Wednesday, 27 March 2013

AN KAFA KUNGIYAR IZALAH NE SABODA KAUDA BIDI'AH DA KUMA TSAIDA SUNNAR ANNABI MAI TSIRA DA AMINCIN ALLAH


AN KAFA KUNGIYAR IZALAH NE SABODA KAUDA BIDI'AH DA KUMA TSAIDA SUNNAR ANNABI MAI TSIRA DA AMINCIN ALLAH
27/3/2013

'Yan'uwa Musulmi masu kaunar Sunnah! Muna kara tunatar da ku cewa lalle an kafa Kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'iah Wa Iqamatis Sunnah ne a 1978 saboda a kauda dukkan wata bidiah da aka cusa cikin addinin Musulunci da sunan neman wata fa'ida a wurin Allah, sannan kuma a tsaida sunnar Annabi mai tsira da aminci cikin dukkan Aqiidah, da dukkan Ibaadah, da dukkan Mu'aamalah. Wannan shi ne dalilin kafa Kungiyar Izalah, kuma wannan ita ce manufar Izalah.

Saboda haka duk mutumin da ya ce an kafa kungiyar izala ne saboda kare wata mazhaba daga cikin mazhabobi, ko saboda kare muradun wani mutum daga cikin mutane, to lalle wannan mutum bai fadi gaskiya ba, lalle wannan mutum ya shara wa Kungiyar Izala karya, lalle wannan mutum ya ci amanar mutanen da suka hadu suka kafa wannan Kungiya tamu mai albarka.

Kuna iya fahimtar cewa duk wata mazhaba da ta saba wa nassin hadithin Manzon Allah, ko ta saba wa wani zahirin hadithin manzon Allah, cikin wata mas'ala daga cikin mas'aloli, to babu ruwan Kungiyar izala da bin wannan mazhabar cikin wannan mas'alar, a'a abin da Kungiyar Izala take yi shi ne: Sai ta bi nassin wannan hadithin, ko zahirin wannan hadithin ta bar abin da wancan mazhabar ta fada, saboda imanin da kungiyar take da shi na cewa ba a aiko mana da kowa ba cikin maluman wadannan mazhabobi, a'a wanda kawai Allah Ya aiko mana a matsayin Manzo shi ne: Annabi Muhammad mai tsira da amincin Allah.

Ga misali daya tak zan ba ku a wannan darasi namu: Tun da aka kafa wannan Kungiya tamu ta Izala, kungiyar take ta yin yaki da daura layu da guraye, kuma take ta bayyana wa al'ummar Duniya cewa daura laya shirka ce, hujjarta kuwa a kan wannan magana nata ita ce: Hadithan Manzon Allah da suka inganta cikin wannan mas'alar, kamar hadithin:-
((من تعلق تميمة فقد اشرك)).
Ma'ana: ((Duk wanda ya rataya laya to hakika ya yi ahirka)). Intaha.
A nana Annabi bai banbanta tsakanin layar da Alkur'ani ko wani ambaton Allah yake cikinta da kuma wacce babu wannan a cikinta ba, saboda haka Kungiyar izala ta yi aiki da umumi ta haramta dukkan abin da za a kira Laya.

Da luma hadithin:-
((ان الرقى والتمائم والتولة شرك)).
Ma'ana: ((Lalle Tawaida-tawaida, da kuma Layu, da Abubuwan sanya soyayya ko kiyayya tsakanin namiji da mace, shika ne)). Intaha.

Kungiyar Izala ta ci gaba da yakar layu dare da rana duk kuwa da cewa a mazhabar Malkiyyah halal ne mutum ya daura laya ko gurun da yake dauke da wasu ayoyin Alkur'ani ko kuma wasu kalmomi na ambaton Allah, kamar yadda ya zo cikin littattafan fikhun Malikiyyah kamar haka:-
1. Ya zo cikin Alfawaakihud Dawaanii sharhin Risalah t1/340 kamar haka:-
((ولا باس بالمعاذة وفيها القران)) 
Ma'ana: ((Babu laifi a daura layar da Alkur'ani yake cikinta)). Intaha.
2. Ya zo cikin Jawaahirul Ikliil sharhin Mukhtasar 1/21 kamar haka:-
((وحرز بساتر وان لحائض)).
Ma'ana: ((Layar da baduku ya rufa ta da fata halal ne a rataya ta, koda kuwa mace ce mai haila)). Intaha.
3. Ya zo cikin As'halul Madaarik kamar haka:-
((يجوز تعليق التمائم وهي العوذة التي تعلق على المريض والصبيان وفيها القران وذكر الله تعالى اذا خرز عليها جلد ويجوز تعليقها على المريض والصحيح خوفا من المرض والعين)).
Ma'ana: ((Yana halatta rataye layu, watau abin tsarin da ake rataya wa mara lafiya da kuma yara, alhali akwai Alkur'ani ko ambaton Allah Madaukaki a cikinsu, matukar dai an rufa layun da fata. Kuma rataya su na halatta ga mara lafiya, da ma wanda yake mai lafiya ne, saboda tsoron kada ya kamu da rashin lafiya ko kambun baka)). Intaha.

'Yan'uwa Musulmi masu kaunar Sunnah! Wannan ita ce Kungiyar Izala, sam ba ta barin abin da ya tabbata a cikin sunnar Annabi mai tsira da amincin, sannan ta koma ta yi riko da fatawar wata mazhaba daga cikin mazhabobi. 
Kuma Wannan shi zai tabbatar muku da cewa: Dukkan mutumin da za ku ji shi yana kyamar sahihiyar sunnar Manzon Allah cikin wata mas'ala yana cewa mu malikiyyah ne saboda haka mu abin da yake rubuce cikin mazhabar malkiyyah kadai za mu bi, domin ai su ma maluman Malikiyyan sun san da wancan hadithin amma kuma suka ki bin shi, saboda haka mu ma a nan da su za mu yi ko yi domin su ma ai magabata ne!! 
Lalle duk wanda kuka ji yana irin wadannan maganganu na shakiyanci da rashin mutunta sunnar Annabi, to lalle ku tabbatar da cewa ba dan izala ba ne na gaskiya, lalle ku tabbatar da cewa shi wannan shakiyyin mutum ya ci amanar Kungiyar Izala.

Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya tabbatar da dugaduganmu a kan sunnar Annabi mai tsira da aminci. Ame

No comments: