MU SANYA AL'UMMAR MASAR CIKIN ADDU'O'INMU
Yana daga cikin cikar Musuluncin Musulmi ya nuna damuwarsa saboda
damuwar da ta samu 'yan'uwansa Musulmi wadanda ake zalunta a ma ko ina
ne cikin wannan duniya tamu.
Lalle muna nuna matukar bakin ciki
da da takaici da irin yadda ake gallaza wa talakawan Kasar Masar
talakawan da aka shaida musu cewa dimokuradiyya ce za a yi a kasarsu,
watau duk wanda mafi yawan jama'a suka jefa wa kuri'a shi ne zai zama
shugaban kasarsu, ko dan majalisar kasarsu. Sun fito zun zabi wadanda
suke so, amma kuma azzulumai sun yi amfani da karfin bindiga suka kauda
zabinsu!!
Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da ya kawo wa
talakawan Masar dauki, ya taimake su a kan azzalumai da suke zaluntarsu,
ya dawo musu da wannan hakki nasu Cikin gaggawa, Ya kuma dawo musu da
zama lafiya cikin wannan kasa tasu mai dimbin tarihi. Ameen
No comments:
Post a Comment