Tuesday, 27 August 2013

DASUNAN ALLAH MAIRAHAMA MAIJINKAI.
Tsira da amincin Allah sutabbata ga annabinmu maidaraja.
Bayan haka:
Duk hukuncin dayake da nassi na Al’qur’ani ko hadisi sahihi, wanda anriga anbayyanashi da nassi, tofa anan kowane irin qiyasi ko tawili basa shiga anan,domin anriga anyi nassi akai.don haka munbayyana muku ayoyin al’qur’ani da hadisan ma’aiki tsira da amincin Allah sutabbata agareshi,akan cewa acikin addinin musulunci ilimi shine sama da komai, samada kowa,malamine ke jagorancin addini , kamar yadda yazo cikin Alqur’ani da hadisi, kuma wannan shine hukuncin da Allah yayi da manzonsa,kuma haka magabata na kwarai suka fahimta ,babu dama asanya ra’ayi anan, bazaka iya ta’awilin wani abu awajanba,saidai kayi dayan abu biyu, na 1.kodai kakaryata ayoyin da hadisan da kowa yafahimcesu ayadda suke kazama kafiri. 2.kokuma kokagaskata ayoyin da hadisan da kowa yafahimcesu ayadda suke ,domin katabbata musulmi. domin Allah yariga yabayyana kuma Annabi(saw) ma yabayyana.kuma nan bawurin kiyasi bane ko ijitihadi wurinbine kawai na da’a . kamar yadda Allah yabayyana dabi’ar muminai game da hukunce hukuncen Allah (swa) ( Bashi yiwa ga wani mumini namiji ko wata mumina ta mace ace Allah da manzansa yayi nassi akan wani hukunci suwatsarda hukuncin Allah da manzansa subi wani zabi nason zuciyarsu , alhali kuwa ga nassi ) suratul ahzab ayata 36
HUKUNCIN DINKULEWA WURI GUDA GAMUMINAI
Dunkulewa wuri guda wajibine, wato farillane, bawai sai mutum yaga damaba ,domin Allah (swa) yayi nassi akan dunkulewa,a’inda yake cewa : (kudunkule wuri guda ga igiyar Allah kada kurarrabu ) Ali imrana ayata 103 zuwa ayata 105 inda Allah kecewa ( kada kuzamo kamar wadanda suka rarraba suka sassabawa juna akan karya (wato kafirai ) tokaga anan dunkulewa wuri guda ga musulmi masu imani da Alkitabu wassunnah dolene basu da wani zabi , kuma anan zamu iya ganewa dukkan wanda baidauki wannan dunkulewa wajibineba kuma yayi watsi da wannnan nassi ya gitta wani sharadi nasa nakashin kansa , yace sai anbiya masa wata bukata tasa , kosai anbashi shugabanci na mutane gaba daya , abisa jahilcinsa inba’abashiba to yafasa dunkulewar, to wannan gaskiya munafikine babu wani addini gareshi shida duk wanda yagoyi bayansa akan haka , ballantana acesu ahlussunnane .don haka ina kira da babbar murya zuwa ga wadanda suka fahimci addini, sudaina wahalarda kansu wajen tunani gameda wanda badan izala ba, wanda bai fahimci komaiba yadda suka fahimta , wanda suna kawai na izala yake amfani dashi, domin biyan wata bukata tasa, saboda izala tayi darajarda basuyi tsammaniba, alhali kuwa ku fahimtane yakawoku dagaske , baikamata kubata lokacinku kan wanda bai fahimci komaiba sai neman girma kawai, yana tsammanin abin abanza kawai yake ba sai anyi aikiba , don haka Ahlussunnah na kwarai sun yarda dahadin kannan, sunyi imani da Alqur’ani da hadisi , don haka sukazo muka hade, gasunan munata mu’amala tare dasu, tundaga kan sheikh yusuf sambo Rigacukum da almajiransa da sheikh Rabi’u Daura da almajiransa , da,da,da,da,da. Duk Sun amince da hukuncin al’qur’ani da hadisi kamar yadda Allah yayi nasssi akan dunkulewa , batare da gitta wani sharadiba, amma kaga wadanda basuyi imaniba sunyi watsi da wannan nassin , tunda ba’abiya musu bukatarsuba dasukazo nema bisa sharadinda suka gitta na kashin kansu, wanda ba Alqur’aniba kuma ba hadisiba, ya ‘yan uwa musulmi gaba daya kusani zamowa dan izala yanada tsada , bakowa kesamun wannan darajaba sai wanda Allah yanufa,saboda haka Allah ma yahana muminai surinka damuwa kan sha’anin munafukai , don haka kudaina kulasu , saboda haka nan Allah ke cewa : ( To menene yasameku acikin munafukai, kunzama qungiya biyu , alhali kuwa Allah ne ya mayardasu baya ( wato ya dilmiyardasu) saboda abinda suka aikata (na munafunci) shin kuna nufin kushiryar da wanda Allah yabatarne ?! kuma wanda Allah yabatar to bazakasamu wata hanyar shiryarshiriyaba agareshi ) Al’imrana ayata 88 Saboda haka muyita wa’azinmu kawai kuma muyi watsi da wadanda Allah ya dilmiyar dasu saboda munafuncinda suka aikata,domin duk wanda yaki karbar nassin Alqur’ani bayyananne yayi nisanda bazai fahimci wa’aziba ko anyi .saboda haka manzon Allah (saw) dukda irin bayanin daya iya mai gamsarwa, haryakoma ga ubangijinsa yabar munafukai basu gamsuba,to waye kuma yake da bayaninda zai gamsardasu, baku ganin Abdullahi bn ubayyu bn salul,saboda shugabancinnan da ba’abashiba, yazama munafiki kuma yana sallah kuma yakanje jahadi tare da Annabi (saw) amma saboda mulkin da ba’abashiba yadoje amunafurci harya mutu haka .
wato asalin abin Dan salul shiza’a nada sarki kamin Annabi (saw) yazo madina ,kafin anadashi Annabi (saw) yazo madina. To kaga babu maganar wani shugaba amadina sai Annabi (saw) to saboda rashin samun shugabancinnan yacigaba da munafunci har karshen rayuwarsa.ammashi yamutu gabanin manzom Allah (saw) yamutu. saidai Dan salul yabar masu rufa masa baya masu yawa, wadanda har manzon Allah (saw) yakoma ga ubangijinsu basu gamsuba . Allah yatsaremu daga sharrin munafukai.
Wato babban abinda nake kokarin ganarda ‘yan uwana ahlussunnah anan shine, mufahinci cewa iya ahlussunnafa sunzo mun hade, amma wadanda suka rage suna jayayyannan basu fahimci sunnah bafa , sabooda haka ‘yan gargajiyane dasunan izala,saboda haka kowa yasan suna bashine aikiba, baku ganin sunabin kowane mutum sallah kuma suci yankan kowa, kuma kowanne irin shirme zaka samesu aciki, to masu irin wannan dabi’ar kake cewa ‘yan izalanesu ?
Wassalamu alaikum. Sai haduwa nagaba insha Allahu

No comments: