DAFATAN ANSHA RUWA LAFIYA,MALAM IDAN
MATAFIYI YANA KASARU IDAN YA GA DAHALIN BIN JAM'I WATO RAKA'A [4] ZAI IYA BI ?
(DAGA SHEHU MUH'D)
AMSA
*******
Eh zai iya bi. Amma kuma mafi alkhairi gareshi shine ya tsaya akan
sunnarsa (wato raka'a biyu) zai yi ko shine yake limanci ko kuma bi yake
yi.
Imam ABU ZAYD ALQAIRAWANY (rah) yana cewa:
"IDAN MATAFIYI YABI MAI ZAMAN GIDA A SALLAH, KO KUMA SHI MAI ZAMAN GIDAN YABI MATAFIYI, TO KOWANNE ZAI TSAYA NE AKAN SUNNARSA"
Wato mazaunin gida zai cika sallarsa, shi kuma matafiyi zai yi kasarunsa.
Sannan kuma yana da za'bi biyu anan.
1. Ko dai yayi sallamarsa da zarar anyi raka'a biyu.
2. Ko kuma idan anyi raka'a biyu sai yaci gaba da zama a inda yake, har
Limaminsa ya ciko raka'a biyunsa, sannan idan limaminsa yayi sallama,
shima sai yayi tasa.
Irin abinda wasu suke yi idan sunyi tafiyar data dace suyi Qasaru, sai suki yi wai AI SU BASU DAUKO TA TUN DAGA GIDA BA.
Wannan kuskure ne. ai ita Qasaru ba daukota akeyi ba. a'a sauki ne
wanda Allah yayiwa bayinsa. kuma ALLAH yana so idan yayiwa bayinsa
sauki, to su yi amfani da wannan saukin.
Amma cika sallah
ayayin tafiyar da takai ayi mata Qasaru, wannan bai dace da sunnah
ba.Sai dai idan mutum yana da niyyar zama achan garin fiye da kwana 4,
(salloli 20) to anan malamai masanan fiqhu irinsu Imamu Malik da Imamush
Shafi'iy sunce zai cika sallarsa ne.
WALLAHU A'ALAM.
No comments:
Post a Comment