MAGANAR MANZON ALLAH ITA CE GABA
23/5/1434 H 4/4/2913 M
Alhafiz Ibnu Rajab wanda ya mutu a shekarar hijira ta 795 watau yau shekaru 639 ke nan da suka wuce, ya yi wa malamai wata maga da ya kamata a rubuta ta da ruwan zinari, ya ce cikin littafinsa mai suna Alhikamul Jadiratu Bil Iza'ah shafi na 12:-
((فالواجب على كل من بلغه امر الرسول صلى الله عليه وسلم وعرفه ان يبينه للامة وينصح لهم ويأمرهم باتباع أمره وان خالف ذلك رأي عظيم من الامة؛ فان امر رسول الله صلى الله عليه وسلم احق ان يعظم ويقتدى به من رأي اي معظم قد خالف أمره في بعض الاشياء خطا، ومن هنا رد الصحابة ومن بعدهم على كل مخالف سنة صحيحة، وربما اغلظوا في الرد لا بغضا له، بل هو محبوب عندهم معظم في نفوسهم، ولكن رسول الله احب اليهم وأمره فوق امر كل مخلوق، فإذا تعارض امر الرسول وأمر غيره فأمر الرسول اولى ان يقدم ويتبع ولا يمنع من ذلك تعظيم من خالف أمره وان كان مغفورا له، بل ذلك المخالف المغفور له لا يكره ان يخالف أمره اذا ظهر امر الرسول صلى الله عليه وسلم بخلافه)). انتهى.
Ma'ana: ((wajibi ne a kan dukkan wanda umurnin Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya isa zuwa gare shi, ya kuma san shi, ya bayyana shi ga Al'ummah, ya musu nasiha, ya umurce su da bin umurninsa koda kuwa hakan ya saba wa ra'ayin wani babba a cikin Al'ummah, saboda umurnin Manzon Allah mai tsira da amincin Allah shi ya fi cancantar a girmama shi, kuma a yi koyi da shi a kan ra'ayin dukkan wani wanda ake girmamawa amma kuma umurninsa ya saba wa umurnin shi cikin sashin lamura cikin kure, wannan shi ya sa ma Sahabbai da wadanda suka biyo bayansu suka yi wa dukkan wanda ya saba wa Sahihiyar Sunnah raddi, wani lokaci ma raddi mai kaushi, ba wai kuma saboda suna nuna kiyayya ba ce gare shi, a'a yana nan abin so a gare su kuma abin girmamawa a cikin rayukansu, to amma Manzon Allah shi ne mafi soyuwa a gare su, sannan umurninsa shi yake sama da umurnin ko wace halitta. Saboda haka idan umurnin Manzon Allah ya yi karo da umurnin waninsa, to umurnin Manzon Allah shi ya fi cancantar a gabatar kuma a bi, wannan kuwa ba zai hana a girmama mutumin da ya saba wa umurnin Manzon Allah ba matukar dai ana gafarta wa kuren cikin Sahari'ah, kuma shi wannan da ya yi sabon cikin kure ba zai nuna kyamar a saba wa umurninsa matukar dai umurnin Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya bayyana a matsayin mai saba masa)). Intaha.
Sannan shi ma Shehu Uthmanu Dan Fodiyo ya yi wata magana mai kyawun gaske wacce za ta amfanar da masu wa'azi a cikin littafin Ihya'us Sunnah shafi na 8:-
((قد انعقد الإجماع على ان آراء المجتهدين كلها مسالك الى الجنة وطرق الى الخيرات فمن سلك منها طريقا وصله الى ما وصلوا اليه حقاً ومن عدل عنه قيل له سحقا! ويجوز تقليدهم في كل رأي الا ما خالف نص القران او نص الحديث او القواعد او القياس الجلي، فافهم)). انتهى.
Ma'ana: ((Ijma'i ya kullu a kan cewa: dukkan ra'ayoyin Mujtahidai mashiga ce ta zuwa Aljanna, kuma hanyoyi ne na alkhairai, wanda duk ya bi wata hanya cikinsu tabbas za ta kai shi inda suka kai, wanda kuma ya baude ga barin su sai a ce da shi tir. Sannan yana halatta a yi koyi da su cikin ko wane ra'ayi, amma banda abin da ra'ayin da ya saba wa nassin Alkur'ani, ko nassin Hadithi, ko saba wa Ka'idodi, da Ijma'i, ko Kiyasi Jaliyyi, ka fahimta)). Intaha.
Dukkan abin da mutum ya san cewa: Annabi mai tsira da amincin Allah ya yi umurni da yin sa, to wajibi ne ya bayyanar da shi ga Al'ummah, da kuma za a samu wani mai son zuciya da zai yi kokarin hana shi yin hakan to ba zai saurara masa ba, wannan shi ne daidai kuma shi ne hanyar Annabi da sauran Maluman Sunnah kamar su Babban masani a ilmin Hadithi Ibnu Rajab.
Haka nan haramun ne a kan kowane Musulmi ya bi ijtihadin wani malami komin girmansa matukar dai ijtihadin ya saba wa nassin Alkur'ani, ko nassin Hadithi, ko nassin Ijma'i, ko Kiyasi Jaliyyi, kamar dai yadda Shehu Dan Fodiyo ya bayyana mana a yanzu.
Hakika, mun sani sau da dama karkatattu -mazansu da matansu, ubanninsu da 'ya'yansu, malumansu da jahilansu- cikin ko wane zamani suna amfani da lafazin "wane na raba kan Al'umma" ko "Wane ba ya son hadin kan Al'umma" saboda neman rufe wata barna da Sari'ar Musulunci ta ce a bayyana ta, ko saboda kare wata barna da Sari'ah ta ce yake ta, to amma irin wannan jinsi na mutane ba za a saurare su ba saboda dillacin Duniya ne yake gabansu. Lalle rashin sauraron wadannan 'yan hayaniya, shi ne hanyar Annabi mai tsira da aminci Allah, kuma shi ne hanyar Kungiyar Izala tun lokacin kafuwarta.
Alhafizu Ibnu Katheer ya ce cikin littafinsa Albidayatu wannihayah 3/55-56:-
((عن سعيد بن جبير وعكرمة عن ابن عباس قال: اجتمع علية من اشراف قريش وعدد أسماءهم بعد غروب الشمس عند ظهر الكعبة، فقال بعضهم لبعض: ابعثوا الى محمد فكلموه، وخاصموه حتى تعذروا فيه، فبعثوا اليه ان اشراف قومك قد اجتمعوا لك ليكلموك، فجاءهم رسول الله صلى الله عليه وسلم سريعا، وهو يظن انه قد بدا لهم في أمره بدء، وكان حريصا يحب رشدهم ويعز عليه عنتهم، حتى جلس اليهم. فقالوا: يا محمد انا قد بعثنا إليك لنعذر فيك، وانا والله لا نعلم رجلا من العرب ادخل على قومه ما أدخلت على قومك؛ لقد شتمت الآباء وعبت الدين، وسفهت الآلهة وفرقت الجماعة، وما بقي من قبيح الا وقد جئته فيما بيننا وبينك..)).
Ma'ana: ((Daga Sa'id Da Jubair da Ikrimah, daga Dan Abbas ya ce: Shugabannin Quraishawa sun hadu a Dakin Ka'abah, sannan suka aika wa Annabi mai tsira da amincin Allah cewa suna bukatar zama da shi, nan-da-nan Annabi mai tsira da amincin Allah ya je ya same su saboda tsammanin da yake yi na cewa za su musulunta ne, domin shi har kullum yana son musu alheri ne kuma ba ya son abin da zai wahalce su. Da ya zo ya zauna a inda suke sai suka ce da shi: Ya Muhammad! Lalle, mun aika Maka ne domin mu yanke uzurinmu gare ka, wallahi mu ba mu taba ganin wani mutum daga cikin Larabawa da ya kawo musiba cikin jama'arsa ba kamar yadda ka kawo musiba cikin jama'arka ba. Hakika ka zagi iyayenmu, kuma ka aibanta addininmu, sannan ka maida masu hankalinmu wawaye, ka kuma zagi allolinmu, ka raba kawunan jama'armu. Babu dai wani mummunan da ya rage wanda ba ka sanya shi tsakaninmu ba..)). Intaha.
Ku dubi wadannan mujrumai! Wai daga cikin laifukan da suke zargin Manzon Allah mai tsira da amincin Allah na yi shi ne: raba kawunan jama'a! saboda kawai ya ce: A bi Addinin gaskiya, kada a karbi umurnin kowa matukar ya saba wa umurnin Allah Madaukakin Sarki, da ManzonSa mai tsira da aminci.
Wannan ita ce al'adar karkatattu, sawa'un mushrukai ne su masu bautan gumaka, ko kuwa kafurai ne ma'abuta littafin, ko kuwa fasikai ne da 'yan bidi'ah cikin Al'ummar Musulmi. Wannan shi ya sa a shekarun farko na kafuwar Kungiyar Izala babban abin da 'yan bidi'ah da ma'abuta maslahar kai suke tuhumar masu wa'azi a cikinta da shi, shi ne: Su masu raba kawunan al'umma ne, masu bata tafiyar Al'ummar Musulmi ne, ba sa yin magana a kan abin da aka yi ittifaki a kan sa sun koma suna magana a kan sabanin fahimta, maimakon su shiga daji su musuluntar da maguzawa sai ga shi sun koma suna cewa wai Darikah ba ta da kyau, wai Shi'ah ba Musulunci ba be, wani abin dariya ma wai taron suna bidi'a ce! wai addu'a bayan salla cikin jam'i bidi'a ce, kai lalle wadannan mutane sun cika fitina tir da halayensu, kuma dole ne a hadu a yake su domin Musulmi su huta da musibarsu.
'yan'uwa masu kaunar Sunnah! Wannan shi ne abin da yake faruwa har kullum tsakanin masu neman a kudurta gaskiya, a kuma fadi gaskiya, sannan a yi aiki da gaskiya cikin dukkan kome. Ina fata ba ku manta da jigon makaalarmu ba, watau ta'ammulin maganar babban Malami Alhafiz Ibnu Rajab ba, da kuma babban Malami Uthmanu Dan Fodiyo ba. Allah Ka ba mu karfin aiki da gaskiya komin dacinta. Ameen.
No comments:
Post a Comment