USKUREN FAHIMTAR NASSIN ALKUR'ANI KO SUNNAH NA WASU MUTANE
GAME DA BAYANAN DA MALAMAI SUKA YI NA HUKUNCIN MAIDA BUDE TARO KO RUFE SHI DA ADDU'A CIKIN JAM'I WATA SUNNAR DA AKE MAIMAITAWA A KULLUM
'Yan'uwa Musulmi! Abin da malaman Sunnah suke cewa shi ne: A daina rikon bude taro ko rufe shi da addu'a a matsayin wata Sunnar da maimaitawa a kullum, ta yadda imma ba a yi addu'ar ba sai a rika ganin an bar wata falala mai yawa ta wuce, alhalin shi wannan lamari na bude taro da addu'a babu inda aka ga cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya yi shi koda sau daya ne duk kuwa da cewa yana da damar yin hakan da yin hakan wani alheri ne, ke nan malaman Sunnah sun fahimta daga hakan cewa: Sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah cikin mas'alar ita ce rashin aikata hakan, domin kamar yadda daliban ilmi ne suka san cewa: wani lokaci Sunnah ta kan kasance ne ta hanyar bari, wani lokacin kuwa ta kan kasance ne ta hanyar yi.
Babban Malami a duniyar Sunnah Shaikhul Islam Ibnu Taimiya -Allah Ya yi masa rahama- ya ce cikin littafinsa Majmuu'ul Fataawa 26/172 :-
((والترك الراتب سنة، كما ان الفعل الراتب سنة، بخلاف ما كان تركه لعدم مقتض، او فوات شرط، او وجود مانع، وحدث بعده من المقتضيات والشروط وزوال المانع ما دلت الشريعة على فعله حينئذ، كجمع القران في المصحف، وجمع الناس في التراويح على امام واحد، وتعلم العربية وأسماء النقلة للعلم، وغير ذلك مما يحتاج اليه في الدين، بحيث لا تتم الواجبات او المستحبات الشرعية الا به، وانما تركه صلى الله عليه وسلم لفوات شرطه او وجود مانع. فأما ما تركه من جنس العبادات مع انه لو كان مشروعا لفعله او اذن فيه ولفعله الخلفاء بعده والصحابة، فيجب القطع بان فعله بدعة وضلالة)). انتهى.
Ma'ana: ((Dawwamanmen bari Sunnah ce, kamar yadda dawwamanmen aiki yake Sunnah, sabanin abin da barin shi ya kasance ne saboda rashin bukatar yin shi, ko kuwa saboda rashin sharadin yin shi, ko kuwa saboda samuwar abin da ya hana yin shi, sannan bayan (mutuwar Annabi) bukatar yin hakan ta taso, ko sharadin yin hakan ya samu, ko abin da ke hana yin hakan ya kau, ta yadda Shari'ah za ta nuna halaccin yin shi, kamar hada Alkur'ani a Mus'hafi, da hada mutane bayan limami daya a cikin sallar tarawihi, da koyon ilmin Larabci, da haddace sunayen masu nakalto ilmi, da wanin wannan daga cikin abin da ake bukatarsa cikin Addini, ta yadda wajibai da mustahabbai na Shari'ah ba sa cika sai tare da shi, saboda da ma can (Manzon Allah) mai tsira da amincn Allah ya bar yin shi ne saboda kubucewar sharadinsa, ko saboda samuwar abin da ke hana yin shi. To amma abin da (Annabi) ya bari daga jinsin Ibadu tare da cewa da abin wani abu ne da ya dace da Shari'ah to da ya aikata shi, ko da ya ba da izinin a yi shi, kuma da ma Khalifofinsa da Sahabbai sun yi shi a bayansa, (irin wannan kam) wajibi ne a tabbatar da cewa lalle yin shi bidi'ah ce kuma bata)). Intaha.
Da wannan magana ta Shaikhul Islam Ibnu Taimiya za mu fahimci cewa: Sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah cikin bude taro ko rufe taro da addu'ah ita ce: Barin yin hakan, saboda masu yin haka suna ganin wata ibada suke yi saboda su samu biyan bukatar Duniya da Lahira, wannan shi ya sa ma in sun ga wasu sun yi taro ba su yi ba sai su rika jin haushinsu, kai su ma rika zaginsu da yi musu jumhuru daban daban!!!
RADDI:-
Idan wani ya kafa hujja da hadithin Abdullahi Dan Umar wanda Tirmizi ya ruwaito cikin Sunan hadithi na 3,502, da kuma Nasaa'i cikin Sunan hadithi na 10,234 cewa:-
((قلما كان رسول الله صلى الله عليه وسلم يقوم من مجلس حتى يدعو بهؤلاء الدعوات لأصحابه: اللهم اقسم لنا من خشيتك ما تحول به بيننا وبين معاصيك، ومن طاعتك ما تبلغنا به جنتك، ومن اليقين ما تهون به مصائب الدنيا، ومتعنا باسماعنا وابصارنا وقوتنا ما احييتنا، واجعله الوارث منا، واجعل ثارنا على من ظلمنا، وانصرنا على من عادانا، ولا تجعل مصيبتنا في ديننا، ولا تجعل الدنيا اكبر همنا ولا مبلغ علمنا، ولا تسلط علينا من لا يرحمنا)). انتهى.
Ma'ana: ((Kadan ne za a ce Mnazon Allah mai tsira da amincin Allah ya tashi daga wata majalisa ba tare da ya yi wa Sahabbansa addu'a da wadannan addu'o'i ba: Ya Allah Ka ba mu wani abu na tsoronKa da zai shiga tsakaninmu da sabonKa, da wani abu na da'arKa da zai kai mu aljannarKa, da wani abu na yakini da zai kai saukaka mana musibun Duniya, ka jiyarda mu dadi da jinmu, da ganinmu, da karfinmu matukar dai Ka rayar da mu, Ka zamar da shi mai gado gare mu, Ka sanya ramuwar gayyarmu a kan wanda ya zalunce mu, Ka taimake mu a kan wanda ya nuna mana kiyayya, kada Ka sanya musibarmu a cikin addininmu, kada Ka sanya Duniya mafi girman hamminmu, ko iya matukar ilminmu, kada Ka dora wanda ba ya tausaya mana a kanmu)). Intaha.
Idan wani ya kafa hujja da wannan hadithin to sai a ce da shi: Shi wannan hadithin abin da kawai ya ce shi ne: "Yan lokuta kadan ne za ce Annabi ya tashi daga wata majalisa ba tare da ya yi wa sahabbansa addu'a ba" hadithin bai ce Annabi yana ce wa sahabbansa ne: ku yi salati goma-goma sannan ya rika yin addu'a su kuma suna cewa: ameen ba!!! Babu wani magabaci da ya yi wa hadithin wannan fahimta, babu kuma wani malami daga cikin masu yi wa hadithai sharhi -a iya sanina- da ya yi wa hadithin wannan fahimta, babu daya daga cikin maluman Da'awah da Aqidah da ya yi wa hadithin wannan fahimta!!! Sannan ko shakka babu da da wannan surar ce Annabi yake yin addu'ar to da an nakalto mana ita, saboda sura ce mai jan hankulan mutane sosai, domin kowa ya kan bar abin da yake yi ne domin ya saurari mai yin addu'a bayan ya yi salati sannan kuma ya rika fadar ameen.
Sannan a cikin hadithin an ce:-
((من مجلس))
Watau: daga ma ko wace majlisa. Ke nan wannan ya hada da majalisar tattauna lamuran duniya na yau da gobe, da majalisar wani darasi, da majalisar koma mene ne. In da kuwa lalle yana yin addu'ar ne a bisa surar da muke yi, to da kuwa an nakalto mana ita. Sannan kuma da Malumanmu na Da'awah da Aqidah ba su hana yin addu'a cikin irin ita wannan surar ba a farko ko karshen majalisar wani darasi, ko majalisar karatun Kur'ani ba, da sauransu.
Sannan abu na biyu shi ne: Mene ne ya hada tsakanin cewa Annabi yana yi wa Sahabbansa addu'a cikin mafi yawan majalisu, da kuma cewa Annabi yana addu'ar bude taro da rufe taro cikin jam'i, in ba ta'assubanci da son zuciya ba? Ga misali: Abu Dawuda ya ruwaito hadithi na 3,203, da Tirmizi hadithi na 1,024, da Nasa'ii hadithi na 1,986' da Ibnu Majah hadithi na 1,498, da Ahmad hadithi na 17,581 daga Sahabi Abu Hurairah da waninsa cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya kasance yana yi wa Sahabbai rayayyu da matattu maza da mata manya da yara addu'a cikin sallar janaza. Ga ma yadda nassin yake:-
((اللهم اغفر لحينا وميتنا وصغيرنا وكبيرنا وذكرنا وانثانا وشاهدنا وغائبنا. اللهم من احييته منا فاحيه على الايمان ومن توفيته منا فتوفه على الاسلام. اللهم لا تحرمنا اجره ولا تضلنا بعده)). انتهى.
Ma'ana: ((Ya Allah Ka gafarta wa rayayyunmu da matattunmu, da kanananmu da manyanmu, da mazanmu da matanmu, da halartattunmu da wadanda ba sa nan daga cikinmu. Ya Allah wanda Ka raya shi daga cikinmu to Ka raya shi a kan Imani, Wanda kuma Ka matar daga cikinmu to Ka matar da shi a kan Musulunci. Ya Allah kada Ka haramta mana ladansa, kada kuma Ka batar da mu bayansa)). Intaha.
A nan addu'a ce da Annabi yake yi wa Sahabbansa, rayayyu da matattu, amma kuma shi kadai yake yin ta ba ma dole ba ne jama'ar da ke tare da shi su abin da yake fada, kuma babu salatin Annabi goma-goma a cikinta, babu kuma fadar ameen daga sauran jama'a. Lalle yadda ita wannan addu'ar take to haka ma addu'ar:-
((اللهم اقسم لنا من خشيتك ما تحول به بيننا وبين معاصيك......)).
take, wannan shi ya sa ma su wadannan kalmomi ba sa canja wa, kamar yadda wadancan su ma ba sa canjawa.
Sannan abu na biyu shi ne: Akwai gurare da yawa da Annabi mai tsira da amincin Allah yake yi wa Sahabbai addu'a, to amma maluman Sunnah ba su fahimci cewa addu'ar jam'i ne yake yi ba. Misali:-
1-Hadithi na 5108 da Abu Dawud ya ruwaito, na 4623 da Abu Ya'ala ya ruwaito cikin Musnad, na 140 da Ibnul Jaaruud ya ruwaiton cikin Muntaqa daga A'isha Allah Ya kara mata yarda ta ce:-
((كان رسول الله صلى الله عليه وسلم يؤتى بالصبيان فيدعو لهم بالبركة)). انتهى.
Ma'ana: ((Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya kasance ana zuwa masa da yara yana musu addu'ar samun albarka)). Intaha. Wannan hadithin Albanii ya inganta shi cikin Alkalimut Tayyib 1/162. Lalle a nan hadthin ba ya nufin jam'in addu'a Annabi yake yi watau ya umurci mutane su daga hannu suna cewa Ameen shi kuwa yana Ddu'a.
2-Hadithi na 502 da Bukharii ya ruwaito cikin Al'adabul Mufrad, da hadithi na 9969 da Baihaqii ya ruwaito cikin Shu'abul Iman cewa:-
((جاءت الحمى الى النبي صلى الله عليه وسلم فقالت: ابعثني الى اثر اهلك عندك. فبعثها الى الأنصار فبقيت عليهم ستة ايام ولياليهن فاشتد ذلك عليهم فاتاهم في ديارهم فشكوا ذلك اليه، فجعل النبي صلى الله عليه وسلم يدخل دارا دارا وبيتا بيتا يدعو لهم بالعافية)). انتهى.
Ma'ana: ((Zazzabi ya zo gurin Annabi mai tsira da amincin Allah sai ya ce: aika ni zuwa ga mutanen da suka fi soyuwa gare ka. Sai ya aika da shi zuwa ga Ansarawa, ya je ya zauna a cikinsu yini shida da dare shida, hakan ya tsananta a kansu, sai ya je musu cikin unguwarsu, sai suka yi masa kukan wannan zazzabin. Sai Annabi mai tsira da amincin Allah ya rika shiga bangare bangare, gida gida yana musu addu'ar samun lafiya)). Intaha. Wannan hadithin Albaanii ya inganta shi cikin Silsilah Sahihah lamba na: 2502. A nan ma babu wani mai sharhin hadithai da ya ce addu'ar jam'i aka yi Annabi na addu'a saura jama'a na cewa: ameen.
3-Hadithi na 1668 da Malik ya ruwaito cikin Muwattaa, da hadithi na 17,959 da Tabaraanii ya ruwaito cikin Almu'ujamul Kabir, da hadithi na 9,503 da Abdur Razzaq ya ruwaito cikin Musannaf daga Abu Burdah cewa:-
((ان النبي صلى الله عليه وسلم يوم حنين أتى القبائل يدعو لهم)). انتهى.
Ma'ana: ((Annabi mai tsira da amincin Allah ya je wa Kabilu a ranar yakin Hunain yana musu addu'a)). Intaha. Mai littafin Majma'uz Zawaa'id 5/407 ya ce: Mazajen isnadin Mazajen Buharii da Muslim ne, in banda Abdullahi Ibnul Mugiirah shi kuwa thiqah ne. A nan ma babu wanda ya ce Annabi ya je yana addu'ar ne sannan ya umurci Kabilun da su rika cewa: ameen.
4- Hadithi na 4,546 da Haakim ya ruwaito cikin Mustadrak daga Waliid Dan Uqbah cewa:-
((لما فتح رسول الله صلى الله عليه وسلم مكة جعل اهل مكة يأتون بصبيانهم فيمسح رسول الله صلى الله عليه وسلم على رؤوسهم ويدعو لهم)). انتهى.
Ma'ana: ((Lokacin da Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya bude Makka, mutanen Makka sun yi ta kawo yaransu Manzon Allah yana ta shafan kawunansu yana musu addu'a)). Intaha. A nan ma babu wani mai sharhin hadithi da ya ce: Annabi ya ce su yi ta cewa ameen ne a lokacin da yake yi wa yaran nasu addu'a. watau babu wanda ya ce addu'ar jam'i Annabi ya yi.
AMSA KAN WATA MAGANAR KUMA
Idan wani ya kafa hujja da wadannan Nassosi kamar:-
((والذين جاءوا من بعدهم يقولون ربنا أغفرلنا ولاخواننا الذين سبقونا بالإيمان)). الحشر:١٠.
Ma'ana: ((Wadanda suka zo daga bayansu suna cewa: Ya Ubangijinmu! Ka gafarta mana, da kuma 'yan'uwanmu wadanda suka riga mu yin Imani)). Intaha. Da kuma:-
((قل ما يعبؤ بكم ربي لولا دعاؤكم)). الفرقان: ٧٧.
Ma'ana: ((Ka ce: Ubangijina ba ya kulawa da ku, in ba domin addu'arku ba)). Intaha. Da kuma:-
((واذا سالك عبادي عني فاني قريب أجيب دعوة الداع اذا دعان)). البقرة: ١٨٦.
Ma'ana: ((Idan bayiNa suka tambaye ka labariNa to Ni kusa Nake, kuma ina amsa addu'ar mai addu'a in ya kira Ni)). Intaha. Da kuma sauran Nassosi masu kama da haka ya ce kuma: Lalle mu muna hana a yi sa Musulmi addu'a ne, alhalin Allah Ya ce a roke Shi zai kuma amsa!!!
Farko dai sai a ce da su tarihi ne yake maimaita kan sa, tsakanin maluman Sunnah da kuma masu bidi'a da bautar son zuciya. Misali: lokacin da Shehu Uthmanu Dan Fodiyo ya ce cikin littafin shi Ihya'us Sunnah shafi na 102:-
((ومن ذلك الدعاء دبر الصلاة بكيفية معلومة وهو ان يدعو الامام ويؤمن الناس، وهو بدعة مكروهة في مذهب مالك)). انتهى.
Ma'ana: ((Daga cikin wannan akwai addu'a bayan Salla a bisa wani yanayi sananne, shi ne kuwa: Liman yana addu'a Mamu suna cewa ameen. Shi wannan bidi'a ce makruuhiya a cikin mazhabar Imam Malik)). Intaha. A lokacin da Shehu Dan Fodiyo da kuma ire-irensa suka fadi haka saboda neman jama'a su yi Musuluncisu kamar yadda Annabi da Sahabbai suka yi an samu wasu masu ta'assubanci wadanda kiyayya da hasada suka cika zukatansu, da suka ki yin aiki da wannan bayani na ilmi da so wa Musulmi alheri, suka koma suna ta kafa hujja da irin wadannan dalilai aammah, wadanda masu ilmi sun san cewa ba za nuni a kan bigiren da aka yi sabani a kan shi. Kamar dai mutumin da za ka ce da shi: ka daina yin Salatul fatih ka rika yin Salatin da Annabi mai tsira da amincin Allah ya koya wa Sahabbai. Sannan shi kuma ya rika gaya wa jama'a cewa: Kai din nan ka hana a rika yi wa Annabi salati!!! Ko kuma ka ce a daina zikirin bidi'ah na ihu da bugun kirji, ko bisa wani adadi wanda ba Shari'a ce ta bayyana ba. Sai kuma a ce: Kai din nan wai ka hana a yi wa Allah zikiri duk kuwa da cewa Nasosi da yawa sun yi umurni da yin hakan!!
Na biyu sai a ce da su: Irin wannan tuhumar ba sabon lamari ba ne ga Maluma masu da'awah wadanda suke kokarin maida mutane a kan Sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah cikin dukkan lamuransu. Imam Abdur Razzaq ya ruwaito cikin littafinsa Musannaf atharii na 4,755 da kuma Imamul Baihaqii a cikin Assunanul Kubra atharii na 4,621 daga Sa'id Dan Musayyib cewa:-
((انه رأى رجلا يصلي بعد طلوع الفجر اكثر من ركعتين يكثر فيها الركوع والسجود، فنهاه، فقال: يا محمد! يعذبني الله على الصلاة؟ قال: لا ولكن يعذبك على خلاف السنة)). انتهى.
Ma'ana: ((Ya ga wani mutum yana salla fiye da raka'a biyu bayan fitowar alfijir yana yawaita ruku'i da sujjada cikin sallar, sai ya hana shi. Sai mutumin ya ce: Ya Abu Muhammad! Yanzu a kan salla ne Allah zai azabtar da ni? Sai ya ce: A'a zai azabtar da kai ne a kan sabawa Sunnah)). Intaha. Sheik Albani bayan ya kawo wannan magana cikin littafinsa Irwa'ul Galil 2/236 kuma ya inganta isnadinta sai ya ce:-
((وهذا من بدائع أجوبة سعيد بن المسيب رحمه الله تعالى، وهو سلاح قوي على المبتدعة الذين يستحسنون كثيرا من البدع باسم انها ذكر وصلاة، ثم ينكرون على اهل السنة انكار ذلك عليهم، ويتهمونهم بانهم ينكرون الذكر والصلاة!! وهم في الحقيقة انما ينكرون خلافهم للسنة في الذكر والصلاة ونحو ذلك)). انتهى.
Ma'ana: ((Wannan yana daga cikin kyawawan jawaban Sa'idu Dan Musayyib Allah Madaukakin Sarki Ya yi masa rahama, sannan kuma shi makami ne mai karfi a kan 'yan bidi'a da suke ganin kyawun da yawa daga cikin bidi'o'i da sunan cewa: Ai zikiri ne, da Salla! Sannan kuma su yi wa Ahlus Sunnah inkarin inkarin da suke yi musu, kuma su tuhumce su da cewa: Suna hana zikirin Allah da kuma Salla!! Wanda kuma a gaskiyar al'amari su suna musu inkarin barin Sunnah ne da suka yi cikin Zikirin da kuma Sallar, da abin da ya yi kama da haka)). Intaha.
Muna rokon Allah Madaukakin Sarki ya nuna mana gaskiya gaskiya ce ya kuma ba mu ikon aiki da ita. Ya kuma nuna mana karya karya ce ya ba mu ikon guje mata. Ameen.
No comments:
Post a Comment