HARAMUN NE A SIFFANTA WANIN ALLAH DA CEWA SHI MASANIN GAIBI NE:
Haramun ne wani mutum ya siffanta wata halitta daga cikin halittun
Allah Madaukakin Sarki: Mala'iku ne, ko Annabawa da cewa shi wannan
halitta masanin gaibi ne, domin yin hakan tamkar karyata Allah
Madaukakin Sarki ne!
Hakan haramun ne saboda Allah Madaukakin Sarki Ya ce cikin Suratun Naml aya ta 65:-
{قل لا يعلم من في السماوات والارض الغيب الا الله وما يشعرون ايان يبعثون}.
Ma'an: {Ka ce: Babu wanda ya san gaibi a cikin Sammai da Kasa face Allah, kuma ba sa sanin cewa a yaushe ne ake tayar da su}.
Lalle akwai ayoyi da hadithai masu yawan gaske da suke tabbatar da
wannan ma'ana ta haramta sifanta wanin Allah da cewa shi masanin gaibi
ne.
KARIN HASKE
Amma idan wani ya ce: Ni ina da hujjar
halatta siffanta Annabi mai tsira da amincin Allah da cewa shi masanin
gaibi ne, hujjar tawa kuwa ita ce:-
Fadar Allah Madaukakin Sarki cikin Suratut Takwiir aya ta 24:-
{وما هو على الغيب بضنين}.
Ma'ana: {Kuma shi (Annabi) ba mai rowan gaibi ba ne}.
Da kuma fadarSa cikin Suratu Aali Imran aya ta 44:-
{ذلك من انباء الغيب نوحيه اليك}.
Ma'ana: {Wannan daga labarun gaibi ne muke yin wahayinsa zuwa gare ka (ya kai Annabi) }.
Da wasu nassosi masu kama da wannan to sai a ce da shi:-
Gaibin da ya zo cikin wadannan nassosi yana nufin wahayin da Allah Yake
yi ne zuwa ga manzanninSa, idan kuwa haka lamarin yake to ba zai
halatta ba a siffanta su manzannin da cewa su masana gaibi ba ne, saboda
abu biyu:-
Na farko dai: Ba ya halatta a ce Alkur'ani zai karyata kansa da kansa, ko kuwa zai yi karo da junansa.
Na biyu: Da zai halatta a siffanta Annabwan Allah da cewa su masana
gaibi ne saboda wahayin da Allah Yake musu, wahayin da yake dauke da
hukunce-hukunce, da kuma wasu abubuwa daban kamar irinsu labaru, to da
hakan zai sa ya halatta a siffanta dukkan mutumin da manzannin za su
isar masa da wannan aike da aka yi musu da cewa shi ma masanin gaibi ne!
Saboda haka mu din nan da muke karanta Alkur'ani mai girma, da kuma
Hadithai masu daraja muke sanin hukunce-hukunce da labarun gaskiya da
suke cikinsu, ke nan zai halatta a siffanta mu da cewa: Mu masan gaibi
ne!! Ina jin kuwa babu wani musulmi da zai yi jaraa'ar fadin haka.
Misalin abin: Kamar shugaban kasa ne ya fidda wata doka sannan ya kira
jami'in yada labarai a fadarsa ya ce da shi: Jeka ka karanta wa
talkawana wannan dokar. Sannan shi jami'in yada labaran ya je karanta wa
jama'ar kasa dokar kamar yadda shugaban kasa ya umurce shi.
Kun ga
ai babu wani mai hankali da zai kira wannan dokar da cewa doka ce ta
jami'in yada labarai, a'a dukkan masu hankali suna sane da cewa dokace
ta shugaban kasa, watau shugaban kasa shi ne mai dokar, koda kuwa shi
jami'in yada labaru shi ya isar da ita zuwa ga sauran talakawa.
Tun da aka fara duniyan nan har zuwa yanzu mu halittu: --Mala'ikunmu da
Annabawanmu- ko wannenmu yana iya sanin wasu abubuwa sannan kuma yana
iya jahiltan wasu abubuwan, wannan sifa ce tabbatacciya gare mu, duk
kuwa mai irin wannan sifa haramun ne wani ya siffanta shi da cewa shi
din nan masanin gaibi mutlaqii ne.
Allah Ya taimake mu Ya tabbatar da dugaduginmu a kan sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah. Ameen.
No comments:
Post a Comment