Malam shin idan aka bawa mutum yarinya, har aka sa ranar aurensu, YA HALATTA YA RIKA TATTABA JIKINTA??
(Daga Aliyu Garba Auchan)
AMSA
*******
Tun kwanakin baya mun amsa irin wannan tambayar tare da hujjoji daga
manyan littattafai da fatawoyin manyan maluma cewar BAI HALATTA BA. BAI
HALATTA BA!!! BAI HALATTA BA!!!
Maluman da suke halatta irin wannan, ya kamata suji tsoron Allah, su
sani cewar irin wannan gurguwar fatawar tana Qara taimakawa wajen rusa
tarbiyar al'ummah.
Mace batta halatta ga namiji sai bayan an
daura musu aure. SADAKI daya ne kawai daga cikin rukunan daurin auren
don ka biya sadaki yarinyar batta halatta agareka ba sai bayan anyi siga
tsakanin waliyyanka da nata, sannan afadi yawan sadakin da biya naqdan
ko ajalan, sannan Shaidu *adalai* (AQALLA MUTUM BIYU KO SAMA DA HAKA) SU
SHAIDA CEWAR WALIYYANTA SUN AURAR MAKA DA ITA.
Daga nan ma idan kaga dama kaje ka kama hannunta. ta riga ta zama matarka.
Don Allah samari da yanmata akiyaye. '
WALLAHU A'ALAM.
No comments:
Post a Comment