Saturday, 20 July 2013


And upon Allâh is the responsibility to explain the Straight Path (i.e. Islâmic Monotheism for mankind i.e. to show them legal and illegal, good and evil things, etc. so, whosoeveraccepts the guidance, it will be for his own benefit and whosoever goes astray, it will be for his own destruction), but there are ways that turn aside (such as Paganism,Judaism, Christianity, etc.). And had He willed, He would have guided you all (mankind). (An-Nahl 16:9)

Tambayata itace yarinya ce ake labarin cewar tayi ciki to amma ance an zubar da cikin,to kuma wani ya Ganta yanaso shin ya halatta ya aureta???
(daga Abubakar kogo Ibrahim)

AMSA
*******
Eh ya halatta ya aureta tunda shi MUSULUNCI ba ya aiki da zargi a irin wannan mas'alar sai dai abinda aka tabbatar.

Idan kuwa an tabbatar, an ganta da cikin (juna biyun) alhali bata ta'ba aure ba, sannan kuma daga baya aka ganta babu cikin, wato ta rabu da cikin ta wata hanya, kamar haifewa ko bari, ko kuma zubarwa (kamar yadda ka ambata) to shikenan idan ta tuba, cikakkiyar tuba, to ya halatta ka aureta idan kaga kana bukata.

Amma idan bata tuba ba, to Malamaisunce HARAMUN NE MUTUM ya auri mazinaciya alhali yana sane.

Suna kafa hujja ne da ayar nan ta 3 acikin SURATUN NUUR.

Sannan hakki ne wanda ya rataya awuyanka, ka zaba ma yaronka uwatagari.
WALLAHU A'ALAM.
YA ALLAH KA SHIRYAR MANA DA DUKKAN ZURRIYYARMU da dukka al'ummar musulmi.
Aaaaameeeeen.
DAFATAN ANSHA RUWA LAFIYA,MALAM IDAN
MATAFIYI YANA KASARU IDAN YA GA DAHALIN BIN JAM'I WATO RAKA'A [4] ZAI IYA BI ?
(DAGA SHEHU MUH'D)

AMSA
*******
Eh zai iya bi. Amma kuma mafi alkhairi gareshi shine ya tsaya akan sunnarsa (wato raka'a biyu) zai yi ko shine yake limanci ko kuma bi yake yi.

Imam ABU ZAYD ALQAIRAWANY (rah) yana cewa:
"IDAN MATAFIYI YABI MAI ZAMAN GIDA A SALLAH, KO KUMA SHI MAI ZAMAN GIDAN YABI MATAFIYI, TO KOWANNE ZAI TSAYA NE AKAN SUNNARSA"
Wato mazaunin gida zai cika sallarsa, shi kuma matafiyi zai yi kasarunsa.
Sannan kuma yana da za'bi biyu anan.

1. Ko dai yayi sallamarsa da zarar anyi raka'a biyu.

2. Ko kuma idan anyi raka'a biyu sai yaci gaba da zama a inda yake, har Limaminsa ya ciko raka'a biyunsa, sannan idan limaminsa yayi sallama, shima sai yayi tasa.

Irin abinda wasu suke yi idan sunyi tafiyar data dace suyi Qasaru, sai suki yi wai AI SU BASU DAUKO TA TUN DAGA GIDA BA.
Wannan kuskure ne. ai ita Qasaru ba daukota akeyi ba. a'a sauki ne wanda Allah yayiwa bayinsa. kuma ALLAH yana so idan yayiwa bayinsa sauki, to su yi amfani da wannan saukin.

Amma cika sallah ayayin tafiyar da takai ayi mata Qasaru, wannan bai dace da sunnah ba.Sai dai idan mutum yana da niyyar zama achan garin fiye da kwana 4, (salloli 20) to anan malamai masanan fiqhu irinsu Imamu Malik da Imamush Shafi'iy sunce zai cika sallarsa ne.
WALLAHU A'ALAM.
Assalam Alaikum Wa Rahmatullahi Ta'ala Wa Barakatuh.
Jama'ar wannan zaure namu mai tarin albarka muna muku barka da warhaka, Barkamu da sake saduwa a wannan rana mai Tarin falala, muna rokon Allah ya sadamu da dukkan alkhairan dake cikinta ya kuma tsaremu da dukkan sharin dake cikinta.
Sannan muna Murnar sanar da yan uwa cewa wannan shafi namu mai tarin albarka yau Allah ya yimasa cika mutum 100, 000. muna rokon Allah yadda ya hadamu a nan, Allah ya hadamu cikin Aljannatul Firdaus, Ameen. Muna sake godewa yan uwa dalibai da suke ta kokarin yada kalmar Allah da sunnar manzonsa. Allah ya bamu dacewa da dai dai Ameen.
Assalam alaikum Wa Rahmatullahi Ta'ala Wa Barakatuh.
Jama'a barkanmu da warhaka barkanmu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka, a cikin wannan wata mai tarin abarka.
Watan da Allah (S.W.T) ya saukarwa da Manzon sa (S.A.W) Alkur'ani mai girma, watan da ake Bude duk wata kofa ta rahama da gafara da ni'ima, watan da ake daure shaidanu, ake kulle wuta. Muna Rokon Allah (S.W.A) ya hadamu da dukkan alkhairan dake kunshe cikin wannan watan kuma ya karemu daga sabawa Allah a cikin wannan watan

Tafsiran Rana ta 1 zuwa ta rana 5.

Alhamdulillah! Cikin yardan Allah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Ya samu nasaran kammala Tafsirin suratul Mujadilah a tafsirin sa na bana (1434).

Kana iya sauraran Tafsiran duka ta wadannan links:

1st Ramadan, 1434: http://www.dandalinsunnah.com/multimedia/amb//tafseer/daurawa/2013/day1.mp3

2nd Ramadan, 1434: http://www.dandalinsunnah.com/multimedia/amb//tafseer/daurawa/2013/day2.mp3

3rd Ramadan, 1434 (By Sheikh Sulaiman kumo) : http://www.dandalinsunnah.com/multimedia/amb//tafseer/daurawa/2013/day3.mp3

4th Ramadan, 1434: http://www.dandalinsunnah.com/multimedia/amb//tafseer/daurawa/2013/day4.mp3

5th, Ramadan, 1434: http://www.dandalinsunnah.com/multimedia/amb//tafseer/daurawa/2013/day5.mp3

TAKAITACCEN BAYANI KAN SURATUL MUJADILAH KAMAR YANDA MALAM YA BAYYANA TUN A GABATARWA:

- ita ce sura ta 58 cikin Jerin surorin alQur'ani.
- ayoyinta 22
- Kalmomin da ke cikin ta 478
- tana da haruffa 1792.
- itace kadai cikin surorin AlQur'ani da ta kasance kowanne aya cikinta akwai sunan ALLAH.
- Surar tana bayanin Shashe daga cikin Hukunce-Hukuncen Shari'a kamar :-
1. Zihari
2. Ganawa (meeting)
3. Ladabin Wurin zama
4. Gabatar da sadaka kafin ganawa da Manzon Allah (S.A.W)
5. Ga wa ya kamata ka mika cikakkiyar soyayyarka.

KAR 'YAN UWA SU MANTA ANA SANYA WANNAN TAFSIRI A WADANNAN GIDAJEN RADIO DA TALABIJIN KAMAR:-
1. Freedom Radio Kano kullum da misalin karfe 2 zuwa 3 na Rana.
2. Sunnah TV karfe 10 zuwa 11 na dare.
3. DITV/RADIO KADUNA.
4. FM Radio Kano.
Ni Ma'aikacin gwabnatine. ya kasance ana bamu bashi a Ma'aikatarmu akarkashin tsarin bankuna, Amma bashin akwai kudin ruwa aciki. Ni kuma ina da larura kuma bani da kudi.
shin malam menene matsayin karban wannan bashin aguna?
zanso a sakaye sunana.

AMSA
*******
To wannan mas'alar ta bashin bankuna mai dauke da kudin ruwa, yana daga cikin manyan bala'in da suka buwayi al'umma awannan zamanin.

★ ALLAH (SWT) yana cewa:

"Allah ya halatta kasuwanci amma ya haramta ribah (kudin ruwa). Duk wanda wa'azi yazo masa daga wajen UBANGIJINSA sai ya hanu (ya dena karba ko bayarwa da kudin ruwa) to an yafe masa abinda ya wuce. kuma al'amarinsa yana wajen Allah.
Wanda kuwa ya koma (yaci gaba da yi), to wadannan sune ma'abotan WUTA (JAHANNAMA) su masu dawwama ne acikinta"

"Allah ya tsine wa kudin ruwa, amma yana ninninka (ladan) sadaka. Allah yana yin azaba ga dukanin kafiri mai mai laifuka"

"YA KU MASU IMANI kuji tsoron Allah ku guji abinda ya saura agareku na daga kudin ruwa, idan kun kasance muminai"

"Idan ba zakuyi haka ba, to SAI KUYI SHIRIN YAQI DA ALLAH DA MANZONSA....."

(Suratul baqara, aya ta 275-279)

Don haka bai kamata duk wai mumini mai Imani ya dauki wannan maganar da sasauci ba. SAI DAI IDAN KANA GANIN ZAKA IYA GWABZA YAQI DA ALLAH DA MANZON ALLAH (SAWW).

Manzon Allah (SAWW) yana cewa:

"Allah ya tsinewa mai karbar kudin ruwa da kuma mai bayarwa"
(sahihin hadisi bukhary 5962)

Sannan yace:

"Dirhami guda daya (kamar kace naira daya) wacc mutum yayi amfani da ita ta dalilin kudin ruwa, to LAIFINTA AGUN ALLAH YAFI NA WANDA YAYI ZINA SAU TALATIN DA SHIDA "

(Ahmad da baihaqee ne suka ruwaito shi kuma ALBANY ya inganta hadisin acikin sahihul jami'i, hadisi mai lamba 3375)

SANNAN MANZO (saww) yace:

"Laifin Ribah (kudin ruwa) yana da kofofi har guda 72. Amma mafi sauki daga ciki shine kamar MUTUM YAYI ZINA DA MAHAIFIYARSA"

(Tabaranee ne ya ruwaito shi acikin AL-AUSAT kuma ALBANY ya inganta hadisin acikin sahihul jami'i hadisi mai lamba 3335)

Idan muka dubi irin QAZANTAR DA TAKE CIKIN HARKAR KUDIN RUWA, TO SAI MUGA CEWAR SHI KADAI MA YA ISHEMU BALA'I AWANNAN ZAMANIN KODA ACHE BABU WANI LAIFIN DA MUKE AIKATAWA SAI WANNAN DIN.

Ku dubi yadda kullum gwamnatocin jihohinmu dana tarayya suke karbowa irin wadannan kudaden daga qasashen waje.

Ku dubi yadda manyan attajiranmu suke hulda da bankuna ta wannan sigar.

YA ALLAH KA TSAREMU.

Dangane da tsurar tambayarka kuwa, EH ZAKA IYA KARBA. AMMA SAI DAI IDAN LARURAR TAKAI YADDA BA ZAKA IYA JUREWA BA.

MISALI : Kamar ace mahaifinka ko kuma wani daga cikin family dinka bashi da lafiya, kuma bakka da kudi, kuma bakka da wanda zai baka bashi sai dai irin wadannan bankunan.

Ko kuma wata larurar makamanciyar wannan.

Amma indai abin bai kai ya kawo ba, to tabbas ZAKA HADU DA MUMMUNAN YAQI DAGA UBANGIJIN HALITTA

Ko HUKUMAR SOJOJIN NAJERIYA CE TACE ZATA GWABZA YAQI DAKAI, YAYA ZAKAJI? Ballantana ALLAH (SWT).

Daga cikin rundunar da yake turowa masu harkar kudin ruwa akwai:

TALAUCI MARAR YANKEWA HAR ZUWA TSUFA

RASHIN KWANCIYAR HANKALI

YUNWA

JINYA MARAR MAGANI

ZURIYA MARASA ALBARKA (SABODA AN CIYAR DASU DA KUDIN RUWA)

MUMMUNAR MUTUWA

HAUKA ALOKACIN DAUKAR RAI

AZABAR QABARI MAI TSANANI

MATSEWAR QABARI

WANI MA KO AN BINNESHI SAI QASAR TAKI KARBARSA

*AKWAI WADANDA GAWARSU TAKE ZAMA SIFFAR JAKI KO KARNUKA
"""""""""
Wannan dan kadan kenan. kafin ranar tashin alkiyama.

YA ALLAH KA KIYAYEM
Assalamu Alaikum, Allah gafarta malam ina hukuncin wanda yake azumi amma baya tsai da sallah?

(Daga ibrahim yola)

AMSA
*******
Ameen w/salam. Hukuncinsa shine: Ayi masa wa'azi aja hankalinsa atsoratar dashi.
Agayamasa cewar : An gina musulunci ne abisa PILLARS GUDA 5.

* KALMAR SHAHADA
* SALLAH.
* ZAKKAH.
* AZUMI.
* HAJJI.

Kuma sallah ita ce mafi girma acikin ayyukan ibada.
MANZON RAHAMA (SAWW) YANA CEWA:

"Sallah ita ce ginshikin addini. duk wanda ya tsaida ita, to hakika ya tsaida addini. wanda duk ya rusheta, to hakika ya rushe addini."

Kua ita ce farkon abinda za;a fara yiwa mutum hisabi akai. idan tayi kyau to shikenan mutum ya haye. idan ba tayi kyau ba to lallai mutum yayi hasara.

Don haka wannan azumin ba zai yi masa cikakken amfani ba sai da sallah.

Muna yi masa addu'ar ALLAH ya shiryar dashi damu baki daya.

WALLAHU A'ALAM
Malam shin idan aka bawa mutum yarinya, har aka sa ranar aurensu, YA HALATTA YA RIKA TATTABA JIKINTA??

(Daga Aliyu Garba Auchan)

AMSA
*******
Tun kwanakin baya mun amsa irin wannan tambayar tare da hujjoji daga manyan littattafai da fatawoyin manyan maluma cewar BAI HALATTA BA. BAI HALATTA BA!!! BAI HALATTA BA!!!

Maluman da suke halatta irin wannan, ya kamata suji tsoron Allah, su sani cewar irin wannan gurguwar fatawar tana Qara taimakawa wajen rusa tarbiyar al'ummah.

Mace batta halatta ga namiji sai bayan an daura musu aure. SADAKI daya ne kawai daga cikin rukunan daurin auren don ka biya sadaki yarinyar batta halatta agareka ba sai bayan anyi siga tsakanin waliyyanka da nata, sannan afadi yawan sadakin da biya naqdan ko ajalan, sannan Shaidu *adalai* (AQALLA MUTUM BIYU KO SAMA DA HAKA) SU SHAIDA CEWAR WALIYYANTA SUN AURAR MAKA DA ITA.

Daga nan ma idan kaga dama kaje ka kama hannunta. ta riga ta zama matarka.

Don Allah samari da yanmata akiyaye. '

WALLAHU A'ALAM.
Malam mace ce taga jini jini a pant dinta kuma tana axumi, amma jini b kamar yadda ta keyi idan tana haila ba. Wannan yayi fari fari bashi da duhu. Kenan axuminta ya karye?
Dan Allah malam a buye sunana. Kuma a taimakamin da addu,a ina yawan mafarkin mace yar uwata tana saduwa dani.
da chan ban dauka a komai b sai danaga posting dinku cewa aljannu na shafar mutum. Ke nan malm aljana ce ta shafeni ko ko yaya?

AMSA
*******
Idan matar da take AZUMI taga wani jini ya digo daga farjinta, to hakika wannan Azumin nata ya karye.Kuma zata ramashi.

Shi jinin haila bashi da iyakacin karancin lokaci abisa mazhabin Imamu Malik (rta). Zai iya zuwa nan take, sannan ya dauke nan take.

Dangane da Kalarsa kuwa, eh yakan chanza kala awasu lokutan. Musamman ma idan an samu wani chanjin yanayin lafiyar jikin. Ko kuma chanjin abinci, ko kuma yawaitar shekaru. (YA DANGANTA DA HALITTAR JIKIN ITA MAI HAILAN)

***AMSAR TAMBAYARKI TA BIYU:
EH Zata iya yuwuwa wata Aljana ko kuma aljani ya shafeki. musamman ma idan kina jin sauran manyan alamomin kamarsu FADUWAR GABA, CIWON KAI, FIRGITA, YAWAN BACIN RAI BABU DALILI, QAIKAYIN GABA, etc.

*Awasu lokutan ALJANI NAMIJI zai iya zuwa miki da siffar mace yana saduwa dake. ko kuma yazo miki da siffar mijinki ko saurayinki...

wani lokacin kuma yazo miki da siffar wani mutum wanda kike jin kunya, etc.

Kuma shima aljanin zai iya haddasa miki RIKICIN JININ AL'ADA.

Ki koma ki duba shawarwarin da muka bayar awadancan postings din domin samun bayanai na taimakon gaggawa.

WALLAHU A'ALAM

DA FATAN ALLAH YA BAKI LAFIYA DAKE DA DUKKAN MASU FAMA DA IRIN WANNAN MATSALAR.
'Yan uwa ku taimaketa da addu'a
Assalamu alaikum.
Malam tambayana shine, shin menene hukuncin
mutumin da ba musulmiba yana/tana Azimi kuma yana/tana sha'awar musulunchi amma saboda wasu dalillai kamar iyaye don tsoron kar su yifushi da shi/
ita bai ba shi/ta damar musulunta ba. Amma yana/tana boye azumin?

Don Allah malam ina neman fatawa akan wannan babbar lamari. Wassalamu alaikum.
JazakAllahu khairan.

(daga Kabiru Bashir)

AMSA
******
To shi Musulunci addini ne wanda aka ginashi abisa GINSHIKAI guda biyar. Amma mafi muhimmanci daga cikin guda biyar dinnan shine KALMAR SHAHADA.

Ita ce kalmar imani kuma da ita ake shiga musulunci.
Don haka duk wasu ayyukan da mutum zai aikata ba zasu amfaneshi awajen Allah ba, mutukar dai bai riga ya furta KALMAR SHAHADA BA.

Don haka abunda yafi ga wannan baiwar ALLAH ko bawan Allah shine SHIGOWA MUSULUNCI kai tsaye ba tare da tsoron kowa ba.

Akwai wani SAHABIN MANZON ALLAH (SAWW) wanda mahaifiyarsa tayi fushi dashi saboda shigarsa cikin musulunci harma ta dena cin abinci.
Wai ba zata ci abinci ba sai ya fita daga Musulunci.
Shi kuwa sai yace mata "ya ke mahaifiya ta! da ache kina da rayuka har guda dubu, ko duk zasu Qare ba zan fita daga addinin Allah ba.

Shi kuwa Sayyiduna ABDULLAHI BN RAWAHA (rta) mahaifinsa babban mai kudi ne. amma sai da ya koreshi saboda shigarsa musulunci ya kwace duk dukiyarsa. Amma duk wannan bai sa sun fasa ba.

Don haka tsoron fushinsu ba hujjah bane agareshi.
TO IDAN KUMA YA MUTU FA TUN KAFIN YA SHIGA MUSULUNCIN??? shin wannan tsoron iyayen zai zama masa hujja awajn Allah?

BABU BIYAYYA GA WANI MAHALUKI ACIKIN SA'BAWA MAHALICCI.

WALLAHU A'ALAM