Tuesday, 17 September 2013

DASUNAN ALLAH MAIRAHAMA MAIJIN KAI
HADISAN DA ‘YAN TAWAYE SUKE KARYATAWA KAI
TSAYE.
Kamar yadda akayimin tambaya kuma aka nemi bayani daga wurina , kuma hadissan da suka karyata suna da yawa ainun , kuma agaskiya hukuncin duk wanda yakaryata Annbi (saw) kafirine kaitsaye, mai karyata Annabi (saw) ba’a binsa sallah kuma ba’a cin yankansa, sai in ya tuba yagyara ,saboda haka ga kadan daga hadisan da suka karyata.
ADDU’O’I
Acikin sunnanittirmizi hadisi na dubu uku da dari uku da tamanin 3380 manzon Allah (saw) yace wadansu mutane basu zauna amajalisin da basu ambaci Allah cikin saba kuma basuyi salati ga Annabinsuba face wannan majalisin yazama hasara garesu ranar qiyama , in Allah yaso ya azabtardasu in Allah yaso saiya yafe musu , tirmizin ya inganta hadisin , haka kuma Albanima ya ingantashi.Saboda haka sai muyita Addu’a aduk inda aka taru da salati wa ma’aiki (saw)
Saboda haka yazo acikin fatahulbari hadisi na 5923 Annabi tsira da amincin Allah sutabbata agareshi yace: wadansu mutane bazasu haduba (wato kowanne irin haduwa na musulunci) sashinsu yana Addu’a sahinsu yana cewa Amin face Allah ya karba musu , haka dabarani hadisi na 206 . haka faddulwa’aa’I hadisi na 23. haka kuma hadisin Abubakar siddiq alokacin daya aiki sa’idu bn Amir ya umarceshi yaje harsaiya samu zaid bn Abu safiyan, sai Abubakar yace bayin Allah Kuroki Allah ya tsare sahibinku da ‘yan uwanku dake tare dashi , yakubutar dasu, sai ku daga hannayenku gaba daya Allah yayi muku rahama , saisuka daga hannayensu gaba dayansu su fiye da mutum hamsin 50 sai Aliyu bn Abi dhalib yace : damasu musulmi masu yawa bazasu daga hannayensu suna rokon Allah wani Abuba face yakarba musu ,matukar basabon Allah suke nufiba ko yanke zumunta . faddul wa’aai hadisi na 13 Haka kuma Ankarbo daga salman yace : manzon Allah (saw) yace wasu jama’a mutane bazasu daga hannayensuba zuwa ga Allah Azzawajallasuna rokonsa wani abuba face yakasance hakki ga Allah yasanya abinda suka nema acikin hannayensu” hadisi sahihi. Faddul wa’aa’I shafina 54
Wadannan hadisai dawasunsu sunyi nuni akan addu’ar jam’I duk inda musulmi suka hadu.
kuma bisa ga maimaita addu’a wa mutanen kirki bizaharil gaibi , kadubi suratul hasher ayata 10 inda Allah kecewa (kuma wadanda sukazo abayansu suna cewa uban gijinmu kagafartamana kuma da ‘yan’uwanmu wadanda suka rigamu imani kuma karka sanya wata gilli acikin zukatanmu gameda wadanda suka rigamu imani ) kuma da makamantan wannan ayar kuma asura tul Muhammad Ayata 19 da kuma Ibrahim Ayata 41. Duka sun bada ma’ana guda gameda addu’ar .saboda haka ,
sai manzon Allah (saw) yafassara ayar da cewa “ babu wani bawa musulmi da zaiyi addu’a ga dan’uwanshi alhali dan uwannashi bayanan face mala’ika yace kaima anbaka duk irin abinda karokamasa” sahihu muslim hadisi na 7103. Wato mana’a “bizaharil gaibi” yazamo wanda akewa addu’ar bayanan awajenda ake addu’ar ko yanada rai ko bayi da rai.
Kuma kadubi hadisin ka’ab bn malik wanda maruzi yaruwaito daga ka’ab bn malik yaddar Allah yatabbata agareshi , dansa Abdurrahman yana cewa nine jagoran babana lokacin da yamakance , kuma duk lokacinda nafita dashi zuwa juma’a idan yaji kiran sallah yana Addu’a da neman gafara wa sa’ad bn zurrara sai yazamana kullum yaji kiran sallar juma’a saiyayi Addu’a wa sa’ad bn zurrara , sai yaron yace ya babana meyasa kaketa maimaita addu’a wa sa’ad bn zurrara ko wace juma’a? sai yace ya dana ai shi sa’ad bn zurrara shine farkon limaminda yafara yimana sallar juma’a Amadina a’unguwar baniibayada, kafin Annabi (saw) ya iso daga makkah , sai yaron yace alokacin kunawane? Sai ka’ab bn malik yace alokacinmu hansin 50 ne. wannan aiki na ka’ab bn malik yana tabbatarda cewa zamuyita maimaita addu’a kenan ga magabata mutanen kirki.
Kuma hadisan ingantattune, sabida haka aiki dasu shine bin sunnar ma’aiki (saw) domin sahabi komai yayi ya koyane daga Annabi (saw)saboda haka ba’a tuhumarsu da saba mashi.
SHAFA HANNAYE AFUSKA
Tirmizi hadisina 3386) An tabbatar dashi kamar haka acikin “ faddul wa’a’I 54”
An karbo daga salim dan Abdullahi bin umar daga Abdullahi bin umar daga umar dan khaddabi , yaddar Allah ta tabbata agaresu , yace : manzon Allah (saw) yakasance idan yadaga hannayensa cikin Addu’a baya saukesu saiya shafi fuskarsa dasu . hadisin sahihine . faddul wa’a’I .shafi na 54
to aikaga bazamu barsuba muje muna aiki da kame kame marar daliliba dan son zuciya ,muje muna cewa malam wane yace wane yace, Alhali kuwa ga ingan tattun hadisai dayawa daga manzon Allah (saw) akan wannan mas’ala saboda haka mumanzon Allah (saw) da sahabbansa (Ra) mukebi akowace mas’ala. Kuma Allah ya taimakemu akan haka Amin .
kuma duk wanda ya karyata hadisan Annabi (saw) ingantattu irin wadannan da gangan harma da ayar Al’qur’ani karara bisa ga maimaita addu’a ga bayin Allah agaskiya yakafurta . kuma ina kira ga ‘yan uwa Ahlussunna sulura akwai wadanda suke tahowa da sunan musulunci Alhali kuwa ba musulmi bane suna zuwane don subata akidar musulmai, domin Annabi (saw) yace addu’a bargon ibadane, “wato kashin bayan addinine” kenan saikalura damaikokarin hanaka addu’a yaya ‘aqidarsa take?.
NADIN RAWANI
Nada rawani sunnane kamar yadda aka tambayi Abdullahi bin umar yafada. Umdatulqari sharhu sahihul bukhari hadisi na 5805 Ababin rawani mailamba na 15 .sunanuttirmizi hadisi na 1736 kuma asaki jela tabaya tsakanin kafadu kota gaba kamar yadda Annabi (saw) yake sakewa, kuma sahabbansa sukayi koyidahaka . akara duba .Fatahul bari 16/356
Sunanun nisa’I hadisi na 5343zuwa 5344 da 5345 da 5346
Sunani abi dauda hadisi na 4076 zuwana 4077kuma ga hadisin Rukana mainuna inda ma’aiki (saw) yake cewa banbanci tsakaninmu da mushirkai Rawani akan hula .sunani Abi dauda hadisi na 4078
Sunani ibni majah , hadisi na 3584 zuwa 3585 zuwa 3586 zuwa 3587 kuma cewa rawani al’adar larabane kawai ,!!wannan magana jahilcine don bahaka maruwaita hadissan suka fahimtaba ,a’a sukam sunfahimci rawani sunnane na ma’aiki (saw) kuma gashi mafiyan maruwaitan ba larabawa bane,haka dukkam malamai suka fahimci rawani sunnane na ma’aiki (saw) tabbatacce.
Wato dai abinda yakamata afahimta anan shine Rawanidai sunnane me karfi na Annabi Muhammad (saw) kamar yadda ya gudana acikin sahabbai da tabi’iyna da tabi’uttabi’iyna har zuwa kan sheikh usman dan fodiyo, idan kadubi ihya’ussunnah shafina 148. Shima danfodiyo fahimtarshi rawani sunnane mai karfi, wato yabi sahun ‘yan’uwansa malaman sunnah. Saboda haka duk mai zagin Rawani to yasani da kyau yana zagin Annabine da sahabbansa da tabi’iyna da tabi’uttabi’iyna, kuma ya bautawa son zuciyarsa , da hakan*
JIYARWA A CIKIN SALLAH
Hakiqa Bukhari yayi tarjama akan jiyarwa a cikin sallah da fadinsa “Babin wanda yajiyar da mutanekabbarorin liman Har yakai zuwa ga fadinsa,Abubakar ya kasance yana jiyar da mutane kabbara.Kuma wannan shine jamhurin maluma suka kafa hujja dashi akan jiyarwa acikin sallah(Fathul Bary 2\259).Daga jabir Allah ya yarda dashi yace “Manzon Allah(saw) yayi mana sallah,Abubakar yana bayansa,Idan Manzon Allah(saw)yayi kabbara sai Abubakar yayi kabbara domin ya jiyar damu”(Muslim Bisharhin Nawawi 2\345) .Imamu Nawawi yace wannan dalili ne akan daga sauti don a jiyar da mutane,kuma ya halatta ga mai koyi da liman ya bi wannan sauti na mai jiyarwa.Kuma wannan itace Mazhabarmu , kuma Mazhabar Jamhur.(Muslim Bisharhin Nawawi 2\355—356 ko Umdatul Qary 3\216 ko Tirmizi 1\378 koNailal Audar 2\269).
Ash-shaukani yace ya halatta ga mai koyi da liman bin sautin mai jiyarwa.Don haka sunnah ce ga mai bin liman ya jiyar da masu sallah kabbarar liman,domin Annabi(saw) ya sunnanta haka a Masallacin sa mai Alfarma.Kuma Sahabbai da Tabi`ai sunyi ta aiki da wannan sunnah har zuwa wannan lokaci namu,kuma a yanzu haka ana aikata sunnar jiyarwa a Masallacin Manzon Allah(saw) da yake Madinah mai Alfarma.kuma anyi ijima,I akan haka .to kaga duk malaman hadisi fahimtarsu kenan gameda wadannan hadissan,to kaga ta yaya za’abar sunnah adawo ana shauraron masu Magana da ka?!!

SADALU
Acikin musannaf na ibni Abi shaiba wanda ake kira “Al’ahadisu wal’asar” jizi’I na daya shafi na 342\343, Anruwaito sadalu daga Hasanul basari da ibrahimunnakha’I . Ashafina 395 anruwaito sadalu daga Abdullahi bn zubair sahabin Annabi (saw) da tabi’innan . ibni sirina da sa’eed bn musayyib da Abdullahi bn yazid da sa’eed bn jubair.dawasunsu,kuma dukkansu tabi’aine . kuma ga hadisin mu’azu bn jabal wanda Dabarani ya ruwaito acin mu’ajjamul kabir juzu’I na 2 shafi na 271 yana cewa : “ Annabi (saw) idan yakabbara sallah sake hannunsa yakeyi, awani lokaci kuma yakanyi qabalu.sa’annan gakuma aikin mutanen madina gabadaya,wanda suka gada daga sahabbai da tabi’iina da tabi’uttabi’iina , kuma wannan hujjane ga dukkan al’umma bisa ijima’in musulmi baki daya , kamar yadda ibni taimiyyah ya bayyana acikin majamu’ul fatawi juzu’I na 20 shafi na 294 ba’ataba samun wadanda suka karyataba, sai ‘yan tawayenmu ayanzu Allah ya shiryesu.
HADISIN SALLAMA DAYA
An samu daga Aishatu Matar Annabi (saw) tace “Annabi (saw) yana yin sallama guda daya ne acikin sallah” Sa`ad ibn Hisham Ibn Amir ya tafi zuwa ga Abdullahi Ibn abbas, ya bashi labari da wannan Magana ta Aishatu cewa Annabi (saw) ya kasance yana yin sallama guda ne acikin sallah.Sai Ibn Abbas yace tayi gaskiya(Muslim 2\170). A cikin ruwayar Tirmizi “Lallai Manzon Allah (saw) ya kasance yana yin sallama acikin sallah, guda daya tagabansa, sannan ya karkata kansa zuwa dama kadan”(Tirmizi 1\320). Daga salmata Ibn Ak,wa,i yace “ naga Manzon Allah (saw) yayi sallama guda daya”( Ibn Majah 1\297). Don haka, an samu ruwayoyi daga Annabi (saw) cewa yayi sallama daya acikin sallah gurare da dama, haka kuma an ruwaito daga khalifofi guda hudu, Abubakar da Umar da Usman da Aliyu da kuma sauran sahabbai kamar ibn Umar da Anas da ibn aby aufa, da Aishatu matar Annabi (saw)da Sa,ad ibn aby Waqqas da salmata bn akawa.u, da jama,a da yawa daga Tabi,ai bayan sahabban. Saboda haka ya tabbata kenan Manzon Allah yana fita daga Sallah da Sallama daya tak. Sigarta shine ASSALAMU ALAIKUM.(Fathul Bary Li ibn Rajab 6\59 ko Aujazul Masalik 2\145 ko Umdatul Qary 6\123—124)
Imamu Nawawi da Ibn Munzir sunce malamai sunhadu kancewa ba abinda ke wajaba ga mai sallah sai sallama daya tak( Muslim Bisharhin Nawawi 3\80 ko Sahihu Fiqhus Sunnah 1\127—326).*
Aby Wa`il da Yahya Ibn Wasib da Umar Ibn AbdulAzeez da Hassan da Ibn Sirin da Qasim Ibn Muhammad da Aishatu (RA) da Anas da Aby Aliya da Aby Raja`ida Ibn Aby Awfi da Ibn Umar da Sa`eed bn Jubair da Suwaidu da qaisu ibn Aby hazim, kuma dukkansu an ruwaito daga garesu da Isnadi mai kyau, kuma AbdurRazaq ya ambaci Sallama daya daga Zuhuri. Tirmizi yace “ Jama`a da yawa daga cikin Sahabban Annabi (saw) da tabi’ ai da wasunsu , sun zabi yin Sallama daya a sallar Farilla”(Nailal Audar 2\343 ). Imamu Ahmad ya ruwaito daga Abdullahi Ibn Aby Awfi cewa Annabi (saw) ya kasance yana fita a sallah ne da sallama daya tak(Musnad na Ahmad 1\236 ko irwa il galil *2\32—33). A cikin wata ruwaya Annabi (saw) ya kasance yana fita a sallah da Sallama Daya wajen Fuskarsa akan sharadin Muslim.Haka kuma Ibn Majah da Ahmad da Nisa`i da Tirmizi da Hakeem da Ibn Hibban da Darul-Quduni sun ruwaito da lafazin cewa “Manzon Allah(saw) ya kasance yana yin sallama daya ne wajen fuskarsa(Nailal Audar 2\341—342).Ahmad yace Salih yace Ibn Muhd yace lalle shi zuhair amintacce ne mai gaskiya.Haka kuma Abu Hatim da wasunsu duk sun tabbatar da haka, kuma hakika Bukhari ya ruwaito Wannan yana nuna amincinsa..Amma Bukhari ya takaita akan fadinsa yayi sallama ba tare da ambaton adadi ba, ya dai ce ATTASLIMU ba TASLIMATANI ba,don haka ATTASLIMU shine asalin kalmar wato MASDARI.MASDARI kuwa baya Magana akan adadi,wato kadan ko mai yawa,don haka sallama daya ta shiga.
An tambayi Malik akan sallama daya a cikin sallah,sai yace haka al`amarin yake.Shugabanni magabata sun kasance suna yin sallama daya ne,sallama biyu ta karfafu ne a lokacin Banu Hashim.Laisu yace mun riski shugabanni magabata da sauran mutane suna sallama daya ne a cikin sallah “ASSALAMU ALAIKUM”(Mukhtasar Iktilaful Ulama,u Lid Dahawi 1\590kuma Ahmad ya ruwaito cewa mutanen Madinah sun kasance suna sallama dayane a cikin sallah,kuma yace sallama biyu ta daukaku ne a cikin zamanin Bany Hashim ma`ana a cikin Mulkin Bany Abbas.Faruwar sallama biyu daga Kuhfa ne wato Iraqi.A wannan lokacin Mutanen Madinah sun kasance suna sallama daya ne tak kamar yadda suka gada daga Annabi,sai akai amfani dakarfin mulki wajen tilastasu ga sallama biyu .Laisu yace “masu Magana akan sallama biyunma, mafiya yawansu sun amince akan idan Mutum ya takaita akan sallama daya ta isar masa, kuma sallarsa ta inganta”.saboda haka Ibnul-Munzir ya ambaci ijima,I kan sallama daya. An ruwaito daga Ibn Umar yin sallama daya ga liman da wanda yake sallah shi kadai, da kuma yin sallama uku ga wanda yake Mamu kuma akwai wani tare da shi agefen hagu.Malik da Dara-Qudani sun tafi akan haka cikin abinda suka ruwaito cewa “Annabi(saw) ya umarcemu da muyi wa limamanmu sallama, kuma sashin mu yayiwa sashi sallama”(Dara Kuduni Hadisi na 1373).Hakika Annabi(saw)yayi sallama daya da Abubakar da Umar da Usman da Umar Ibn Abdul-Azeez. (mudawwana juzu,I nadaya shafi 196) kuma hadisin ingantaccene daga Aishatu(R.A).Hakeem yace hadisin ingantaccene akan sharadin Bukhari da Muslim.Hakama Sheikh Ahmad Shakir alokacinda yake tahaqiqi kan sunanuttirmizi, yace: sallama daya ingan taccene daga Annabi (saw)
nikuma inacewa wannan hadisin har ma Albani wanda yake ingantawa ko ya raunana yadda yaga dama, shima ya inganta wannan hadisin a cikin sahihu ibnu majah (750). Kuma hakika an ruwaito sallama biyu daga Abdullahi Ibn Mas`ud,kenan kaga ashe sallama biyumma akwai hadisi * tokaga Ashe sallama daya ko biyu duk wanda kayi sallarka ta inganta , saidai sallama daya tafi yawan hadissai ingantattu, shiyasa bukari bai ruwaici hadisin sallama biyuba .
ALQUNUTU
A alqunutu zamu gabatarda hadisin Anas inda yake cewa manzon Allah (saw) yakasance yana Alqunutu asallar Asuba harsaida yabar duniya baibariba . Ahmad ya ruwaitoshi juzu’ina 3 shafi na 162da ibni Abi shaiba juzi’ina 2 shafi na 312 musannaf na Abdurrazaq juzu’ina 3 shafi na 110 sharhul Asar na dahawi juzu’ina 1 shafi na 244 Assunnan darul quduni juzu’I na 2 shafi na Albaihaqi juzi’I na 2 shafi na 201 sharhissunnah na bagawi juzu’I 39 na 3 shafi 123\124 Al’I’itibar na hazimi shafina 188 zadal mi’ad na ibnul qayyim juzu’ina 1 shafi na 275 nasaburraya juzu’I na 2 shafina 132 Addinul kalis na imamussubuki juzu’I nz 4 shafi 29 majma’uzzawa’id juzu’I na 2 shafi na 162 Al majamu’u na imamunnawawi juzu’I na 3 shafi na 504 sahihul bukhari juzu’I na 2 shafi na 14 fathul bari juzu’I na 2 shafi na 621 sunanuttirmizi juzu’I na 1 shafi na 311 tuh

No comments: