ALKALAMI SHI NE FARKON ABIN DA ALLAH YA HALITTA,
BA HASKEN MANZON ALLAH KO ZATINSA BA, KAMAR YADDA MASU BIDI'A KE CEWA:
*****************************************
KARA TUNATAR DA AL'UMMAR MUSULMI ABIN DA YA ZAMA WAJIBI SU YI IMANI DA SHI
******************************************
Sau da dama 'Yan'uwa Musulmi za ku rika ganin cewa Sufaye da dukkan
wadanda suka saki hanyar Shari'ah cikin tafiyar da addininsu suna barin
yin aiki da nassin Alkur'ani, ko nassin ingantaccen hadithi, su koma
suna yin aiki da nassoshin da ko dai su ne suka kirkiro su da kansu, ko
kuwa a'a wasu hadithai ne masu rauni matuka, ko kuwa wasu hadithai ne na
karya a bisa ittifakin masana ilmin hadithi!!
Misali: Imam
Abu Daawuud ya ruwaito hadithi na 4,702, da Imamut Tirmizi hadithi na
2,155, da Imam Ahmad hadithi na 22,757 daga Sahabi Ubaadatu Dan Saamit,
haka nan ma Imamul Haakim cikin Mustadrak dinsa hadithi na 3,693, da
Imamut Tabaraanii cikin Almu'ujamul Kabeer hadithi na 12,060, da Imamul
Baihaqii cikin As-Sunanul Kubraa hadithi na 18,157 daga Sahaabi
Abdullahi Dan Abbas, sannan Imamul Albaanii da sauran masana Ilmin
Hadithi sun inganta shi, dukkan wadannan Sahabbai biyu ko wannensu ya
ce:-
((سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: ان اول ما خلق
الله القلم، فقال له: اكتب. قال: رب وماذا اكتب؟ قال: اكتب مقادير كل شيء
حتى تقوم الساعة)). انتهى.
Ma'ana: ((Na ji Manzon Allah mai
tsira da amincin Allah yana cewa: Lalle farkon abin da Allah Ya halitta
shi ne Alkalami, sannan Ya ce da shi: Ka rubuta, to sai ya ce: Ya
Ubangijina mene ne zan rubuta? Sai Ya ce: Ka rubuta kaddarorin kome har
Sa'ah ta tsaya)). Intaha.
Kamar yadda kuke gani wannan nassi ne
na sahihin hadithi, to amma kuma duk da haka sai ga shi Aluusii ya
hikaito daga Sufaye cikin tafsirinsa mai suna Ruuhul Ma'aanii 17/105
cewa sun ce ya zo cikin Hadithi cewa Annabi mai tsira da amincin Allah
ya ce wa Sahabi Jabir Dan Abdullahi :-
((اول ما خلق الله تعالى نور نبيك يا جابر)). انتهى.
Ma'ana: ((Ya Jabir! Farkon abin da Allah Madaukakin Sarki Ya halitta shi ne hasken Annabinka)). Intaha.
Don Allah ku duba ku ga irin yadda Sufaye suka bar yin aiki da
ingantaccen hadithi, suka koma suka kirkiro wani hadithin karya suka
jingina shi zuwa ga Annabi mai tsira da amincin Allah, ta inda kuwa za
ku fahimci cewa hadithi ne karya shi ne: Sam ba ya rubuce cikin
littattafan hadithi sanannu, wannan shi ya sa ma a lokacin da Sheik
Muhammad Jameel Zainu yake bayanin hadithai na karya cikin littafinsa
Mai suna: Minhaajul Firqatin Naajiyah Wat Taa'ifatil Mansuurah shafi na
74 ya ce:-
((اول ما خلق الله نور نبيك يا جابر". موضوع)). انتهى.
Ma'ana: ((Ya Jabir! Farkon abin da Allah Ya halitta shi ne hasken
Annabinka". maudhuu'ine)). Intaha. Haka ma Sheik Albanii ma a cikin
littafinsa Silsilatul Ahaadithis Sahiihah 1/457 a lokacin da ya kawo
hadithin nan na 2,996 da Imam Muslim ya ruwaito cikin Sahihinsa watau:-
((خلقت الملائكة من نور وخلق الجان من مارج من نار، وخلق ادم مما وصف لكم)). انتهى.
Ma'an: ((An halicci Mala'iku daga wani irin haske ne, sannan an halicci
Aljannu daga wani irin harshen wuta mai launin baki-baki ne, sannan
kuma an halicci Adamu ne daga abin da aka siffanta muku)). Sai shi
Albaanii ya ce:-
((فيه إشارة الى بطلان الحديث المشهور على السنة
الناس: "اول ما خلق الله نور نبيك يا جابر" و نحوه من الأحاديث التي تقول
بانه صلى الله عليه وسلم خلق من نور، فان هذا الحديث دليل واضح على ان
الملائكة فقط هم الذين خلقوا من نور، دون ادم وبنيه، فتنبه ولا تكن من
الغافلين)). انتهى.
Ma'ana: ((Cikin wannan hadithin akwai
isharar cewa hadithin nan da ya shahara cikin harsunan mutane, watau:
"Ya Jabir farkon abin da Allah Ya halitta shi ne hasken annabinka" da ma
irinsa daga cikin hadithan da suke cewa: Annabi mai tsira da amincin
Allah an halicce shi ne daga wani irin haske magana ce ta karya. Lalle
wannan hadithin hujja ce karara da ke nuna cewa: lalle Mala'iku ne kadai
aka halitta su daga wani irin haske, amma banda Adamu da 'ya'yan shi.
Sai ka fadaka, kada ka kasance daga cikin gafalallu)). Intaha.
Allah Ya shiryar da sufayenmu cikin wannan Al'ummah, da ma dukkan sauran
karkatattu da ake da su cikin wannan Al'ummah Muhammadiyyah.
Ya Allah! Ka nuna mana gaskiya gaskiya ce Ka ba mu ikon bin ta, Ka nuna mana karya karya ce Ka ba mu ikon guje mata. Ameen
No comments:
Post a Comment