Wednesday, 28 August 2013


MAGANIN HASSADA A ZUCIYA!!!

Sanin girman laifinsa a wurin Allah da cewa shi (Laifi) ne dake cinye aikin kwarai, kamar yadda wuta take cin itatuwa, kamar yadda ya inganta a cikin hadithi.

Abin da Allah Ta'ala ya baiwa waninka to wannan karkashin ikon Allah ne da kuma hikimarsa. Kuma rashin yarda da hakan, yana nuni ne zuwa ga kauda kai daga Allah.
Kuma raunin imani ne da abin da Allah ta'ala ya kaddara, kuma ya hukunta

Yawan fadin cewa: MASHA ALLAHU , TABARAKALLAH; Ma'ana: "Haka Allah yaso, Allah yayi albarka".
Wannan kuwa yana faruwa ne a duk lokacin da mutum yaga abin da yake burge shi.
Yin hakan yana nunawar cewa kana da kyakkyawar zuciya.

Sanin ladan da Allah ta'ala yake bayarwa ga duk wanda ya guji hassada.
Duk wanda yayi barci alhali babu hassada a cikin zuciyarsa ga dayanmu, lallai ladansa mai girma ne.
Kamar yadda ya tabbata daga Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi, " Lallai yayiwa daya daga cikin sahabbansa bushara da aljannah.
Abdullahi dan Umar Allah ya kara masa yarda, yaje gidan wannan mutumin ya kwana kuma ya sami tabbacin cewa babu abin da ya sanya har ya sami wannan bushara face yana kwana ne babu wani a cikin ransa.

Yan uwa mu guji hassada a dukkan lamuran mu, mu daina sa haushin wani namu ya samu wani abu, dukkan abin da ka samu rabonka ne, haka dukkan abin da ka rasa ba rabonka bane, duk bakin cikin mai bakin ciki ko hassadar mai hassada basu iya hanama abin da Allah ya hukunta rabonka ne, Allah yasa mu gane.

No comments: