Saturday, 20 April 2013

TA TUHUME NI DA CUTAR DA KE CIKIN JIKINTA SANNAN SAI TA KOMA GEFE 

20/4/2013

Akwai karin magana da Larabawa ke amfani da shi a lokacin da suka ga cewa wani mai aibi a jikinsa ya zargi abokin husumarsa da wannan aibin alhalin babu wannan aibin a cikin shi abokin husumar nasa. Suna cewa:-
((رمتني بدائها وانسلت))
Watau: ((Ta jefe ni da cutarta sannan ta koma gefe)).

Asalin wannan karin maganar shi ne: Akwai wani mutum da ake kira Sa'ad Dan Yazidu Manah, yana auren wata mata mai suna Ruhm Yar Khazraj ita mace ce mai kyawun gaske har ma ta haifa wa wannan miji nata wani yaro mai suna Malik, to ita Ruhm tana da kishiyoyi wadanda suke yawan aibanta ta da wani aibi da take da shi a bakin mahaifarta mai kama da gwaiwa saboda haka sai suna aibanta ta da wannan aibin suna kiran ta: "Ya Aflaa"! Watau Ya ke mai gwaiwar bakin mahaifa!!

To sai uwarta ta koya mata wata dabarar karya ta ce da ita: Ke Ruhm ga mafita nan: da zarar kin yi fada da wata kishiya daga cikin shiyoyinki, toh ki yi maza ki riga ta magana nan da nan ki ce da ita: Ya Aflaa!! Watau ja mani daga nan, mai gwaiwar bakin mahaifa kawai!!

Shi ke nan sai Ruhm ta riki wannan tarbiyyar karaya da uwarta ta koya mata, saboda haka da zarar ta bata da daya daga cikin kshiyoyin nan nata nan sai ta yi wuf ta ce da ita:- Ke! Bani wuri nan mai gwaiwar bakin mahaifa kawai!!! Sai ita kuma kishiyar ta tsaya tana mamakin wannan tsaurin ido na Ruhm tana cewa: Ta zage ni ta hanyar aibin da yake jikinta -ni kuwa babu shi a jikina saboda nuna tsaurin ido- sannan kuma ta yi mirsisi tamkar wata lafiyayya, mai kuma gaskiya cikin abin da ta fada!!
((رمتني بدائها وانسلت)).
Daga nan ne fa hakan ya zama karin magan a cikin Larabawa, ya zamanto dukkan wani mai wani aibi amma kuma sai ya zagi abokin husumarsa da wannan aibin to sai su ambaci wannan jumla:-
((رمتني بدائها وانسلت)).

SUN ZARGE MU DA SABA ALKAWARI, SUN KUMA ZARGE MU DA RASHIN SON HADUWAR KUNGIYAR IZALA!!!

Malam Sani Yahya Jingir da jama'arsa sun cutar da mu matuka, sun mana yarfe da jumhuri iri-iri, sun yi kokarin bata mana suna a idanun duniya ta hanyar daukan laifuffukansu suna dora mana. Zan dan ba ku misali kadan a wannan dan takaitaccen rubutu nawa domin lamarin cutarsu ya kara fita fili ga dukkan mai son gaskiya, da kuma kyamatar karya.

1. Sun zarge mu da cewa mu ba ma son hadin kan kungiyar izala!!
Alhali hakika tana bayyanar da cewa su din ne ba sa son hadin kan kungiyar izala ba wai mu ba, domin kuwa abin da ya faru shi ne: Yan kungiyar izala sun hadu a Masallacin Sultan Bello a karkashin jagorancin mutum 24 mutum 12 daga ko wane bangare a ranar 26/1/1433 H wanda ya yi daidai da 21/122011 M sannan suka zabi Sheik Abdullahi Bala Lau a matsayin shugaban kungiyar izala na kasa baki daya, suka kuma zabi Sheik Kabiru Haruna Gombe a matsayin babban sakataren kungiyar izala, suka kuma zabi Sheik Sani Yahya Jingir a matsayin shugaban majalisar malamai na kungiyar izala, suka kuma zabi M. Isa Waziri a matsayin darajtan yan agajin kungiyar izala. 

To amma sai daga baya wasu mutane suka koma gefe suka ce: Su kam shugabansu na kungiyar izala ba shi ne Sheik Abdullahi Bala Lau ba, a'a su shugabansu na kungiyar izala shi ne shugaban majalisar malaman kungiyar izalan watau Sheik Sani Yahya Jingir!!

Sannan kuma suka dinga yada cewa dukkn mutumin da ya yadda da cewa shi Sheik Abdullahi Bala Lau shi ne shugaban kungiyar izala, ko ya halarci taron da ya kira to lallai wannan ba ya son hadin kan kungiyar izalah, lalle wannan ya zama mai raba kan Al'ummah, lalle wannan ya zama munafuki cikin Al'ummah, lalle wannan ya zama mai yi wa shugabancin izala tawaye!!!

Alhali kuwa a wurin dukkan masu hankali su din nan su ne suke cikin wadannan siffofi dumu-dumu, ba wai wadanda suka bi ka'ida suka ce Sheik Abdullahi Bala Lau shi shugaban kungiyar izala ba.

2. Sun zargi Shugaban kungiyar izalah na kasa Sheik Abdullahi Bala Lau tare wadanda suka yadda da shugabancinsa da cewa su masu saba alkawari ne!!
Alhali kuwa su din nan su ne masu halin saba alkawari cikin kusan dukkan wani ittifaki da ya gudana tsakaninmu da su, abubuwan da suka saba alkawari a cikinsu suna da yawan gske, amma zan ambaci daya kawai daga cikinsu a matsayin misali:-

A zaman karshe da membobin kwamitin shuran nan mai mutum 24 suka yi a Kaduna a Masallacin Sultan Bello wanda shugaban kungiyar izala ya ke ciki, kuma shi ma shugaban majalisar malamai na kungiyar izala yake ciki an yi matsayar cewa: kada wani ya sake kiran shugaban Kungiyar izala da sunan "shugaban gudanarwa". Sannan lokacin da aka je wa'azin kasa a garin Lafiya, shi shugaban kungiyar izala na kasa Sheik Abdullahi Bala Lau, da kuma shi shugaban majalisar malamai ta kungiyar izala ko wanne daga cikinsu ya kara tabbatar da wannan matsaya da aka cimma a Kaduna a kan mimbarin kungiyar izala. 

To amma abin mamaki sai ga shi a kan mimbarin wa'azi a garin Kano shi shugaban majalisar malamai M. Sani Yahya ya warware wannan yerjejeniya, ya yi watsi da wannan alkawari, da wannan matsaya da aka cimma a garin Kaduna cikin Masallacin Sultan Bello, babu tsoron Allah babu kunyar jama'a ya fito fili ya kira shugaban kungiyar kungiyar izala da sunan shugaban gudanarwa!!!

Mun yi wannan rubutun ne saboda yakar karya da bazu a cikin mutane, da kuma tabbatar da gaskiya, domin kowa ya kasance a bisa basira cikin lamarinsa. Wannan kuwa dama shi ne aikin Kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunnah.

Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da ya hada kan al'ummarmu a kan gaskiya, ya kuma tsare mu daga sharrin masu yaudarar jama'a, ya kuma tabbatar da dugaduganmu a kan riko da sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah cikin dukkan aqiidarmu, da dukkan ibadarmu, da dukkan mu'amalarmu. Amee

No comments: