Wednesday, 28 August 2013
ALKALAMI SHI NE FARKON ABIN DA ALLAH YA HALITTA,
 BA HASKEN MANZON ALLAH KO ZATINSA BA, KAMAR YADDA MASU BIDI'A KE CEWA:
 ****************************** ***********
 KARA TUNATAR DA AL'UMMAR MUSULMI ABIN DA YA ZAMA WAJIBI SU YI IMANI DA SHI
 ****************************** ************
 
 Sau da dama 'Yan'uwa Musulmi za ku rika ganin cewa Sufaye da dukkan 
wadanda suka saki hanyar Shari'ah cikin tafiyar da addininsu suna barin 
yin aiki da nassin Alkur'ani, ko nassin ingantaccen hadithi, su koma 
suna yin aiki da nassoshin da ko dai su ne suka kirkiro su da kansu, ko 
kuwa a'a wasu hadithai ne masu rauni matuka, ko kuwa wasu hadithai ne na
 karya a bisa ittifakin masana ilmin hadithi!! 
 
 Misali: Imam 
Abu Daawuud ya ruwaito hadithi na 4,702, da Imamut Tirmizi hadithi na 
2,155, da Imam Ahmad hadithi na 22,757 daga Sahabi Ubaadatu Dan Saamit, 
haka nan ma Imamul Haakim cikin Mustadrak dinsa hadithi na 3,693, da 
Imamut Tabaraanii cikin Almu'ujamul Kabeer hadithi na 12,060, da Imamul 
Baihaqii cikin As-Sunanul Kubraa hadithi na 18,157 daga Sahaabi 
Abdullahi Dan Abbas, sannan Imamul Albaanii da sauran masana Ilmin 
Hadithi sun inganta shi, dukkan wadannan Sahabbai biyu ko wannensu ya 
ce:- 
 
 ((سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: ان اول ما خلق 
الله القلم، فقال له: اكتب. قال: رب وماذا اكتب؟ قال: اكتب مقادير كل شيء 
حتى تقوم الساعة)). انتهى. 
 
 Ma'ana: ((Na ji Manzon Allah mai 
tsira da amincin Allah yana cewa: Lalle farkon abin da Allah Ya halitta 
shi ne Alkalami, sannan Ya ce da shi: Ka rubuta, to sai ya ce: Ya 
Ubangijina mene ne zan rubuta? Sai Ya ce: Ka rubuta kaddarorin kome har 
Sa'ah ta tsaya)). Intaha.
 
 Kamar yadda kuke gani wannan nassi ne
 na sahihin hadithi, to amma kuma duk da haka sai ga shi Aluusii ya 
hikaito daga Sufaye cikin tafsirinsa mai suna Ruuhul Ma'aanii 17/105 
cewa sun ce ya zo cikin Hadithi cewa Annabi mai tsira da amincin Allah 
ya ce wa Sahabi Jabir Dan Abdullahi :-
 
 ((اول ما خلق الله تعالى نور نبيك يا جابر)). انتهى. 
 
 Ma'ana: ((Ya Jabir! Farkon abin da Allah Madaukakin Sarki Ya halitta shi ne hasken Annabinka)). Intaha.
 
 Don Allah ku duba ku ga irin yadda Sufaye suka bar yin aiki da 
ingantaccen hadithi, suka koma suka kirkiro wani hadithin karya  suka 
jingina shi zuwa ga Annabi mai tsira da amincin Allah, ta inda kuwa za 
ku fahimci cewa hadithi ne karya shi ne: Sam ba ya rubuce cikin 
littattafan hadithi sanannu, wannan shi ya sa ma a lokacin da Sheik 
Muhammad Jameel Zainu yake bayanin hadithai na karya cikin littafinsa 
Mai suna: Minhaajul Firqatin Naajiyah Wat Taa'ifatil Mansuurah shafi na 
74 ya ce:-
 
 ((اول ما خلق الله نور نبيك يا جابر". موضوع)). انتهى.
 
 Ma'ana: ((Ya Jabir! Farkon abin da Allah Ya halitta shi ne hasken 
Annabinka". maudhuu'ine)). Intaha. Haka ma Sheik Albanii ma a cikin 
littafinsa Silsilatul Ahaadithis Sahiihah 1/457 a lokacin da ya kawo 
hadithin nan na 2,996 da Imam Muslim ya ruwaito cikin Sahihinsa watau:-
 ((خلقت الملائكة من نور وخلق الجان من مارج من نار، وخلق ادم مما وصف لكم)). انتهى.
 
 Ma'an: ((An halicci Mala'iku daga wani irin haske ne, sannan an halicci
 Aljannu daga wani irin harshen wuta mai launin baki-baki ne, sannan 
kuma an halicci Adamu ne daga abin da aka siffanta muku)). Sai shi 
Albaanii ya ce:-
 ((فيه إشارة الى بطلان الحديث المشهور على السنة 
الناس: "اول ما خلق الله نور نبيك يا جابر" و نحوه من الأحاديث التي تقول 
بانه صلى الله عليه وسلم خلق من نور، فان هذا الحديث دليل واضح على ان 
الملائكة فقط هم الذين خلقوا من نور، دون ادم وبنيه، فتنبه ولا تكن من 
الغافلين)). انتهى.
 
 Ma'ana: ((Cikin wannan hadithin akwai 
isharar cewa hadithin nan da ya shahara cikin harsunan mutane, watau: 
"Ya Jabir farkon abin da Allah Ya halitta shi ne hasken annabinka" da ma
 irinsa daga cikin hadithan da suke cewa: Annabi mai tsira da amincin 
Allah an halicce shi ne daga wani irin haske magana ce ta karya. Lalle 
wannan hadithin hujja ce karara da ke nuna cewa: lalle Mala'iku ne kadai
 aka halitta su daga wani irin haske, amma banda Adamu da 'ya'yan shi. 
Sai ka fadaka, kada ka kasance daga cikin gafalallu)). Intaha.
 
 
Allah Ya shiryar da sufayenmu cikin wannan Al'ummah, da ma dukkan sauran
 karkatattu da ake da su cikin wannan Al'ummah Muhammadiyyah.
 
 Ya Allah! Ka nuna mana gaskiya gaskiya ce Ka ba mu ikon bin ta, Ka nuna mana karya karya ce Ka ba mu ikon guje mata. Ameen
Tuesday, 27 August 2013
MU SANYA AL'UMMAR MASAR CIKIN ADDU'O'INMU
 
 Yana daga cikin cikar Musuluncin Musulmi ya nuna damuwarsa saboda 
damuwar da ta samu 'yan'uwansa Musulmi wadanda ake zalunta a ma ko ina 
ne cikin wannan duniya tamu.
 
 Lalle muna nuna matukar bakin ciki
 da da takaici da irin yadda ake gallaza wa talakawan Kasar Masar 
talakawan da aka shaida musu cewa dimokuradiyya ce za a yi a kasarsu, 
watau duk wanda mafi yawan jama'a suka jefa wa kuri'a shi ne zai zama 
shugaban kasarsu, ko dan majalisar kasarsu. Sun fito zun zabi wadanda 
suke so, amma kuma azzulumai sun yi amfani da karfin bindiga suka kauda 
zabinsu!!
 
 Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da ya kawo wa 
talakawan Masar dauki, ya taimake su a kan azzalumai da suke zaluntarsu,
 ya dawo musu da wannan hakki nasu Cikin gaggawa, Ya kuma dawo musu da 
zama lafiya cikin wannan kasa tasu mai dimbin tarihi. Ameen
HARAMUN NE A SIFFANTA WANIN ALLAH DA CEWA SHI MASANIN GAIBI NE:
 
 Haramun ne wani mutum ya siffanta wata halitta daga cikin halittun 
Allah Madaukakin Sarki: Mala'iku ne, ko Annabawa da cewa shi wannan 
halitta masanin gaibi ne, domin yin hakan tamkar karyata Allah 
Madaukakin Sarki ne! 
 
 Hakan haramun ne saboda Allah Madaukakin Sarki Ya ce cikin Suratun Naml aya ta 65:-
 {قل لا يعلم من في السماوات والارض الغيب الا الله وما يشعرون ايان يبعثون}.
 
 Ma'an: {Ka ce: Babu wanda ya san gaibi a cikin Sammai da Kasa face Allah, kuma ba sa sanin cewa a yaushe ne ake tayar da su}.
 
 Lalle akwai ayoyi da hadithai masu yawan gaske da suke tabbatar da 
wannan ma'ana ta haramta sifanta wanin Allah da cewa shi masanin gaibi 
ne.
 
 KARIN HASKE
 
 Amma idan wani ya ce: Ni ina da hujjar
 halatta siffanta Annabi mai tsira da amincin Allah da cewa shi masanin 
gaibi ne, hujjar tawa kuwa ita ce:-
 
 Fadar Allah Madaukakin Sarki cikin Suratut Takwiir aya ta 24:-
 {وما هو على الغيب بضنين}.
 Ma'ana: {Kuma shi (Annabi) ba mai rowan gaibi ba ne}.
 
 Da kuma fadarSa cikin Suratu Aali Imran aya ta 44:-
 {ذلك من انباء الغيب نوحيه اليك}.
 Ma'ana: {Wannan daga labarun gaibi ne muke yin wahayinsa zuwa gare ka (ya kai Annabi) }.
 Da wasu nassosi masu kama da wannan to sai a ce da shi:-
 
 Gaibin da ya zo cikin wadannan nassosi yana nufin wahayin da Allah Yake
 yi ne zuwa ga manzanninSa, idan kuwa haka lamarin yake to ba zai 
halatta ba a siffanta su manzannin da cewa su masana gaibi ba ne, saboda
 abu biyu:-
 
 Na farko dai: Ba ya halatta a ce Alkur'ani zai karyata kansa da kansa, ko kuwa zai yi karo da junansa.
 Na biyu: Da zai halatta a siffanta Annabwan Allah da cewa su masana 
gaibi ne saboda wahayin da Allah Yake musu, wahayin da yake dauke da 
hukunce-hukunce, da kuma wasu abubuwa daban kamar irinsu labaru, to da 
hakan zai sa ya halatta a siffanta dukkan mutumin da manzannin za su 
isar masa da wannan aike da aka yi musu da cewa shi ma masanin gaibi ne!
 Saboda haka mu din nan da muke karanta Alkur'ani mai girma, da kuma 
Hadithai masu daraja muke sanin hukunce-hukunce da labarun gaskiya da 
suke cikinsu, ke nan zai halatta a siffanta mu da cewa: Mu masan gaibi 
ne!! Ina jin kuwa babu wani musulmi da zai yi jaraa'ar fadin haka.
 
 Misalin abin: Kamar shugaban kasa ne ya fidda wata doka sannan ya kira 
jami'in yada labarai a fadarsa ya ce da shi: Jeka ka karanta wa 
talkawana wannan dokar. Sannan shi jami'in yada labaran ya je karanta wa
 jama'ar kasa dokar kamar yadda shugaban kasa ya umurce shi.
 Kun ga 
ai babu wani mai hankali da zai kira wannan dokar da cewa doka ce ta 
jami'in yada labarai, a'a dukkan masu hankali suna sane da cewa dokace 
ta shugaban kasa, watau shugaban kasa shi ne mai dokar, koda kuwa shi 
jami'in yada labaru shi ya isar da ita zuwa ga sauran talakawa.
 
 Tun da aka fara duniyan nan har zuwa yanzu mu halittu: --Mala'ikunmu da
 Annabawanmu- ko wannenmu yana iya sanin wasu abubuwa sannan kuma yana 
iya jahiltan wasu abubuwan, wannan sifa ce tabbatacciya gare mu, duk 
kuwa mai irin wannan sifa haramun ne wani ya siffanta shi da cewa shi 
din nan masanin gaibi mutlaqii ne.
 
 Allah Ya taimake mu Ya tabbatar da dugaduginmu a kan sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah. Ameen.
DASUNAN ALLAH MAIRAHAMA MAIJINKAI.
 Tsira da amincin Allah sutabbata ga annabinmu maidaraja.
 Bayan haka:
 Duk hukuncin dayake da nassi na Al’qur’ani ko hadisi sahihi, wanda 
anriga anbayyanashi da nassi, tofa anan kowane irin qiyasi ko tawili 
basa shiga anan,domin anriga anyi nassi akai.don haka munbayyana muku 
ayoyin al’qur’ani da hadisan ma’aiki tsira da amincin Allah sutabbata 
agareshi,akan cewa acikin addinin musulunci ilimi shine sama da komai, 
samada kowa,malamine ke jagorancin addini , kamar yadda yazo cikin 
Alqur’ani da hadisi, kuma wannan shine hukuncin da Allah yayi da 
manzonsa,kuma haka magabata na kwarai suka fahimta ,babu dama asanya 
ra’ayi anan, bazaka iya ta’awilin wani abu awajanba,saidai kayi dayan 
abu biyu, na 1.kodai kakaryata ayoyin da hadisan da kowa yafahimcesu 
ayadda suke kazama kafiri. 2.kokuma kokagaskata ayoyin da hadisan da 
kowa yafahimcesu ayadda suke ,domin katabbata musulmi. domin Allah 
yariga yabayyana kuma Annabi(saw) ma yabayyana.kuma nan bawurin kiyasi 
bane ko ijitihadi wurinbine kawai na da’a . kamar yadda Allah yabayyana 
dabi’ar muminai game da hukunce hukuncen Allah (swa) ( Bashi yiwa ga 
wani mumini namiji ko wata mumina ta mace ace Allah da manzansa yayi 
nassi akan wani hukunci suwatsarda hukuncin Allah da manzansa subi wani 
zabi nason zuciyarsu , alhali kuwa ga nassi ) suratul ahzab ayata 36 
 HUKUNCIN DINKULEWA WURI GUDA GAMUMINAI
 Dunkulewa wuri guda wajibine, wato farillane, bawai sai mutum yaga 
damaba ,domin Allah (swa) yayi nassi akan dunkulewa,a’inda yake cewa : 
(kudunkule wuri guda ga igiyar Allah kada kurarrabu ) Ali imrana ayata 
103 zuwa ayata 105 inda Allah kecewa ( kada kuzamo kamar wadanda suka 
rarraba  suka sassabawa juna akan karya (wato kafirai ) tokaga anan 
dunkulewa wuri guda ga musulmi masu imani da Alkitabu wassunnah dolene  
basu da wani  zabi , kuma anan zamu iya ganewa dukkan wanda baidauki 
wannan dunkulewa wajibineba kuma yayi watsi da wannnan nassi ya gitta 
wani sharadi nasa nakashin kansa , yace sai anbiya masa wata bukata tasa
 , kosai anbashi shugabanci na mutane gaba daya , abisa jahilcinsa 
inba’abashiba to yafasa dunkulewar, to wannan gaskiya munafikine babu 
wani addini gareshi shida duk wanda yagoyi bayansa akan haka , 
ballantana acesu ahlussunnane .don haka ina kira da babbar murya zuwa ga
 wadanda suka fahimci addini, sudaina wahalarda kansu wajen tunani 
gameda wanda badan izala ba, wanda bai fahimci komaiba yadda suka 
fahimta , wanda suna kawai na izala yake amfani dashi, domin biyan wata 
bukata tasa, saboda izala tayi darajarda basuyi tsammaniba, alhali kuwa 
ku fahimtane yakawoku dagaske , baikamata kubata lokacinku kan wanda bai
 fahimci komaiba sai neman girma kawai, yana tsammanin abin abanza kawai
 yake ba sai anyi aikiba , don haka Ahlussunnah na kwarai sun yarda 
dahadin kannan, sunyi imani da Alqur’ani da hadisi , don haka sukazo 
muka hade, gasunan munata mu’amala tare dasu, tundaga kan sheikh yusuf 
sambo Rigacukum da almajiransa da sheikh Rabi’u Daura da almajiransa , 
da,da,da,da,da. Duk Sun amince da hukuncin al’qur’ani da hadisi kamar 
yadda Allah yayi nasssi akan dunkulewa , batare da gitta wani sharadiba,
 amma kaga wadanda basuyi imaniba sunyi watsi da wannan nassin , tunda 
ba’abiya musu bukatarsuba dasukazo nema bisa sharadinda suka gitta na 
kashin kansu, wanda ba Alqur’aniba kuma ba hadisiba, ya ‘yan uwa musulmi
 gaba daya  kusani zamowa dan izala yanada tsada , bakowa kesamun wannan
 darajaba sai wanda Allah yanufa,saboda haka Allah ma yahana muminai 
surinka damuwa kan sha’anin munafukai , don haka kudaina kulasu , saboda
 haka nan Allah ke cewa : ( To menene yasameku acikin munafukai, kunzama
 qungiya biyu , alhali kuwa Allah ne ya mayardasu baya ( wato ya 
dilmiyardasu) saboda abinda suka aikata (na munafunci) shin kuna nufin 
kushiryar da wanda Allah yabatarne ?! kuma wanda Allah yabatar to 
bazakasamu wata hanyar shiryarshiriyaba agareshi ) Al’imrana ayata 88 
Saboda haka muyita wa’azinmu kawai kuma muyi watsi da wadanda Allah ya 
dilmiyar dasu saboda munafuncinda suka aikata,domin duk wanda yaki 
karbar nassin Alqur’ani bayyananne yayi nisanda bazai fahimci wa’aziba 
ko anyi .saboda haka manzon Allah (saw) dukda irin bayanin daya iya mai 
gamsarwa, haryakoma ga ubangijinsa yabar munafukai basu gamsuba,to waye 
kuma yake da bayaninda zai gamsardasu, baku ganin Abdullahi bn ubayyu bn
 salul,saboda shugabancinnan da ba’abashiba, yazama munafiki kuma yana 
sallah kuma yakanje jahadi tare da Annabi (saw) amma saboda mulkin da 
ba’abashiba yadoje amunafurci harya mutu haka .
 wato asalin abin Dan
 salul shiza’a nada sarki kamin Annabi (saw) yazo madina ,kafin anadashi
 Annabi (saw) yazo madina. To kaga babu maganar wani shugaba amadina sai
 Annabi (saw) to saboda rashin samun shugabancinnan yacigaba  da 
munafunci har karshen rayuwarsa.ammashi yamutu gabanin manzom Allah 
(saw) yamutu. saidai Dan salul yabar masu rufa masa baya masu yawa, 
wadanda har manzon Allah (saw) yakoma ga ubangijinsu basu gamsuba . 
Allah yatsaremu daga sharrin munafukai.
 Wato babban abinda nake 
kokarin ganarda ‘yan uwana ahlussunnah anan shine, mufahinci cewa iya 
ahlussunnafa sunzo mun hade, amma wadanda suka rage suna jayayyannan 
basu fahimci sunnah bafa , sabooda haka ‘yan gargajiyane dasunan 
izala,saboda haka kowa yasan suna bashine aikiba, baku ganin sunabin 
kowane mutum sallah kuma suci yankan kowa, kuma kowanne irin shirme zaka
 samesu aciki, to masu irin wannan dabi’ar kake cewa ‘yan izalanesu ?
 Wassalamu alaikum. Sai haduwa nagaba insha Allahu
Subscribe to:
Comments (Atom)
