Sunday, 20 October 2013


ZAGI DA IGILIN YAN BIDI,A KADA YA BAKA TSORO WAJEN RIQO DA SUNNAH INAI MAKA ALBISHIR DA CEWA: BABU WATA FUSKA DAKE RAYE AYAU ABAYAN QASA DA TAKE KAMA DATA SAHABBAI SE FUSKOKIN AHLUSSUNNAH SUNE WADANDA FUSKARSU TAKE CIKE DA HASKEN QIYAMULLAILI MAGANGANUNSU DA AYYUKANSU SUNA TAFIYAR DASUNE AKAN DORON KOYARWAR FIYAYYEN HALITTA MANZO SAW.

SHIN BA ANNABI SAW BANE YACE: DUK ME RIQO DA SUNNAH TA A LOKACINDA AL,UMMATA ZASU LALACE KAMAR ME RIQONE DA GARWASHIN WUTA??

SHIN MANZO SAW BE BAR MANA WASIYYABA CEWA DUK WANDA YAI TSAWON KWANA ZEGA SABANI ME YAWA AMMA NAI MUKU WASIYYA DA KU LAZIMCI KARANTARWATA DA KARANTARWAR KHALIFOFINA SHIRYAYYU (ABUBAKAR DA UMAR DA USMAN DA ALI) ???????

ME ZE DAMEKA AKAN ANWA GEMUNKA DA WANDONKA IZGILANCI BAYAN KASAN ANNABI SAW NE YA AIKATA KUMA YACE KU AIKATA??

ME ZE DAMEKA KAN YAN BIDI,A SUNCE DUK DA ANNABI SAW DA ZURIYARSA DA SAHABBANSA BASUYI MAULIDIBA SU SE SUNYI, ME ZE DAMEKA ME ZE BAQANTA MAKA RAI BAYAN KASAN ANNABI SAW YACE DUKKAN BIDI,A BATACE SANNAN YACE KOWANE BATA ME BILLEWA NE DA MESHI ZUWA GIDAN WUTA??????

TARE DA CEWA ALLAH YANA CEWA:

أفمن حق عليه كلمة العذاب أفأنت تنقذ من فب النار

SHIN WANDA KALMAR AZABA TA TABBATA AKANSA SHIN KAI ZAKA IYA TERATAR DA WANDA(ALLAH YA QADDARA RAUWARSA) A WUTA???

DAN HAKA KAIDAI KAITA AIKI DA SUNNAH KANA NISANTAR BIDI,A KUMA KA KOYAR DASU DA SANNU ZA,A WAYI GARI SUMA SUNA KOYAR DA WASU

Zanga-zangar talakawa saboda neman tabbataccen wani hakki nasu, ko saboda neman tunkude wani zalunci a kansu daga shugabanni masu mulkarsu, wani abu ne da ake gani yana faruwa daga lokaci zuwa lokaci cikin al'ummai daban-daban.

A wannan makala tamu muna so ne mu dubi mahangar Musulunci cikin mas'alar, muna kuma rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya yi mana jagora ckin abin da za mu fada, Ya kuma amfanar da Al'ummarmu da ita.

Farko dai ya kamata a san cewa babu sabani a tsakanin Malumanmu cewa: zanga-zangar hayaniya da kone-kone, da kuma wacce a ka gina saboda tabbatar da zalunci, irin wannan nau'i na zanga-zanga ba ya halatta.
*****************************
Amma zanga-zangar lumana wacce aka tsara saboda neman wani tabbataccen hakki, ko neman tunkude wani tabbataccen zalunci daga shugabanni, ko daga wasunsu, lalle malamanmu na Musulunci a wannan zamani sun kasu kashi biyu game da hukuncinta.

Kashi na farko suka ce: Zanga-zangar talakawa ba ta halatta saboda abubuwa uku:-
Na farko: Akwai kamanta kai da kafurai cikin yin ta, domin kafurai ne aka san cewa suna daukar yin zanga-zanga a matsayin wata hanya ta neman kauda wani munkari, duk kuwa abin da kafurai za su kebanta da shi, to ba halal ba ne Musulmi su rika yin shi.
Na biyu: zanga-zanga na daga cikin fararrun al'amura a cikin Addini, duk kuwa abin da yake fararren lamari cikin addini ta ba daidai ba ne a yi shi.
Na uku: dogara da Qa'idar "sadduz Zari'ah" domin sau da dama yin zanga-zanga saboda neman kauda wani munkari ya kan sabbaba fadawa cikin munkari mafi girma, wannan zai wajabta nisantarsa tun farkon fari.
*****************************
Kashi na biyu kuwa suka ce: Zanga-zangar lumana halal ce "babu wani laifi a yi amfani da ita saboda neman kauda wani munkari. Sun kafa hujja kamar haka:-
Na farko: Suka ce: zanga-zangar lumana wani abu ne da Salaf suka yi amfani da shi domin kauda munkari. Imam Abubakar Dan Khallal ya ce cikin littafinsa mai suna Al-Amru Bil Ma'arufi Wan Nahyu anil Munkari shafi na 50:-
((عن محمد بن أبي حرب قال: سالت أبا عبد الله عن الرجل يسمع المنكر في دار بعض جيرانه. قال: يأمره. قلت: فان لم يقبل؟ قال: تجمع عليه الجيران وتهول عليه)). انتهى.
Ma'ana ((Daga Muhammad Dan Abi Harb, ya ce: na tambayi Abu Abdullahi (watau Imam Ahmad Dan Hanbal) game da mutumin da yake jin munkari cikin gidan sashin makwabtansa. Sai ya ce: Zai umurce shi (da ya bari). Sai na ce: To in bai karba ba fa? Sai ya ce: sai a tara masa makwabta a tsoratar da shi)). Intaha. Sannan har yanzu Khallal ya riwaito cikin shafi na 50-51 ya ce:-
((عن جعفر بن محمد النسائي قال: سمعت أبا عبد الله سئل عن الرجل يمر بالقوم يغنون؟ قال: اذا ظهر له هم داخل. قلت: لكن يسمع الصوت يسمع في الطريق. قال: هذا ظهر عليه ان ينهاهم. ورأى ان ينكر الطبل يعني اذا سمع حسه. قيل: مررنا بقوم وقد اشرفوا من علية لهم وهم يغنون فجئنا الى صاحب الخبر فاخبرناه. فقال: لم تكلموا في الموضع الذي سمعتم؟ فقيل: لا. قال: كان يعجبني ان تكلموا لعل الناس كانوا يجتمعون وكانوا يشهرون)). انتهى.
Ma'ana: ((Daga Ja'afar Dan Muhammad An-Nasaaii ya ce: Na ji Abu Abdillah an tambaye shi game da mutumin da ya wuce wasu mutane suna wake-wake? Sai ya ce: idan ya bayyana gare shi cewa suna cikin gida. Sai na ce: sai dai ana jin sauti ana ji a cikin hanya. Ya ce: wannan ya zama wajibi a kan shi ya hana su. Kuma ina ganin ya yi inkarin babbar ganga, watau idan suka ji motsin shi. Sai aka ce: mun wuce wasu mutane suna kan wani bene nasu suna ta wake-wake, sai muka je wa jami'in hukuma wanda ake kai masa labarai aka ba shi labari. Sai ya ce: ba su yi magana cikin maudhu'in da kuka ji ba? Sai aka ce: a'a. Sai ya ce: ya kasance yana kayatar da ni su yi magana, watakila mutane za su kasance suna taruwa suna yayata lamarinsu)). Intaha.

Kun gani a cikin wadannan atharai biyu Imam Ahmad ya yi fatawar mutane su taru saboda inkarin munkari saboda a tsoratar da Mai munkarin da kuma yayata lamarinsa.
Sannan Abul Faraj Abdurrahman Ibnul Jauzii wanda ya rasu shekarar hijira 527 ya ce cikin littafin tarihinsa mai suna: Al-Mutazim Fi Tarikhil Muluuki Wal Umam 8/240:-
((واجتمع في يوم الخميس رابع عشر المحرم خلق كثير من الحربية والنصرية وشارع دار الرقيق وباب البصرة والقلائين ونهر طابق بعد ان أغلقوا دكاكينهم وقصدوا دار الخلافة وبين ايديهم الدعاة والقراء وهم يلعنون اهل الكرخ، وازدحموا على باب الغربة وتكلموا من غير تحفظ في القول، فراسلهم الخليفة ببعض الخدم: اننا قد انكرنا ما انكرتم، وتقدمنا بان لا يقع معاودة، ونحن نغفل في هذا ما لا يقع به المراد. فانصرفوا وقبض على ابن الفاخر العلوي في آخرين، ووكل بهم في الديوان. وهرب صاحب الشرطة؛ لانه كان أجاز لأهل الكرخ ما فعلوا)). انتهى.
Ma'ana: ((Mutane da yawa suka hadu ranar alhamis sha hudu ga Muharram, daga Harbiyyah, da Nasriyyah, da Shari'u Darir Raqiq, da Babul Basrah, da Qalaawiin, da Nahru Tabiq bayan sun kukkulle kantuna sun nufi Fadar Khalifah, a gaba gare su akwai Masu wa'azi da Makaranta Alkur'ani suna ta tsine wa jama'ar Karkh, suka yi cinkoso a kofar gurbah, suka yi ta magana ba tare da wani rufa-rufa ba. Khalifah sai ya aiko wasu yaran Sarki zuwa gare su (da sakon): Lalle mu mun yi inkarin abin da kuka yi inkarin shi, kuma muna gabatar da (akawalin cewa) haka ba zai sake faruwa ba, kuma mu za mu tushe aukuwar dukkan abin da ba shi ne manufa ba. Sai suka watse, kuma aka kama Ibnul Faakhir Ba'alawe da ma wasu daban. Kuma aka jingina su cikin Diwani, sannan shugaban yan sanda ya gudu, saboda shi ne ya ba wa jama'ar Karkh izinin yin abin da suka yi)). Intaha.

Wannan zanga-zangar ta faru ne a shekarar hijira 458 watau yau shekaru 975 ke nan da suka wuce. Idan ka dubi maganar Imam Ahmad sannan ka dubi wannan kissa za ka fahimci cewa zanga-zanga saboda inkarin wani munkari lamari mai asali a cikin Musulunci, ba yi da alaka da abin da za a kira: Kwaikwayon kafirai.

Hujjarsu ta biyu suka ce: da za a kaddara, zanga-zanga wata sabuwar wasilar inkarin munkari ne ba wai tsohuwa ba ce a cikin Musulunci, to da ma hakan ba zai maida ita haramun ba, ko kuwa hakan ba zai sanya ta cikin jerin bidi'o'i a cikin Addini ba, saboda su Wasaa'il matukar dai ba su kasance haramun ba ne saboda zatinsu, ko kuwa matukar dai ba su kasance wani shi'ari ba ne kebabbe ga kafurai to babu wani laifi Musulmi su fa'idantu da su a cikin Maqaasidush Shari'ah, kamar yadda dai Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah yake cewa cikin Majmu'ul Fatawa 30/206 watau kamar fa'idantuwa da kayayyakin gini, da saka, da sauran sana'o'i. Kuma a wannan zamani namu sai mu ce kamar su lasfikar da za a kira salla da ita saboda Kara sauti. Kai kamar rike tasbaha saboda kidayar lafuzan zikiri, kun san cewa babban Shaikhinmu Sheik Ibnu Uthaimiin yana ganin halaccin amfani da shi, kamar yadda ya zo cikin littafin: Jalasaatu Wa Fataawa Ibni Uthaimeen 8/32 saboda ita tasbaha tana daga cikin babi ne na Wasaa'il.

Muna fata Allah Ya nuna mana gaskiya gaskiya ce Ya ba mu ikon bin ta, Ya kuma nuna mana karya karya ce Ya ba mu ikon guje mata.
A2, KADA KAYI MAMAKIN GANIN KANKA CIKIN WUTA RANAR LAHIRA MATUƘAR KAƘI KIYAYE SALLOLI DOMIN ALLAH, acikin tambayoyi da ake yiwa ƴan'wuta ranar alƙiyama akwai bada amsa danganeda rashin sallah. Allah yacce ماسلككم في سقر، قالو لم نك من المصلين، ولم نك نطعم المسكين، وكنانخوض مع الخائضين، وكنانكذب بيوم الدين، حتى أتانااليقين. Allahu swa yacce me ya sanyaku acikin wutar saqara? Sai sukace bamu zamo daga cikin masu sallah bane, kuma bamu zamo muna ciyarwa ga miskinai ba, kuma mun kasance muna kutsawa daga cikin masu kutsaw, kuma mun kasance muna ƙaryatawa ga ranar sakamako, har mutuwa taxo muna, Allah kayiab iko kiyaye salloli cikin lkc.
A2, a COMPENSATORY RITUAL are REQUIRED MAMAKIN KAYI GANIN KANKA CIKIN WUTA RANAR LAHIRA MATUƘAR KAƘI KIYAYE SALLOLI DOMIN acikin tambayoyi God, the da ake yiwa ranar ƴan'wuta alƙiyama bada danganeda amsa akwai rashin sallah. God yacce ماسلككم في سقر ، قالو نك من المصلين لم ولم نك ، نطعم المسكين ، وكنانخوض الخائضين ، وكنانكذب مع بيوم الدين أتانااليقين حتى ،. Allahu swa yacce ya me acikin sanyaku wutar saqara? Sai cikin sukace daga Wednesday zamo bamu masu sallah bane, kuma bamu zamo muna ciyarwa ga ba miskinai, kuma kasance mun muna kutsawa cikin kutsaw daga Wednesday masu, kuma mun kasance muna ƙaryatawa ga ranar sakamako, har mutuwa taxo muna, God kayiab cikin salloli kiyaye iko lk