Saturday, 23 March 2013

HUKUNCIN YIN SALLA HANNAYE A SAKE BAYAN TSAYUWAR HUJJA, SABODA KAWAI TA'ASSUBANCI DA INAADI

HUKUNCIN YIN SALLA HANNAYE A SAKE BAYAN TSAYUWAR HUJJA, SABODA KAWAI TA'ASSUBANCI DA INAADI:
9/5/1434 H 21/3/2013 M

Sau da dama mu kan ji wasu mutane na cewa: Haba wasu fitinannu suna ta umurtan mutane da cewa su rika dora damansu a kan hagunsu cikin sallarsu, suna kuma cewa wai hakan Sunnah ce ta Annabi mai tsira da amincin Allah, wanda kuma ya nuna mata kyama to lalle wannan ya jawo wa kansa a sara!! To ga tambaya ga wadannan fitinannun: Mene ne hukuncina in har na yi salla hannayena a sake, shin sallata ta baci ne, shin ba'di ne, ko kabli yake kaina??

JAWABI:
Kafin mu ba da amsar tambaya a kan hukuncin wanda yake kyamatar sunnar dora dama a kan hagu a cikin salla, ya kamata mu yi bayani a kan wasu lamura guda biyu:-

Lamari na farko: Ya kamata a san cewa babu hadithi koda daya ne da ya inganta daga Annabi mai tsira da amincin Allah da ya ce Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya yi salla hannayensa a sake, ko kuwa ya yi umurni da hakan, ko kuwa an yi hakan a gabansa amma kuma bai hana ba.

Lamari na biyu: Ya kamata a san cewa Sunnah Kauliyyah, da Sunnah Fi'iliyyah, da Sunnah Takririyyah dukkan wadannan nau'uka uku na Sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah sun tabbatar da dora dama a kan hagu a cikin salla. Domin tabbatar da wannan magana a cikin sauki sai a dubi littafin Sifatu Salaatin Nabiyyi na Sheik Naasirud Diinil Albaanii shafi na 87-88.

Idan an fahimta daga bayanan da suka gabata cewa abin da sahihiyar Sunnar Annabi mai taira da amincin Allah ta zo da shi shi ne dora dama a kan hagu a cikin salla, ba wai yin salla hannaye a sake ba, to lalle wanda duk ya ki bin wannan Sunnah, ya ki bauta wa Allah da ita a cikin sallarsa, bayan hujja da tsayu gare shi, to kuwa wannan ya jawo wa kansa asara, saboda hukuncinsa ya fi karfin a ce ba'adi ne ko kabli yake kansa, ko kuma a'a sallar tasa ce ta baci saboda haka ya sake wata, a'a shi wannan bayan hujja ta tsayu a kansa hukuncinsa ya zarce wannan domin shi ya dauki hanyar kalubalantar Annabi ne bayan tsayuwar hujja, kamar mai yin rantsuwa ne a kan karya, ba a cewa da shi ya yi kaffara sai dai kawai ya tuba ya komo kan hanya.

Ga fatawowin babban malami a duniyar Ahlus Sunnah Wal Jama'ah Ibnu Taimiyah game da mai kyamar Sunnah cikin lamuransa.

Ibnu Taimiyah ya ce cikin Majmuu'ul Fataawaa 24/202:-
((واما من تبينت له السنة فظن ان غيرها خير منها فهو ضال مبتدع بل كافر)).
Ma'ana: ((Amma wannan da Sunnah ta bayyana gare shi, sannan ya yi zaton cewa waninta ya fi ta alheri, to shi dan'bidi'ah ne, kai kafiri ne ma)).

Sannan ya sake cewa cikin littafin 27/125:-
((ومن ترك النقل المصدق عن القائل المعصوم واتبع نقلا غير مصدق عن قائل غير معصوم فقد ضل ضلالا بعيدا)).
Ma'ana: ((Wanda ya bar nakalin da aka gaskata daga mai fada wanda yake ma'asuu'mi, sannan ya bi nakalin da ba a gaskata ba daga mai fadan da ba ma'asuu'mi ba, hakika ya bace bata mai nisa)).

Sannan ya sake cewa a cikin littafin 20/251:-
((وليس لاحد ان يعارض الحديث عن النبي صلى الله عليه وسلم بقول احد من الناس كما قال ابن عباس رضي الله عنهما لرجل ساله عن مسالة فاجابه فيها بحديث فقال له: قال ابو بكر وعمر فقال ابن عباس: يوشك ان تنزل عليكم حجارة من السماء اقول لكم قال رسول الله صلى الله عليه وسلم وتقولون قال ابو بكر وعمر)).
Ma'ana: ((Babu wanda yake da damar ya kalubalanci Hadithi daga Annabi mai tsira da amincin Allah saboda maganar wani mutum daga cikin mutane, kamar dai yadda Dan Abbas Allah Ya kara musu yarda ya ce wa wani mutumin da ya tambaye shi game da wata mas'ala' sai ya ba shi amsa da wani hadithi, sai mutumin ya ce da shi: Amma Abubakar, da Umar kuma sun ce!! Sai Dan Abbas ya ce: Duwatsu sun yi kusa su sauko a kanku, ina cewa da ku Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce, sannan ku kuma kuna cewa: Abubakar da Umar sun ce))?

Yan'uwa Musulmi! Wannan shi zai nuna mana jahilcin mai cewa: Ai tun da ba a rubuta a ckin Mukhtasar, ko Risalah ba cewa: Akwai kabli ko ba'adi a kan wanda bai sanya dama a kan hagu ba a cikin salla, to kuwa ni babu ruwana da dora dama a kan hagu a cikin sallata. Lalle wannan jahilin bai san cewa ba lalle hukuncin kyamatar sahihiyar sunnar Annabi shi ne bata da kafirci Allah Ya sawwake.

Sannan kuma in banda wauta, ko son zuciya ba, wane ne ya ce maka mai Mukhtasar, ko mai Risalah, ko mai Askari za ka bi ka bar bin Annabi muhammadu mai tsira da amincin Allah, a lokacin da maganarsu ta yi hannun riga da maganar shi Annabi?

Sannan dukkan daidaikun Musulmin duniyan nan babu ma'asuumi a cikinsu, Annabi shi ne kawai ma'asuumi shi kuma kawai wanda ake yi masa wahayi. Allah ya taimake mu ya raba mu da son zuciya da kuma aikin jahilci. Ameen. GA HADISIN DA ANNABI YA KOYAWAR DA SALLAH DA BAKIN SA MAI DARAJA, AMMA BAI WAJABTA DORA HANNUN DAMA AKAN HAGUN BA

ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ ﺃﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺩﺧﻞ ﺍﻟﻤﺴﺠﺪ ﻓﺪ ﺧﻞ ﺭﺟﻞ ﻓﺼﻠﻰ ﻓﺴﻠﻢ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﻓﺮﺩ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﻓﻘﺎﻝ ﺍﺭﺟﻊ ﻓﺼﻞ ﻓﺈﻧﻚ ﻟﻢ ﺗﺼﻞ ﻓﺮﺟﻊ ﻳﺼﻠﻲ ﻛﻤﺎ ﺻﻠﻰ ﺛﻢ ﺟﺎﺀ ﻓﺴﻠﻢ ﻋﻠﻲ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﻓﻘﺎﻝ ﺍﺭﺟﻊ ﻓﺼﻞ ﻓﺈﻧﻚ ﻟﻢ ﺗﺼﻞ ﺛﻼﺛﺎ ﻓﻘﺎﻝ ﻭﺍﻟﺬﻱ ﺑﻌﺜﻚ ﺑﺎﻟﺤﻖ ﻣﺎ ﺃﺣﺴﻦ ﻋﻴﺮﻩ ﻓﻌﻠﻤﻨﻲ ﻓﻘﺎﻝ ﺇﺫﺍ ﻗﻤﺖ ﺇﻯ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﻓﻜﺒﺮ ﺛﻢ ﺍﻗﺮﺃ ﻣﺎ ﺗﻴﺴﺮ ﻣﻌﻚ ﻣﻦ ﺍﻟﻘﺮﺁﻥ ﺛﻢ ﺍﺭﻛﻊ ﺣﺘﻰ ﺗﻄﻤﺌﻦ ﺭﺍﻛﻌﺎ ﺛﻢ ﺍﺭﻓﻊ ..... ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﺑﺎﺏ ﻭﺟﻮﺏ ﺍﻟﻘﺮﺍﺀﺓ

MA'ANA:

wata rana annabi ya shiga masallaci, sai ga wani mutum ya shigo masalacin yayi sallah, bayan ya idda sallah yazo yayi sallama, annabi ya
amsa kuma yace je ka sake sallah domin bakayi sallah ba, har sau uku. daga karshe wannan mutum yace na rantse
da wanda ya aiko ka da gaskiya ban iya wata sallah samada wannan ba ,Ya manzo Allah koyamin sallah sai annabi (saw) yace, idan
ka tashi zuwaga sallah kayi kabbara, sannan ka karanta abunda ya samu daga alqur'ani, sannan kayi rukuu har saika
daidaita, sannan ka dago saika daidaita a tsaye, sai kayi sujjada. daga karshe annabi yace haka zakayi a dukkan
sallarka.

Abun mamaki annabi bai wajabta masa dora dama akan haguba, sai wasu da wuce gona da iri suna cewa idan kayi sallah baka dora dama akan haguba wai kayi kabaira, don Allah ina suka samo wannan magana. Allah ka
shiryemu. Bukhari juz 2 shafi 203 hadisi 793, da 757.muslim hadisi 911.damansu a kan hagunsu cikin sallarsu, suna kuma cewa wai hakan Sunnah ce ta Annabi mai tsira da amincin Allah, wanda kuma ya nuna mata kyama to lalle wannan ya jawo wa kansa a sara!! To ga tambaya ga wadannan fitinannun: Mene ne hukuncina in har na yi salla hannayena a sake, shin sallata ta baci ne, shin ba'di ne, ko kabli yake kaina??

shiryemu. Bukhari juz 2 shafi 203 hadisi 793, da 757.muslim hadisi 911

No comments: