ولا فعله الصحابة ولا التابعون ولا العلماء المتدينون فيما علمت وهذا جوابي عنه بين يدي الله ان عنه سئلت ولا جائز ان يكون مباحا لان الابتداع في الدين ليس مباحا بإجماع المسلمين فلم يبق الا ان يكون مكروها او حراما)). انتهى.
Ma'ana: ((Ban san wata hujja da za ta halatta yin maulidi ba a cikin Alkur'ani da Sunnah, kuma ba a nakalto yin bukin maulidi koda daga mutum daya ba cikin maluman Al'umma wadanda su ne abin koyi a cikin Addini , kuma su ne ke riko da maganganun magabata, kai, abin da dai yake ciki shi ne: shi dai maulidi wata biri'ah ce da marasa aikin yi suka kirkira kuma sha'awar son rai ce da masu cin dukiyar mutane cikin karya suka runguma, saboda shi dai bukin maulidi idan muka shimfida shi a kan hukunce-hukuncin nan guda biyar sai mu ce: ko dai ya zama wajibi, ko kuwa ya zama mustahabbi, ko kuwa ya zama mubaahi, ko kuwa ya zama makruuhi, ko kuwa ya zama haraamun, to in mun yi hakan za mu ga cewa shi dai ba wajibi ba ne bisa Ijmaa'in Malamai, shi kuwa ba mustahabbi ba ne domin abin da ake nufi da mustahabbi shi ne abin da Shari'ah ta ce a yi ba tare da an zargi Wanda ya ki yi ba, shi kuwa maulidi Shari'ah ba ta ce a yi shi ba, kuma ni a sanina Sahabbai, da Taabi'ai, da malamai masu riko da Addini ba su yi shi ba, wannan shi ne jawabina a gaban Allah a kan bukin maulidi in har aka tambaye ni. Kuma ba zai halatta ba a ce Maulidi ya zama mubaahi saboda kirkiran wani abu cikin addini ba zai zama mubaahi ba a bisa Ijmaa'in Musulmi, saboda haka babu abin da ya rage face maulidi ya zama makruuhi ko kuwa haramun)). Intaha.

Sannan Imamush Shaatibii ya ce -a lokacin da yake yin bayanin ma'anar bidi'ah- cikin littafinsa mai suna Alitisam 1/50,53 :-
((عبارة عن طريقة في الدين مخترعة تضاهي الشرعية يقصد بالسلوك عليها المبالغة في التعبد لله سبحانه.... يعني انها تشابه الطريقة الشرعية من غير ان تكون في الحقيقة كذلك بل هي مضادة لها من أوجه متعددة .... منها التزام الكيفيات والهيئات المعينة كالذكر بهيئة الاجتماع على صوت واحد واتخاذ يوم ولادة النبي صلى الله عليه وسلم عيدا وما أشبه ذلك)). انتهى.
Ma'ana: ((Bidi'ah wata kirkirarriyar hanya ce cikin addini mai kama da addinin gaskiya ana nufin kaiwa matuka matuka cikin bautar Allah da yin ta .., ina nufin ita bidi'ah tana kama da hanyar Shari'ah ba tare da ta kasance hanyar Shari'ah ta hakika ba, kai a gaskiya ma tana karo ne da hanyar Shari'ah ta fiskoki da yawa ... Daga cikinsu akwai lazimtar wasu irin siffofi ayyanannu, kamar zikirin da ake yi a bisa tsarin haduwa a kan sauti daya' da kuma rikon ranar haihuwar Manzon Allah mai tsira da amincin Allah a matsayin idi, da abin da yake Kama da haka)). Intaha.

Sannan Shehu Uthmanu Dan Fodiyo ya ce cikin littafinsa mai suna Ihyaaus Sunnah wa Iqmaadul Bid'ah shafi na 104 :-
((فان قلت ما حكم ما يفعل الناس في شهر ربيع الاول في يوم المولد او اليوم السابع من المولد من اجتماع الناس للذكر والطعام الذي يعملونه لذلك؟ قلت: انه بدعة مكروهة ان خلا عن كل معصية. وقيل: ان الصواب ان عمل المولد الشريف النبوي من البدع الحسنة المندوبة اذا خلا عن معصية. وأما ما يعتاده الناس في هذا الزمان في ذلك من اختلاط الرجال والنساء فمعاذ الله ان يقول احد بجوازه)). انتهى.
Ma'ana: ((Idan ka ce: Mene ne hukuncin abin da mutane suke yi a cikin watan Rabii'ul Awwal a ranar maulidi ko kuwa a ranar bakwai ga maulidi na taruwar jama'a saboda yin zikiri da cin abincin da aka yi tanadinsa saboda hakan? Sai in ce: Wannan bidi'ah ce makruuhiyah in yin maulidin ya wofinta daga dukkan sabon Allah. Amma kuma wasu sun ce: Abin da yake daidai shi ne shi bukin maulidin Annabi yana daga cikin bidi'o'i masu kyau matukar dai ya wofinta daga ko wane sabon Allah. To amma abin da mutane suka Saba yin shi a maulidi a wannan zamani na cakuda tsakanin maza da mata a'uuzu billahi da wani mutum zai ce halal ne)). Intaha.
Wannan shi ne abin da malumanmu na mazhabar Malikiyyah suka fada game da bukin maulidi. 

Sannan Shaikhul Islam Ibnu Taimiyah wanda ya rasu a shekarar hijira ta 728 watau shekaru 706 ke nan da suka wuce shi ya yi maganar maulidi ya kuma tabbatar da cewa maulidi bidi'ah ce, ya rubuta cikin littafinsa mai suna Iqtidhaa'us Siraa'til Mustaqiim 2/123-124 :-
((وكذلك ما يحدثه بعض الناس اما مضاهاة للنصارى في ميلاد عيسى عليه السلام واما محبة للنبي صلى الله عليه وسلم وتعظيما والله قد يثيبهم على هذه المحبة والاجتهاد لا على البدع من اتخاذ مولد النبي صلى الله عليه وسلم عيدا مع اختلاف الناس في مولده فان هذا لم يفعله السلف مع قيام المقتضي له وعدم المانع منه لو كان خيرا ولو كان هذا خيرا محضا او راجحا لكان السلف رضي الله عنهم احق به منا فانهم كانوا اشد محبة لرسول الله صلى الله عليه وسلم وتعظيما له منا وهم على الخير احرص وانما كمال محبته وتعظيمه في متابعته وطاعته واتباع أمره وإحياء سنته باطنا وظاهرا ونشر ما بعث. به والجهاد على ذلك بالقلب واليد واللسان فان هذه طريقة السابقين الأولين من المهاجرين والأنصار والذين اتبعوهم بإحسان)). انتهى. 
Ma'ana: ((Haka nan abin da sashin mutane ke kirkira ko dai saboda koyi da Kiristoci cikin bukin Kirsimeti' ko kuwa saboda son Annabi mai tsira da amincin Allah da girmama shi, zai yiwu Allah ya ba su lada a kan nuna kokari da soyayya' amma ba zai ba su lada a kan bidi'o'in rikon maulidin Annabi mai tsira da amincin Allah a matsayin idi ba duk da yake ma masu tarihi sun yi sabani a kan wace rana ce da wani wata ne aka haife shi! Shi dai bukin maulidi babu wani daga cikin magabata da ya yi shi duk kuwa da cewa dukkan dalilan da ake bayarwa na yin bukin a yanzu akwai su a wancan lokacin ma, kuma babu wani abu da zai hana su yin bukin inda yin shi alheri ne. Lalle ne da yin bukin maulidi tsantsar alheri ne to da Salaf Magabata su suka fi cancantar yin sa a kanmu, saboda sun fi mu son Manzon Allah mai tsira da amincin Allah da girmama shi, kuma sun fi kowa son aikata alheri. Lalle cikar soyayya da girmamawa ga Annabi tana cikin bin shi ne da yi masa da'ah da bin umurnin shi, da raya sunnar shi ciki da waje, da yada abin da aka aiko da shi, da yin jihadi da zuciya, da hannu, da harshe a kan hakan wannan ita ce hanyar Magabata na farko daga cikin Muhajirai da Ansarawa da wadanda suka bi su da kyautayi)). Intaha.

Yan'uwa Musulmi! Wannan shi ne matsayin bukin maulidi daga bakunan wadannan gagga-gaggan maluman Musulunci, tare ma kuma da cewa Maluman tarihi da siiirah sun yi sabani game da ranar haihuwar shi Annabi mai tsira da amincin Allah, a inda wasu suka ce: 
1- An haife shi ne a ran biyu ga watan Rabii'ul Awwal. 
2- Wasu kuwa suka ce an haife shi ne a ran takwas ga watan Rabii'ul Awwal.
3- Wasu kuwa suka ce an haife shi ne a ran goma ga watan Rabii'ul Awwal.
4- Wasu kuwa suka ce an haife shi ne a ran goma sha biyumga watan Rabii'ul Awwal.
5- wasu kuwa suka ce an haife shi ne a ran goma sha bakwai ga watan Rabii'ul Awwal.
6- Wasu kuwa suka ce an haife shi ne a ran ashrin ga watan Rabii'ul Awwal.
7- Wasu kuwa suka ce an haife shi ne a ran goma sha biyu ga watan Ramadhan.
Domin ganin wannan sabanin sai ku dubi littafin Taariikhul Islam na Imamuz Zahbii a Juz'in Siirah shafi na 25-27, da kuma littafin Albidaayatu wan Nihaayatu na Alhaafiz Ibnu Katheer 2/662.

Yan'uwa Musulmi! Kauli daidai har bakwai a kan ranar haihuwar Annabi mai tsira da amincin Allah babu kuma wani wanda ya isa ya ce: wannan kauli shi ne hakikanin gaskiya wancan kaulin kuma ba gaskiy ba ne, saboda abu ne da ya faru kafin zuwan Musulunci kuma bayan shi Musulunci ya zo bai tabbatar da ranar haihuwar ba ta hanyar wahayi saboda rashin muhimmancin yin hakan a cikin Addini. 
Ke nan ware wata rana daga cikin ranakun nan da aka ambata da riyawar cewa ita ce ranar da aka haifi Manzon Allah mai tsira da amincin Allah akwai nau'i na karya da shedan zur a cikin yin hakan. Allah ya tsare mu da son zuciya. 

Wannan shi ne kashi na farko game da bayananmu a kan bukin maulidi, kashi biyu na tafe in sha Allahu Ta'ala, kuma zai yi bayani ne game da shubuhohin da yan bidi'ah ke ambatawa domin tabbatar da bidi'ar maulidi. 

Allah Ya nuna mana gaskiya gaskiya ce ya ba mu ikon

No comments: