Wai
 shin tsakanin shafa kafa da wanke kafa wannene Farilla a alwala? Shin 
da gaske ne cewa ayar alkur’ani da shafa ta sauka?? Shin da gaske ne 
cewa Manzon Allah (S) shafa kafarsa ya yi a alwala ba wankewa ba??? 
 Darasin da na ke sa ran fara kawowa kenan da yardan Allah! Kuma da 
hujjoji gamsassu ga duk wanda yake son ya gamsu In sha Allah! Fatana 
shine Allah ya nuna mana gaskya gaskiya ce ya bamu ikon binta ya nuna 
mana karya, karya ce ya bamu ikon nisantar ta. Domin tabbas ba fahimtar 
gaskiya bane mai wuya ba, a’a danne zuciya ta dawo ta bi wannan gaskiyan
 shine mai wuya. Sau tari mutum zai fahimci gaskiya har cikin zuciyarsa 
amma zuciyarsa sai ta hana shi bin ita gaskiyar duk da ya san gaskiya 
ne! Ya Allah ka sa mu fi karfin zuciyoyinmu. Ina kuma baran addu’a ga 
yan uwa musamman masu azumi a cikin wannan watan mai daraja da su sa 
mahaifiyata marigayiya Hajiya A’ishatu Atiku a cikin addu’oin su. Na 
gode
 
 
 
          
      
 
  
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
No comments:
Post a Comment