Assalamu alaikum.
Malam tambayana shine, shin menene hukuncin
mutumin da ba musulmiba yana/tana Azimi kuma yana/tana sha'awar
musulunchi amma saboda wasu dalillai kamar iyaye don tsoron kar su
yifushi da shi/
ita bai ba shi/ta damar musulunta ba. Amma yana/tana boye azumin?
Don Allah malam ina neman fatawa akan wannan babbar lamari. Wassalamu alaikum.
JazakAllahu khairan.
(daga Kabiru Bashir)
AMSA
******
To shi Musulunci addini ne wanda aka ginashi abisa GINSHIKAI guda
biyar. Amma mafi muhimmanci daga cikin guda biyar dinnan shine KALMAR
SHAHADA.
Ita ce kalmar imani kuma da ita ake shiga musulunci.
Don haka duk wasu ayyukan da mutum zai aikata ba zasu amfaneshi awajen
Allah ba, mutukar dai bai riga ya furta KALMAR SHAHADA BA.
Don haka abunda yafi ga wannan baiwar ALLAH ko bawan Allah shine SHIGOWA MUSULUNCI kai tsaye ba tare da tsoron kowa ba.
Akwai wani SAHABIN MANZON ALLAH (SAWW) wanda mahaifiyarsa tayi fushi
dashi saboda shigarsa cikin musulunci harma ta dena cin abinci.
Wai ba zata ci abinci ba sai ya fita daga Musulunci.
Shi kuwa sai yace mata "ya ke mahaifiya ta! da ache kina da rayuka har
guda dubu, ko duk zasu Qare ba zan fita daga addinin Allah ba.
Shi kuwa Sayyiduna ABDULLAHI BN RAWAHA (rta) mahaifinsa babban mai kudi
ne. amma sai da ya koreshi saboda shigarsa musulunci ya kwace duk
dukiyarsa. Amma duk wannan bai sa sun fasa ba.
Don haka tsoron fushinsu ba hujjah bane agareshi.
TO IDAN KUMA YA MUTU FA TUN KAFIN YA SHIGA MUSULUNCIN??? shin wannan tsoron iyayen zai zama masa hujja awajn Allah?
BABU BIYAYYA GA WANI MAHALUKI ACIKIN SA'BAWA MAHALICCI.
WALLAHU A'ALAM
No comments:
Post a Comment