TAMBAYA:- Mallam ya halarta don namiji ya kawowa mace sadaki ba'a daura
 musu aure ba, ya nemeta(da saduwa)? kuma shin ya halarta ta yadda 
dashi?
 
 (By Pretty Hidaya)
 
 AMSA:
 A'a bai halatta ba. Domin kuwa mace bata zama halal ga wani namiji sai ta hanyoyi guda biyu:
 
 1. Mallaka (wato bauta) 
 
 2. Aure.
 
 Shi kuwa biyan sadaki daya ne daga cikin sharudan aure. Amma ba shi bane auren. Domin ana iya daura auren ba tare dashi ba.
 (NIKAHUT TAFWEEDH).
 
 Don namiji ya biya sadakin mace batta zama matarsa har sai an daura 
musu aure. Malaman da suke bada fatawar halaccin saduwa da mace kafin 
daurin aure, suna bin son zuciyarsu ne kawai. Kuma suna bunkasa fasadi 
ne abayan Qasa.
 
 Yanzu 'yan mata nawa ne suka lalace ta dalilin 
haka? Nawa ne sukayi cikin shege ta dalilin irin wannan? Don haka bai 
halatta a matsayinki na 'Ya mace, ki yarda da wani shaitanin saurayi ya 
rika kusantarki yana Zina dake don kawai ya biya sadaki ba. Kawai 
yaudararki zai yi idan yayi zina dake yaji yadda kike, shikenan sai yaje
 yace ya fasa aurenki. Ya tura gidanku a karbo masa kudinsa shikenan ya 
lalata miki rayuwa.
 
 
 
 
          
      
 
  
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
No comments:
Post a Comment