Zanga-zangar
 talakawa saboda neman tabbataccen wani hakki nasu, ko saboda neman 
tunkude wani zalunci a kansu daga shugabanni masu mulkarsu, wani abu ne 
da ake gani yana faruwa daga lokaci zuwa lokaci cikin al'ummai 
daban-daban. 
 
 A wannan makala tamu muna so ne mu dubi mahangar 
Musulunci cikin mas'alar, muna kuma rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya 
yi mana jagora ckin abin da za mu fada, Ya kuma amfanar da Al'ummarmu da
 ita.
 
 Farko dai ya kamata a san cewa babu sabani a tsakanin 
Malumanmu cewa: zanga-zangar hayaniya da kone-kone, da kuma wacce a ka 
gina saboda tabbatar da zalunci, irin wannan nau'i na zanga-zanga ba ya 
halatta.
 *****************************
 Amma zanga-zangar lumana 
wacce aka tsara saboda neman wani tabbataccen hakki, ko neman tunkude 
wani tabbataccen zalunci daga shugabanni, ko daga wasunsu, lalle 
malamanmu na Musulunci a wannan zamani sun kasu kashi biyu game da 
hukuncinta.
 
 Kashi na farko suka ce: Zanga-zangar talakawa ba ta halatta saboda abubuwa uku:-
 Na farko: Akwai kamanta kai da kafurai cikin yin ta, domin kafurai ne 
aka san cewa suna daukar yin zanga-zanga a matsayin wata hanya ta neman 
kauda wani munkari, duk kuwa abin da kafurai za su kebanta da shi, to ba
 halal ba ne Musulmi su rika yin shi.
 Na biyu: zanga-zanga na daga 
cikin fararrun al'amura a cikin Addini, duk kuwa abin da yake fararren 
lamari cikin addini ta ba daidai ba ne a yi shi.
 Na uku: dogara da 
Qa'idar "sadduz Zari'ah" domin sau da dama yin zanga-zanga saboda neman 
kauda wani munkari ya kan sabbaba fadawa cikin munkari mafi girma, 
wannan zai wajabta nisantarsa tun farkon fari.
 *****************************
 Kashi na biyu kuwa suka ce: Zanga-zangar lumana halal ce "babu wani 
laifi a yi amfani da ita saboda neman kauda wani munkari. Sun kafa hujja
 kamar haka:-
 Na farko: Suka ce: zanga-zangar lumana wani abu ne da 
Salaf suka yi amfani da shi domin kauda munkari. Imam Abubakar Dan 
Khallal ya ce cikin littafinsa mai suna Al-Amru Bil Ma'arufi Wan Nahyu 
anil Munkari shafi na 50:-
 ((عن محمد بن أبي حرب قال: سالت أبا عبد 
الله عن الرجل يسمع المنكر في دار بعض جيرانه. قال: يأمره. قلت: فان لم 
يقبل؟ قال: تجمع عليه الجيران وتهول عليه)). انتهى.
 Ma'ana ((Daga 
Muhammad Dan Abi Harb, ya ce: na tambayi Abu Abdullahi (watau Imam Ahmad
 Dan Hanbal) game da mutumin da yake jin munkari cikin gidan sashin 
makwabtansa. Sai ya ce: Zai umurce shi (da ya bari). Sai na ce: To in 
bai karba ba fa? Sai ya ce: sai a tara masa makwabta a tsoratar da 
shi)). Intaha. Sannan har yanzu Khallal ya riwaito cikin shafi na 50-51 
ya ce:-
 ((عن جعفر بن محمد النسائي قال: سمعت أبا عبد الله سئل عن 
الرجل يمر بالقوم يغنون؟ قال: اذا ظهر له هم داخل. قلت: لكن يسمع الصوت 
يسمع في الطريق. قال: هذا ظهر عليه ان ينهاهم. ورأى ان ينكر الطبل يعني اذا
 سمع حسه. قيل: مررنا بقوم وقد اشرفوا من علية لهم وهم يغنون فجئنا الى 
صاحب الخبر فاخبرناه. فقال: لم تكلموا في الموضع الذي سمعتم؟ فقيل: لا. 
قال: كان يعجبني ان تكلموا لعل الناس كانوا يجتمعون وكانوا يشهرون)). 
انتهى.
 Ma'ana: ((Daga Ja'afar Dan Muhammad An-Nasaaii ya ce: Na ji 
Abu Abdillah an tambaye shi game da mutumin da ya wuce wasu mutane suna 
wake-wake? Sai ya ce: idan ya bayyana gare shi cewa suna cikin gida. Sai
 na ce: sai dai ana jin sauti ana ji a cikin hanya. Ya ce: wannan ya 
zama wajibi a kan shi ya hana su. Kuma ina ganin ya yi inkarin babbar 
ganga, watau idan suka ji motsin shi. Sai aka ce: mun wuce wasu mutane 
suna kan wani bene nasu suna ta wake-wake, sai muka je wa jami'in hukuma
 wanda ake kai masa labarai aka ba shi labari. Sai ya ce: ba su yi 
magana cikin maudhu'in da kuka ji ba? Sai aka ce: a'a. Sai ya ce: ya 
kasance yana kayatar da ni su yi magana, watakila mutane za su kasance 
suna taruwa suna yayata lamarinsu)). Intaha. 
 
 Kun gani a cikin 
wadannan atharai biyu Imam Ahmad ya yi fatawar mutane su taru saboda 
inkarin munkari saboda a tsoratar da Mai munkarin da kuma yayata 
lamarinsa.
 Sannan Abul Faraj Abdurrahman Ibnul Jauzii wanda ya rasu 
shekarar hijira 527 ya ce cikin littafin tarihinsa mai suna: Al-Mutazim 
Fi Tarikhil Muluuki Wal Umam 8/240:-
 ((واجتمع في يوم الخميس رابع عشر
 المحرم خلق كثير من الحربية والنصرية وشارع دار الرقيق وباب البصرة 
والقلائين ونهر طابق بعد ان أغلقوا دكاكينهم وقصدوا دار الخلافة وبين 
ايديهم الدعاة والقراء وهم يلعنون اهل الكرخ، وازدحموا على باب الغربة 
وتكلموا من غير تحفظ في القول، فراسلهم الخليفة ببعض الخدم: اننا قد انكرنا
 ما انكرتم، وتقدمنا بان لا يقع معاودة، ونحن نغفل في هذا ما لا يقع به 
المراد. فانصرفوا وقبض على ابن الفاخر العلوي في آخرين، ووكل بهم في 
الديوان. وهرب صاحب الشرطة؛ لانه كان أجاز لأهل الكرخ ما فعلوا)). انتهى.
 Ma'ana: ((Mutane da yawa suka hadu ranar alhamis sha hudu ga Muharram, 
daga Harbiyyah, da Nasriyyah, da Shari'u Darir Raqiq, da Babul Basrah, 
da Qalaawiin, da Nahru Tabiq bayan sun kukkulle kantuna sun nufi Fadar 
Khalifah, a gaba gare su akwai Masu wa'azi da Makaranta Alkur'ani suna 
ta tsine wa jama'ar Karkh, suka yi cinkoso a kofar gurbah, suka yi ta 
magana ba tare da wani rufa-rufa ba. Khalifah sai ya aiko wasu yaran 
Sarki zuwa gare su (da sakon): Lalle mu mun yi inkarin abin da kuka yi 
inkarin shi, kuma muna gabatar da (akawalin cewa) haka ba zai sake 
faruwa ba, kuma mu za mu tushe aukuwar dukkan abin da ba shi ne manufa 
ba. Sai suka watse, kuma aka kama Ibnul Faakhir Ba'alawe da ma wasu 
daban. Kuma aka jingina su cikin Diwani, sannan shugaban yan sanda ya 
gudu, saboda shi ne ya ba wa jama'ar Karkh izinin yin abin da suka yi)).
 Intaha.
 
  Wannan zanga-zangar ta faru ne a shekarar hijira 458 
watau yau shekaru 975 ke nan da suka wuce. Idan ka dubi maganar Imam 
Ahmad sannan ka dubi wannan kissa za ka fahimci cewa zanga-zanga saboda 
inkarin wani munkari lamari mai asali a cikin Musulunci, ba yi da alaka 
da abin da za a kira: Kwaikwayon kafirai.
 
 Hujjarsu ta biyu suka
 ce: da za a kaddara, zanga-zanga wata sabuwar wasilar inkarin munkari 
ne ba wai tsohuwa ba ce a cikin Musulunci, to da ma hakan ba zai maida 
ita haramun ba, ko kuwa hakan ba zai sanya ta cikin jerin bidi'o'i a 
cikin Addini ba, saboda su Wasaa'il matukar dai ba su kasance haramun ba
 ne saboda zatinsu, ko kuwa matukar dai ba su kasance wani shi'ari ba ne
 kebabbe ga kafurai to babu wani laifi Musulmi su fa'idantu da su a 
cikin Maqaasidush Shari'ah, kamar yadda dai Shaikhul Islam Ibnu 
Taimiyyah yake cewa cikin Majmu'ul Fatawa 30/206 watau kamar fa'idantuwa
 da kayayyakin gini, da saka, da sauran sana'o'i. Kuma a wannan zamani 
namu sai mu ce kamar su lasfikar da za a kira salla da ita saboda Kara 
sauti. Kai kamar rike tasbaha saboda kidayar lafuzan zikiri, kun san 
cewa babban Shaikhinmu Sheik Ibnu Uthaimiin yana ganin halaccin amfani 
da shi, kamar yadda ya zo cikin littafin: Jalasaatu Wa Fataawa Ibni 
Uthaimeen 8/32 saboda ita tasbaha tana daga cikin babi ne na Wasaa'il. 
 
 Muna fata Allah Ya nuna mana gaskiya gaskiya ce Ya ba mu ikon bin ta, Ya kuma nuna mana karya karya ce Ya ba mu ikon guje mata.
 
 
 
          
      
 
  
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
No comments:
Post a Comment