Wednesday, 13 March 2013
DALILAN DA YA SA TA’ADDANCI ZAI DADE BA A DAINA BA A WANNAN KASA TA NIGERIA
Duk wanda ya kasance hanyar da cimma manufofinsa ita ce ta hanyar zubar da jini da kisa to lallai wannan mutumin dan ta’addane. Daga yanzu ya bayyana cewa harkar ta’addanci ba kwai ya takaita ga wani dan gungun samarin musulmai ba ne wadanda suka zabi zubar da jini a matsayin hanyar cimma burinsu ko kuma ramuwar gayya a kan rashin adalcin da aka yi musu, ko ga musulmi kamar yadda suke fadi. A’a ayyukan ta’addanci sun fi karfin haka kuma basu takaitu ga wadannan samari ba kawai. Babu wanda ya san iyakan ayyukan ta’addanci, domin a cikin addini da kabilanci da wariyar launin fata da dai sauransu duk ana samun ayyukan ta’addanci a cikin su.
Mu dai a musulunci mun yi sa’a cewa, wasu ‘yan tsirarun samari ne suka riki wannan gurbatacciyar fahimta, domin musulunci yayi kakkausar suka da gargadi kan kashe rai ba da hakkin shari’aba. Kuma yin haddi na tabbata ne kadai idan al’umma suka hadu suka zabi shugaba ta hanyar shawara (shurah). To, irin wannan shugaba shi kadai ya ke da ikon zartar da haddi. In ba kadan da muke gani ba a yanzu, ya na da wuya musulmi kaga ya yi kisan kai.
Yawan kashe-kashe da ya yadu a kasashen yammaci, hakan ya faru ne a sakamakon rayuwa ta rashin da kuma rashin kula da yaduwar makamai a tsakaninsu. Akwai makamai ma su yawa a kasar Yamen a hannun mutane, amma saboda addini da kuma sani da suka yi na cewar addinin musulunci ya hana kashe rai ba da hakkinta ba, musulmi da wand aba musulmi ba sai ya kasance kasar bata da yawan kisa da zubar da jinni. Wannan kuwa ba haka ya ke ba a wani bangaren addini wanda ba musulunci ba.
Ayyukan ta’addanci da yafi muni a wannan kasa shine irin yadda jami’an tsaro na gwamnati suke amfani da damarsu suke kashe mutane ba tare da ji ko gani ba wadanda basu da laifi. Suna yin haka ne domin cimma wata manufa ta tabbatansu a kan mulki ko kuma domin cimma manufar siyasa.
Kamar a Najeriya mun ga yadda wadansu kiristoci suka kashe shuwagabannin musulmi don cimma manufarsu ta siyasa. Wadannan mutane sun fi hatsari fiye da ‘yan boko haram.
Manufarsu shine su rusa musulunci gaba dayansa ta hanyar karkashe shuwagabannin mu, domin su bar sauran al’ummar musulmi a matsayin bayi. Wannan shine dalilan da ya sa Abubakar Tafawa Balewa da Sardauna da Akintola da Gen. Murtala Muhammad suka rasa rayukunsu ta hanyar wadannan ‘yan ta’adda.
Wadannan ‘yan ta’adda su ne a yau wai su ke jagorancin fada da ta’addanci ko yaki da boko haram. Wannan yaki da suke yi sun fake ne da guzuma suna saran karsana. Domin sun kashe mana shuwagabanni a baya, yanzu kuma suna sake binsu tare da samarinmu suna kashe su lokaci guda. Ga yadda suke kara karfi a soja da madafun iko. Suna yi wa musulmai na kwarai ritaya don tabbatar da manufofinsu na ta’addanci da suka faro tun daga 1966.
Suna zaton suke da wuka da nama, don sun riga sun makance a cikin kiyayya tare da hassada da kuma ta’addanci. Har ba sa iya ganin cewa mugun aikinsu yana bayyana da manufofinsu tare da hujjoji. Ba sa iya ganin cewar Allah da kanSa ya dauki yakin da suke yi da musulumi da musulunci, yakin yanzu ya koma shi da su, saboda miyagun manufofinsu. Kaduna ma anso a mayar da ita kamar garin Maiduguri ne sai Allah ya shiga tsakani.
Sun manta cewar baka iya tabbatar da rayuwarka ko mulkin ka ta hanyar kashe wani, kana iya tsare rayuwar ka ne idan ka bar wani ya rayu kuma ya zauna lafiya (Kowa ya ce wutar kara ta kwana, to, shine ya kwana bai yi barci ba). Suna zaton cewar suna iya tabbata a mulki ta hanyar amfani da muggan makamai, sun manta cewa dukkan karfi ya tabbata ga Allah ne? Najeriya zata tabbata ne kuma ta zauna lafiya idan ire-iren wadannan mugayen mutane an kore su daga tsarin gwamnati da jami’an tsaro. A ka maye su da mutane na gari, wannan shine bangare mafi hatsari wanda mutane suka kau da kai daga gare shi, wanda wajibi ne mutane su lura su sa ido akai.
Miyagun ayyuka da muggan dabi’u ba za su kai ga nasara ba Insha Allah.
Allah ya tsare mu daga dukkan shar
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment