Ni
Ma'aikacin gwabnatine. ya kasance ana bamu bashi a Ma'aikatarmu
akarkashin tsarin bankuna, Amma bashin akwai kudin ruwa aciki. Ni kuma
ina da larura kuma bani da kudi.
shin malam menene matsayin karban wannan bashin aguna?
zanso a sakaye sunana.
AMSA
*******
To wannan mas'alar ta bashin bankuna mai dauke da kudin ruwa, yana daga cikin manyan bala'in da suka buwayi al'umma awannan zamanin.
★ ALLAH (SWT) yana cewa:
"Allah ya halatta kasuwanci amma ya haramta ribah (kudin ruwa). Duk
wanda wa'azi yazo masa daga wajen UBANGIJINSA sai ya hanu (ya dena karba
ko bayarwa da kudin ruwa) to an yafe masa abinda ya wuce. kuma
al'amarinsa yana wajen Allah.
Wanda kuwa ya koma (yaci gaba da yi), to wadannan sune ma'abotan WUTA (JAHANNAMA) su masu dawwama ne acikinta"
"Allah ya tsine wa kudin ruwa, amma yana ninninka (ladan) sadaka. Allah yana yin azaba ga dukanin kafiri mai mai laifuka"
"YA KU MASU IMANI kuji tsoron Allah ku guji abinda ya saura agareku na daga kudin ruwa, idan kun kasance muminai"
"Idan ba zakuyi haka ba, to SAI KUYI SHIRIN YAQI DA ALLAH DA MANZONSA....."
(Suratul baqara, aya ta 275-279)
Don haka bai kamata duk wai mumini mai Imani ya dauki wannan maganar da
sasauci ba. SAI DAI IDAN KANA GANIN ZAKA IYA GWABZA YAQI DA ALLAH DA
MANZON ALLAH (SAWW).
Manzon Allah (SAWW) yana cewa:
"Allah ya tsinewa mai karbar kudin ruwa da kuma mai bayarwa"
(sahihin hadisi bukhary 5962)
Sannan yace:
"Dirhami guda daya (kamar kace naira daya) wacc mutum yayi amfani da
ita ta dalilin kudin ruwa, to LAIFINTA AGUN ALLAH YAFI NA WANDA YAYI
ZINA SAU TALATIN DA SHIDA "
(Ahmad da baihaqee ne suka ruwaito shi kuma ALBANY ya inganta hadisin acikin sahihul jami'i, hadisi mai lamba 3375)
SANNAN MANZO (saww) yace:
"Laifin Ribah (kudin ruwa) yana da kofofi har guda 72. Amma mafi sauki daga ciki shine kamar MUTUM YAYI ZINA DA MAHAIFIYARSA"
(Tabaranee ne ya ruwaito shi acikin AL-AUSAT kuma ALBANY ya inganta hadisin acikin sahihul jami'i hadisi mai lamba 3335)
Idan muka dubi irin QAZANTAR DA TAKE CIKIN HARKAR KUDIN RUWA, TO SAI
MUGA CEWAR SHI KADAI MA YA ISHEMU BALA'I AWANNAN ZAMANIN KODA ACHE BABU
WANI LAIFIN DA MUKE AIKATAWA SAI WANNAN DIN.
Ku dubi yadda kullum gwamnatocin jihohinmu dana tarayya suke karbowa irin wadannan kudaden daga qasashen waje.
Ku dubi yadda manyan attajiranmu suke hulda da bankuna ta wannan sigar.
YA ALLAH KA TSAREMU.
Dangane da tsurar tambayarka kuwa, EH ZAKA IYA KARBA. AMMA SAI DAI IDAN LARURAR TAKAI YADDA BA ZAKA IYA JUREWA BA.
MISALI : Kamar ace mahaifinka ko kuma wani daga cikin family dinka
bashi da lafiya, kuma bakka da kudi, kuma bakka da wanda zai baka bashi
sai dai irin wadannan bankunan.
Ko kuma wata larurar makamanciyar wannan.
Amma indai abin bai kai ya kawo ba, to tabbas ZAKA HADU DA MUMMUNAN YAQI DAGA UBANGIJIN HALITTA
Ko HUKUMAR SOJOJIN NAJERIYA CE TACE ZATA GWABZA YAQI DAKAI, YAYA ZAKAJI? Ballantana ALLAH (SWT).
Daga cikin rundunar da yake turowa masu harkar kudin ruwa akwai:
TALAUCI MARAR YANKEWA HAR ZUWA TSUFA
RASHIN KWANCIYAR HANKALI
YUNWA
JINYA MARAR MAGANI
ZURIYA MARASA ALBARKA (SABODA AN CIYAR DASU DA KUDIN RUWA)
MUMMUNAR MUTUWA
HAUKA ALOKACIN DAUKAR RAI
AZABAR QABARI MAI TSANANI
MATSEWAR QABARI
WANI MA KO AN BINNESHI SAI QASAR TAKI KARBARSA
*AKWAI WADANDA GAWARSU TAKE ZAMA SIFFAR JAKI KO KARNUKA
"""""""""
Wannan dan kadan kenan. kafin ranar tashin alkiyama.
YA ALLAH KA KIYAYEM
No comments:
Post a Comment