Malam
mace ce taga jini jini a pant dinta kuma tana axumi, amma jini b kamar
yadda ta keyi idan tana haila ba. Wannan yayi fari fari bashi da duhu.
Kenan axuminta ya karye?
Dan Allah malam a buye sunana. Kuma a taimakamin da addu,a ina yawan mafarkin mace yar uwata tana saduwa dani.
da chan ban dauka a komai b sai danaga posting dinku cewa aljannu na shafar mutum. Ke nan malm aljana ce ta shafeni ko ko yaya?
AMSA
*******
Idan matar da take AZUMI taga wani jini ya digo daga farjinta, to hakika wannan Azumin nata ya karye.Kuma zata ramashi.
Shi jinin haila bashi da iyakacin karancin lokaci abisa mazhabin Imamu
Malik (rta). Zai iya zuwa nan take, sannan ya dauke nan take.
Dangane da Kalarsa kuwa, eh yakan chanza kala awasu lokutan. Musamman ma
idan an samu wani chanjin yanayin lafiyar jikin. Ko kuma chanjin
abinci, ko kuma yawaitar shekaru. (YA DANGANTA DA HALITTAR JIKIN ITA
MAI HAILAN)
***AMSAR TAMBAYARKI TA BIYU:
EH Zata iya yuwuwa
wata Aljana ko kuma aljani ya shafeki. musamman ma idan kina jin sauran
manyan alamomin kamarsu FADUWAR GABA, CIWON KAI, FIRGITA, YAWAN BACIN
RAI BABU DALILI, QAIKAYIN GABA, etc.
*Awasu lokutan ALJANI
NAMIJI zai iya zuwa miki da siffar mace yana saduwa dake. ko kuma yazo
miki da siffar mijinki ko saurayinki...
wani lokacin kuma yazo miki da siffar wani mutum wanda kike jin kunya, etc.
Kuma shima aljanin zai iya haddasa miki RIKICIN JININ AL'ADA.
Ki koma ki duba shawarwarin da muka bayar awadancan postings din domin samun bayanai na taimakon gaggawa.
WALLAHU A'ALAM
DA FATAN ALLAH YA BAKI LAFIYA DAKE DA DUKKAN MASU FAMA DA IRIN WANNAN MATSALAR.
'Yan uwa ku taimaketa da addu'a
No comments:
Post a Comment