DASUNAN ALLAH MAIRAHAMA MAIJIN KAI
HADISAN DA ‘YAN TAWAYE SUKE KARYATAWA KAI
TSAYE.
Kamar yadda akayimin tambaya kuma aka nemi bayani daga wurina , kuma
hadissan da suka karyata suna da yawa ainun , kuma agaskiya hukuncin duk
wanda yakaryata Annbi (saw) kafirine kaitsaye, mai karyata Annabi (saw)
ba’a binsa sallah kuma ba’a cin yankansa, sai in ya tuba yagyara
,saboda haka ga kadan daga hadisan da suka karyata.
ADDU’O’I
Acikin sunnanittirmizi hadisi na dubu uku da dari uku da tamanin 3380
manzon Allah (saw) yace wadansu mutane basu zauna amajalisin da basu
ambaci Allah cikin saba kuma basuyi salati ga Annabinsuba face wannan
majalisin yazama hasara garesu ranar qiyama , in Allah yaso ya
azabtardasu in Allah yaso saiya yafe musu , tirmizin ya inganta
hadisin , haka kuma Albanima ya ingantashi.Saboda haka sai muyita Addu’a
aduk inda aka taru da salati wa ma’aiki (saw)
Saboda haka yazo
acikin fatahulbari hadisi na 5923 Annabi tsira da amincin Allah
sutabbata agareshi yace: wadansu mutane bazasu haduba (wato kowanne
irin haduwa na musulunci) sashinsu yana Addu’a sahinsu yana cewa Amin
face Allah ya karba musu , haka dabarani hadisi na 206 . haka
faddulwa’aa’I hadisi na 23. haka kuma hadisin Abubakar siddiq alokacin
daya aiki sa’idu bn Amir ya umarceshi yaje harsaiya samu zaid bn Abu
safiyan, sai Abubakar yace bayin Allah Kuroki Allah ya tsare sahibinku
da ‘yan uwanku dake tare dashi , yakubutar dasu, sai ku daga
hannayenku gaba daya Allah yayi muku rahama , saisuka daga hannayensu
gaba dayansu su fiye da mutum hamsin 50 sai Aliyu bn Abi dhalib yace :
damasu musulmi masu yawa bazasu daga hannayensu suna rokon Allah wani
Abuba face yakarba musu ,matukar basabon Allah suke nufiba ko yanke
zumunta . faddul wa’aai hadisi na 13 Haka kuma Ankarbo daga salman yace
: manzon Allah (saw) yace wasu jama’a mutane bazasu daga hannayensuba
zuwa ga Allah Azzawajallasuna rokonsa wani abuba face yakasance hakki ga
Allah yasanya abinda suka nema acikin hannayensu” hadisi sahihi. Faddul
wa’aa’I shafina 54
Wadannan hadisai dawasunsu sunyi nuni akan addu’ar jam’I duk inda musulmi suka hadu.
kuma bisa ga maimaita addu’a wa mutanen kirki bizaharil gaibi , kadubi
suratul hasher ayata 10 inda Allah kecewa (kuma wadanda sukazo abayansu
suna cewa uban gijinmu kagafartamana kuma da ‘yan’uwanmu wadanda suka
rigamu imani kuma karka sanya wata gilli acikin zukatanmu gameda wadanda
suka rigamu imani ) kuma da makamantan wannan ayar kuma asura tul
Muhammad Ayata 19 da kuma Ibrahim Ayata 41. Duka sun bada ma’ana
guda gameda addu’ar .saboda haka ,
sai manzon Allah (saw)
yafassara ayar da cewa “ babu wani bawa musulmi da zaiyi addu’a ga
dan’uwanshi alhali dan uwannashi bayanan face mala’ika yace kaima
anbaka duk irin abinda karokamasa” sahihu muslim hadisi na 7103. Wato
mana’a “bizaharil gaibi” yazamo wanda akewa addu’ar bayanan awajenda ake
addu’ar ko yanada rai ko bayi da rai.
Kuma kadubi hadisin ka’ab bn
malik wanda maruzi yaruwaito daga ka’ab bn malik yaddar Allah yatabbata
agareshi , dansa Abdurrahman yana cewa nine jagoran babana lokacin da
yamakance , kuma duk lokacinda nafita dashi zuwa juma’a idan yaji kiran
sallah yana Addu’a da neman gafara wa sa’ad bn zurrara sai yazamana
kullum yaji kiran sallar juma’a saiyayi Addu’a wa sa’ad bn zurrara , sai
yaron yace ya babana meyasa kaketa maimaita addu’a wa sa’ad bn zurrara
ko wace juma’a? sai yace ya dana ai shi sa’ad bn zurrara shine farkon
limaminda yafara yimana sallar juma’a Amadina a’unguwar baniibayada,
kafin Annabi (saw) ya iso daga makkah , sai yaron yace alokacin
kunawane? Sai ka’ab bn malik yace alokacinmu hansin 50 ne. wannan aiki
na ka’ab bn malik yana tabbatarda cewa zamuyita maimaita addu’a kenan ga
magabata mutanen kirki.
Kuma hadisan ingantattune, sabida haka
aiki dasu shine bin sunnar ma’aiki (saw) domin sahabi komai yayi ya
koyane daga Annabi (saw)saboda haka ba’a tuhumarsu da saba mashi.
SHAFA HANNAYE AFUSKA
Tirmizi hadisina 3386) An tabbatar dashi kamar haka acikin “ faddul wa’a’I 54”
An karbo daga salim dan Abdullahi bin umar daga Abdullahi bin umar daga
umar dan khaddabi , yaddar Allah ta tabbata agaresu , yace : manzon
Allah (saw) yakasance idan yadaga hannayensa cikin Addu’a baya saukesu
saiya shafi fuskarsa dasu . hadisin sahihine . faddul wa’a’I .shafi na
54
to aikaga bazamu barsuba muje muna aiki da kame kame marar
daliliba dan son zuciya ,muje muna cewa malam wane yace wane yace,
Alhali kuwa ga ingan tattun hadisai dayawa daga manzon Allah (saw) akan
wannan mas’ala saboda haka mumanzon Allah (saw) da sahabbansa (Ra)
mukebi akowace mas’ala. Kuma Allah ya taimakemu akan haka Amin .
kuma duk wanda ya karyata hadisan Annabi (saw) ingantattu irin wadannan
da gangan harma da ayar Al’qur’ani karara bisa ga maimaita addu’a ga
bayin Allah agaskiya yakafurta . kuma ina kira ga ‘yan uwa Ahlussunna
sulura akwai wadanda suke tahowa da sunan musulunci Alhali kuwa ba
musulmi bane suna zuwane don subata akidar musulmai, domin Annabi (saw)
yace addu’a bargon ibadane, “wato kashin bayan addinine” kenan
saikalura damaikokarin hanaka addu’a yaya ‘aqidarsa take?.
NADIN RAWANI
Nada rawani sunnane kamar yadda aka tambayi Abdullahi bin umar yafada.
Umdatulqari sharhu sahihul bukhari hadisi na 5805 Ababin rawani mailamba
na 15 .sunanuttirmizi hadisi na 1736 kuma asaki jela tabaya tsakanin
kafadu kota gaba kamar yadda Annabi (saw) yake sakewa, kuma sahabbansa
sukayi koyidahaka . akara duba .Fatahul bari 16/356
Sunanun nisa’I hadisi na 5343zuwa 5344 da 5345 da 5346
Sunani abi dauda hadisi na 4076 zuwana 4077kuma ga hadisin Rukana
mainuna inda ma’aiki (saw) yake cewa banbanci tsakaninmu da mushirkai
Rawani akan hula .sunani Abi dauda hadisi na 4078
Sunani ibni majah ,
hadisi na 3584 zuwa 3585 zuwa 3586 zuwa 3587 kuma cewa rawani al’adar
larabane kawai ,!!wannan magana jahilcine don bahaka maruwaita hadissan
suka fahimtaba ,a’a sukam sunfahimci rawani sunnane na ma’aiki (saw)
kuma gashi mafiyan maruwaitan ba larabawa bane,haka dukkam malamai suka
fahimci rawani sunnane na ma’aiki (saw) tabbatacce.
Wato dai abinda
yakamata afahimta anan shine Rawanidai sunnane me karfi na Annabi
Muhammad (saw) kamar yadda ya gudana acikin sahabbai da tabi’iyna da
tabi’uttabi’iyna har zuwa kan sheikh usman dan fodiyo, idan kadubi
ihya’ussunnah shafina 148. Shima danfodiyo fahimtarshi rawani sunnane
mai karfi, wato yabi sahun ‘yan’uwansa malaman sunnah. Saboda haka duk
mai zagin Rawani to yasani da kyau yana zagin Annabine da sahabbansa da
tabi’iyna da tabi’uttabi’iyna, kuma ya bautawa son zuciyarsa , da hakan*
JIYARWA A CIKIN SALLAH
Hakiqa Bukhari yayi tarjama akan jiyarwa a cikin sallah da fadinsa
“Babin wanda yajiyar da mutanekabbarorin liman Har yakai zuwa ga
fadinsa,Abubakar ya kasance yana jiyar da mutane kabbara.Kuma wannan
shine jamhurin maluma suka kafa hujja dashi akan jiyarwa acikin
sallah(Fathul Bary 2\259).Daga jabir Allah ya yarda dashi yace “Manzon
Allah(saw) yayi mana sallah,Abubakar yana bayansa,Idan Manzon
Allah(saw)yayi kabbara sai Abubakar yayi kabbara domin ya jiyar
damu”(Muslim Bisharhin Nawawi 2\345) .Imamu Nawawi yace wannan dalili ne
akan daga sauti don a jiyar da mutane,kuma ya halatta ga mai koyi da
liman ya bi wannan sauti na mai jiyarwa.Kuma wannan itace Mazhabarmu ,
kuma Mazhabar Jamhur.(Muslim Bisharhin Nawawi 2\355—356 ko Umdatul Qary
3\216 ko Tirmizi 1\378 koNailal Audar 2\269).
Ash-shaukani yace ya
halatta ga mai koyi da liman bin sautin mai jiyarwa.Don haka sunnah ce
ga mai bin liman ya jiyar da masu sallah kabbarar liman,domin
Annabi(saw) ya sunnanta haka a Masallacin sa mai Alfarma.Kuma Sahabbai
da Tabi`ai sunyi ta aiki da wannan sunnah har zuwa wannan lokaci
namu,kuma a yanzu haka ana aikata sunnar jiyarwa a Masallacin Manzon
Allah(saw) da yake Madinah mai Alfarma.kuma anyi ijima,I akan haka .to
kaga duk malaman hadisi fahimtarsu kenan gameda wadannan hadissan,to
kaga ta yaya za’abar sunnah adawo ana shauraron masu Magana da ka?!!
SADALU
Acikin musannaf na ibni Abi shaiba wanda ake kira “Al’ahadisu wal’asar”
jizi’I na daya shafi na 342\343, Anruwaito sadalu daga Hasanul basari
da ibrahimunnakha’I . Ashafina 395 anruwaito sadalu daga Abdullahi bn
zubair sahabin Annabi (saw) da tabi’innan . ibni sirina da sa’eed bn
musayyib da Abdullahi bn yazid da sa’eed bn jubair.dawasunsu,kuma
dukkansu tabi’aine . kuma ga hadisin mu’azu bn jabal wanda Dabarani ya
ruwaito acin mu’ajjamul kabir juzu’I na 2 shafi na 271 yana cewa : “
Annabi (saw) idan yakabbara sallah sake hannunsa yakeyi, awani lokaci
kuma yakanyi qabalu.sa’annan gakuma aikin mutanen madina gabadaya,wanda
suka gada daga sahabbai da tabi’iina da tabi’uttabi’iina , kuma wannan
hujjane ga dukkan al’umma bisa ijima’in musulmi baki daya , kamar yadda
ibni taimiyyah ya bayyana acikin majamu’ul fatawi juzu’I na 20 shafi na
294 ba’ataba samun wadanda suka karyataba, sai ‘yan tawayenmu ayanzu
Allah ya shiryesu.
HADISIN SALLAMA DAYA
An samu daga Aishatu
Matar Annabi (saw) tace “Annabi (saw) yana yin sallama guda daya ne
acikin sallah” Sa`ad ibn Hisham Ibn Amir ya tafi zuwa ga Abdullahi Ibn
abbas, ya bashi labari da wannan Magana ta Aishatu cewa Annabi (saw) ya
kasance yana yin sallama guda ne acikin sallah.Sai Ibn Abbas yace tayi
gaskiya(Muslim 2\170). A cikin ruwayar Tirmizi “Lallai Manzon Allah
(saw) ya kasance yana yin sallama acikin sallah, guda daya tagabansa,
sannan ya karkata kansa zuwa dama kadan”(Tirmizi 1\320). Daga salmata
Ibn Ak,wa,i yace “ naga Manzon Allah (saw) yayi sallama guda daya”( Ibn
Majah 1\297). Don haka, an samu ruwayoyi daga Annabi (saw) cewa yayi
sallama daya acikin sallah gurare da dama, haka kuma an ruwaito daga
khalifofi guda hudu, Abubakar da Umar da Usman da Aliyu da kuma sauran
sahabbai kamar ibn Umar da Anas da ibn aby aufa, da Aishatu matar Annabi
(saw)da Sa,ad ibn aby Waqqas da salmata bn akawa.u, da jama,a da yawa
daga Tabi,ai bayan sahabban. Saboda haka ya tabbata kenan Manzon Allah
yana fita daga Sallah da Sallama daya tak. Sigarta shine ASSALAMU
ALAIKUM.(Fathul Bary Li ibn Rajab 6\59 ko Aujazul Masalik 2\145 ko
Umdatul Qary 6\123—124)
Imamu Nawawi da Ibn Munzir sunce malamai
sunhadu kancewa ba abinda ke wajaba ga mai sallah sai sallama daya tak(
Muslim Bisharhin Nawawi 3\80 ko Sahihu Fiqhus Sunnah 1\127—326).*
Aby Wa`il da Yahya Ibn Wasib da Umar Ibn AbdulAzeez da Hassan da Ibn
Sirin da Qasim Ibn Muhammad da Aishatu (RA) da Anas da Aby Aliya da Aby
Raja`ida Ibn Aby Awfi da Ibn Umar da Sa`eed bn Jubair da Suwaidu da
qaisu ibn Aby hazim, kuma dukkansu an ruwaito daga garesu da Isnadi mai
kyau, kuma AbdurRazaq ya ambaci Sallama daya daga Zuhuri. Tirmizi yace “
Jama`a da yawa daga cikin Sahabban Annabi (saw) da tabi’ ai da wasunsu ,
sun zabi yin Sallama daya a sallar Farilla”(Nailal Audar 2\343 ).
Imamu Ahmad ya ruwaito daga Abdullahi Ibn Aby Awfi cewa Annabi (saw) ya
kasance yana fita a sallah ne da sallama daya tak(Musnad na Ahmad 1\236
ko irwa il galil *2\32—33). A cikin wata ruwaya Annabi (saw) ya kasance
yana fita a sallah da Sallama Daya wajen Fuskarsa akan sharadin
Muslim.Haka kuma Ibn Majah da Ahmad da Nisa`i da Tirmizi da Hakeem da
Ibn Hibban da Darul-Quduni sun ruwaito da lafazin cewa “Manzon
Allah(saw) ya kasance yana yin sallama daya ne wajen fuskarsa(Nailal
Audar 2\341—342).Ahmad yace Salih yace Ibn Muhd yace lalle shi zuhair
amintacce ne mai gaskiya.Haka kuma Abu Hatim da wasunsu duk sun tabbatar
da haka, kuma hakika Bukhari ya ruwaito Wannan yana nuna
amincinsa..Amma Bukhari ya takaita akan fadinsa yayi sallama ba tare da
ambaton adadi ba, ya dai ce ATTASLIMU ba TASLIMATANI ba,don haka
ATTASLIMU shine asalin kalmar wato MASDARI.MASDARI kuwa baya Magana akan
adadi,wato kadan ko mai yawa,don haka sallama daya ta shiga.
An
tambayi Malik akan sallama daya a cikin sallah,sai yace haka al`amarin
yake.Shugabanni magabata sun kasance suna yin sallama daya ne,sallama
biyu ta karfafu ne a lokacin Banu Hashim.Laisu yace mun riski shugabanni
magabata da sauran mutane suna sallama daya ne a cikin sallah
“ASSALAMU ALAIKUM”(Mukhtasar Iktilaful Ulama,u Lid Dahawi 1\590kuma
Ahmad ya ruwaito cewa mutanen Madinah sun kasance suna sallama dayane a
cikin sallah,kuma yace sallama biyu ta daukaku ne a cikin zamanin Bany
Hashim ma`ana a cikin Mulkin Bany Abbas.Faruwar sallama biyu daga Kuhfa
ne wato Iraqi.A wannan lokacin Mutanen Madinah sun kasance suna sallama
daya ne tak kamar yadda suka gada daga Annabi,sai akai amfani dakarfin
mulki wajen tilastasu ga sallama biyu .Laisu yace “masu Magana akan
sallama biyunma, mafiya yawansu sun amince akan idan Mutum ya takaita
akan sallama daya ta isar masa, kuma sallarsa ta inganta”.saboda haka
Ibnul-Munzir ya ambaci ijima,I kan sallama daya. An ruwaito daga Ibn
Umar yin sallama daya ga liman da wanda yake sallah shi kadai, da kuma
yin sallama uku ga wanda yake Mamu kuma akwai wani tare da shi agefen
hagu.Malik da Dara-Qudani sun tafi akan haka cikin abinda suka ruwaito
cewa “Annabi(saw) ya umarcemu da muyi wa limamanmu sallama, kuma sashin
mu yayiwa sashi sallama”(Dara Kuduni Hadisi na 1373).Hakika
Annabi(saw)yayi sallama daya da Abubakar da Umar da Usman da Umar Ibn
Abdul-Azeez. (mudawwana juzu,I nadaya shafi 196) kuma hadisin
ingantaccene daga Aishatu(R.A).Hakeem yace hadisin ingantaccene akan
sharadin Bukhari da Muslim.Hakama Sheikh Ahmad Shakir alokacinda yake
tahaqiqi kan sunanuttirmizi, yace: sallama daya ingan taccene daga
Annabi (saw)
nikuma inacewa wannan hadisin har ma Albani wanda yake
ingantawa ko ya raunana yadda yaga dama, shima ya inganta wannan
hadisin a cikin sahihu ibnu majah (750). Kuma hakika an ruwaito sallama
biyu daga Abdullahi Ibn Mas`ud,kenan kaga ashe sallama biyumma akwai
hadisi * tokaga Ashe sallama daya ko biyu duk wanda kayi sallarka ta
inganta , saidai sallama daya tafi yawan hadissai ingantattu, shiyasa
bukari bai ruwaici hadisin sallama biyuba .
ALQUNUTU
A alqunutu
zamu gabatarda hadisin Anas inda yake cewa manzon Allah (saw) yakasance
yana Alqunutu asallar Asuba harsaida yabar duniya baibariba . Ahmad ya
ruwaitoshi juzu’ina 3 shafi na 162da ibni Abi shaiba juzi’ina 2 shafi na
312 musannaf na Abdurrazaq juzu’ina 3 shafi na 110 sharhul Asar na
dahawi juzu’ina 1 shafi na 244 Assunnan darul quduni juzu’I na 2 shafi
na Albaihaqi juzi’I na 2 shafi na 201 sharhissunnah na bagawi juzu’I 39
na 3 shafi 123\124 Al’I’itibar na hazimi shafina 188 zadal mi’ad na
ibnul qayyim juzu’ina 1 shafi na 275 nasaburraya juzu’I na 2 shafina
132 Addinul kalis na imamussubuki juzu’I nz 4 shafi 29 majma’uzzawa’id
juzu’I na 2 shafi na 162 Al majamu’u na imamunnawawi juzu’I na 3 shafi
na 504 sahihul bukhari juzu’I na 2 shafi na 14 fathul bari juzu’I na 2
shafi na 621 sunanuttirmizi juzu’I na 1 shafi na 311 tuh
No comments:
Post a Comment