Monday, 17 June 2013

Wai shin tsakanin shafa kafa da wanke kafa wannene Farilla a alwala? Shin da gaske ne cewa ayar alkur’ani da shafa ta sauka?? Shin da gaske ne cewa Manzon Allah (S) shafa kafarsa ya yi a alwala ba wankewa ba???
Darasin da na ke sa ran fara kawowa kenan da yardan Allah! Kuma da hujjoji gamsassu ga duk wanda yake son ya gamsu In sha Allah! Fatana shine Allah ya nuna mana gaskya gaskiya ce ya bamu ikon binta ya nuna mana karya, karya ce ya bamu ikon nisantar ta. Domin tabbas ba fahimtar gaskiya bane mai wuya ba, a’a danne zuciya ta dawo ta bi wannan gaskiyan shine mai wuya. Sau tari mutum zai fahimci gaskiya har cikin zuciyarsa amma zuciyarsa sai ta hana shi bin ita gaskiyar duk da ya san gaskiya ne! Ya Allah ka sa mu fi karfin zuciyoyinmu. Ina kuma baran addu’a ga yan uwa musamman masu azumi a cikin wannan watan mai daraja da su sa mahaifiyata marigayiya Hajiya A’ishatu Atiku a cikin addu’oin su. Na gode

ATA MASU GOYO DA MASU LAULAYIN CIKIN SUNA IYA AJIYE AZIMIN RAMADANA?

AMSA:

Game da wannan tambayar akwai maganganun malamai guda uku. Akwai daga cikin malamai masu cewa. Ta ajiye aziminta, amma kuma ta ciyar, sannan kuma ta rama wannan azimin a bayan sallah. Wannan shine fahimtar wasu malamai kamar shekh takiyyuddin da Turmizi. Su kuma mutanen mazhabar malikiyya da ta Hanafiyya cewa sukayi: Mata masu ciki da masu shayarwa ba su ciyarwa saboda sun sha azimi, sai dai kawai bayan sallah sai su rama azimin da ba suyi ba, saboda wannan larurar kawai. Su kuma mutanen mazhabar imamu shafi’i da Ahmad bini Hambali sunce mata masu ciki da masu shayarwa hukuncin su ]aya dana tsohon da ba ya iya yin azimi saboda tsufa. Don haka sai suka ce mace mai ciki ko mai shayarwa idan har tana tsoron kada wani abu ya sami ]an da ke cikin cikinta, ko kuma jaririn ta wanda take shayarwa, ko kuma ita kanta. To tana iya ajiye azimin Ramadana. Sai ta dinga ciyarwa kullum a maimakon azimin ta, sannan kuma bayan sallah ba za ta rama ba. Kuma ciyarwar da za tayi shi ne, taba miskini abincin da zai ci ya koshi sau daya kawai a cikin ko wane yini daya. Kullum idan tayi hakan, to kamar tayi azumi daya kenan. Wannan shine abin da muka sani Allah shi ne mafi sani.
Akramakallah idan namiji ya ba matarsa takardar saki, taki karba sai ya yaga takardar.

sakin yayi kuwa?

Tambaya ta 2:
Idan mutun sukayi fada da matarsa ransa yabaci ya dauko biro da takarda yafara
rubuta mata saki sai wani ya kwace
takardar ya yaga.saki yatabbata anan kokuwa?.

(daga Bashir Zamfara).

AMSA
*****
TAMBAYAR FARKO: eeh sakin ya yuwu. Domin kuwa ikon yiwuwar sakin ba'a hannun matar yake ba.. Ahannun mijin ne. Tunda yace ya saketa ko ta yarda ko bata yarda ba ta saku..

Ko ta karbi takardar ko bata karba ba ta saku. In dai yace mata ga takarda na sake ki shikenan.

Wallahu a'alam.

TAMBAYARKA TA BIYU: Malamai sunce duk lokacin da mutum ya rubuta takardar saki kuma aka samu koda mutum daya ya shaidar da hakan, to saki ya yiwu babu damar janyewa.

Don haka In dai har ya riga ya rubuta kalmar saki acikin takardar, kuma shi wannan mutumin ya karanta kafin ya yaga, shikenan sakin yayiwu.

Amma idan ya dauko kenan ya fara rubuta Kwanan wata (date) kenan sai wannan mutumin ya karbe ya yaga, (Tun bai rubuta kalamar saki acikin takardar ba) to shikenan BATA SAKU BA. Aurensu yana nan..

Irin abin nan da iyaye suke yi wani lokacin idan Dansu ya saki matarsa, sai suje gun matar su karbe takardar su yaga, suce mata yi zamanki, wannan ma bai kamata adauki cewar wannan sakin bai yiwu ba. Saki ya yiwu.. In dai wannan 'Dan nasu ya balaga, kuma yana da hankali ba mahaukaci bane..

Wallahu a'alam.
Salamu alaikum malam, Nakasance nabi wani mutum sallar azahar, Araka'ar farko sai ya zauna sai nace "SUB-HANALLAH!!!"

Sai ya mike muka kawo ta 2 mukayi
tahiyaH, muka karo 2 mukayi sallama.

To malam sai ya mike yatafi baiyi sujadar rafkanuwa ba.

To malam yaya sallah ta?

(daga Aminu Shehu).

AMSA
====
Malam Aminu sallarka tayi. Domin kuwa dukkanin Imamai na Mazhabobon nan hudu sunyi ittifaki akan cewa Duk wanda ya manche sujjadar rafkanuwa bai yita ba, to Sallarsa tayi.

Amma awajen Imamu Malik in dai ba'adiy ce zai rama ta koda bayan shekara guda ne.
Saboda haka kaima sujjadah Ba'adin zakayi domin kuwa ita ce ta kamaku acikin wannan rafkanuwar da ku kayi..

Wannan zaman da ku kayi, sannan ku ka dawo kuka mike, ya zamanto kamar kunyi Qari ne asallar.

Duk wanda yayi Qari asallah, sujjadah ba'ady zai yi.

WALLAHU A'ALAM.
Assalamu alaikum. malam, shin mutumin da yake da mata hudu Idan ya saki daya daga cikinsu, zai iya kara aure kafin tayi iddah?

(daga Musnah Majadun).

AMSA
====
Idan namiji ya saki matarsa tana cikin iddah, duk da haka akwai sauran alaqah atsakaninsu wacce addini ya shimfida.

Saboda wannan ne ma yasa zata iya gadonsa idan ya rasu kafin ta gama iddarta.

Sai dai idan saki uku yayi mata, ko kuma irin rabuwar nan wacce babu damar mayar da auren.

Abisa wannan dalilin ne Malamai Fuqaha'u suka ce: Idan namiji mai Mata hudu ya rabu da wata daga cikinsu, mutukar ba saki uku yayi mata ba, to babu damar ya cike gurbinta har sai ta gama idda..

WALLAHU A'ALAM.,

BALA'IN DA YAKE CIKIN ZINA !!
Don Allah menene hukuncin SAURAYIN da yana neman yarinya da
aure amma sai shedan ya rudesu suka nemi junansu (sukayi zina).

Sannan sukayi aure daga baya. yaya hukuncin auren su ayanzu.

(daga mohd Auwal)

AMSA
====
Aurensu yayi, Kuma sun dace da Juna tunda dukkansu mazinata ne.

Allah (swt) yana cewa:

"Mazinaci ba zai aura ba sai Mazinaciya ko Mushrika, Hakanan Mazinaciya ma ba zata aura ba sai Mazinaci ko mushriki".

Sannan yace:

"Mataye Qazamai (masu dau'dar zina) sun dace ne da Mazaje Qazamai (masu dau'dar zina)..

Don haka wadannan ma'auratan sun daukowa kansu babban Bala'in da sai ya shafi dukkan zurriyyarsu idan basu tuba ba.

Imamus Suyuti ya kawo Wani hadisi acikin littafinsa TANQEEHUL-QAULIL HATHEETH" daga Anas bn Malik (ra).

Manzon Allah (saww) yana cewa: "Duk wanda yayi zina sai anyi da (wanin)shi".

Ma'ana sai anyi zina da 'yarsa ko da uwarsa ko da Qanwarsa ko da yayarsa, ko da Qanwar Mahaifinsa ko Qanwar mahaifiyarsa. (Wal-iyazu billah).

Sannan Annabi (saww) yace:

"Duk wanda yayi zina da wata mace, za'a bude masa Kofofin wuta guda takwas acikin Qabarinsa, Akwai Kunami da macizai da zasu rika shigowa cikin Qabarin nasa ta cikin wadannan kofofin har izuwa ranar Alkiyamah".

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN.

Insha Allahu nan gaba zamuyi posting na musamman akan Bala'in da suke cikin zina.

Wallahu a'alam.

Salam alaikum malam idan mutum kaga dan uwanka ya fara alamun ya shiga shi'a kuma daga baya ka tabbatar cewa hakanne yaya xakayi dashi?Allah ya taimaki malam ya biya masa bukatunsa na alkhairi.

(Daga wani bawan Allah.).

AMSA
====
Abinda ya wajabta agareka shine ka nuna masa gaskiya.

Ka gaya masa cewa Kaunar Sahabbai wajibi ne. Kuma yana daga cikin alamomin imani.

Kuma Mutum baya cika Masoyin Annabi da Ahlul-Baiti har sai yaso Sahabbai gaba dayansu.

Kuma ka gaya masa zagin Sahabbai fasikanci ne. Wasu Maluman ma sun ce Kafurci ne.

Kuma ka gaya masa cewa Alkur'ani dai guda daya ne. Kuma ya cika. Babu wani abinda ya saura.

Don haka ya guji afkawa cikin mummunar Akidar nan ta Shi'a.

Allah ya karemu. Allah ya Qara mana shiriya abisa tafarkin Manzon Tsira (saww).
ssalamu Alaikum! Malam shin ya halaTta a cikin tahiyar farko mutum ya karanta salatin Annabi (saww) ko kuwa sai a tahiya ta biyu,daganan sai addua da sallama.Allah yasaka da alkhairi. (daga Maharazu Ali)

AMSA
====
Idan mutum yayi haka, sallarsa tayi kuma bai aikata laifi ba asallarsa. Domin Salatin Annabi (saww) abu ne mai kyau. Kuma ibada ce tsarkakakkiya.

Amma yadda yazo aSunnah, ana Karanta Salatin Annabi (saww) ne alokacin zaman tahiya na biyu..

Malamai sun bada muhimmanci sosai akan wannan. Domin kuwa akwai wadanda suke ganin cewar FARILLAH ne daga cikin farillan sallah. Idan mutum ya qi yin Salatin da gangan to bashi da Sallah. (Wannan shine ra'ayin Imamush-Shafi'iy).

WALLAHU A'ALAM.
Assalamu Alaikum mallam mainene
hukuncin wanda yake yawan mantuwa acikin sallah?

(Daga Rahmatu Ladidi).

AMSA
*****
Wanda yake yawan yin mantuwa ko kokwanto acikin Sallarsa, harma abin ya zame masa jiki, to anan Malamai suka ce "DUK WANDA KOKWANTO YA AURESHI, ZAI RIKA YIN SUJJADAH BA'ADI NE.

Kamar yadda Shaykh Abdurrahman Al'akhdhary ya fada acikin littafinsa.

Amma idan kuma ba ko yaushe yake yin mantuwar ba, ko kuma kokwanton bai riga ya aureshi ba, To anan sai ya duba ya gani:

idan ya manche Farillah, to wajibi ne sai ya kawota, sannan yayi Sujjada ba'ady.

Idan kuma ya manche Sunnoni guda biyu ko fiye da haka, to zai yi sujjadah Qably ne. (Kamar wanda ya manche zaman tahiyar farko, ko kuma ya manta fadar Sami'allahu liman-hamidahu sau 2, ko fiye da haka, ko kuma ya manche kabbarori guda biyu ko fiye da haka (amma banda kabbarar harama). Ko kuma wanda ya manche karatun sura bayan fatiha, To wadannan dukka sujjada Qabaliy zaki yi.

Sannan akwai abubuwan (Mustahabbai) wadanda ba'ayin Sujjada Qabali ko Ba'ady saboda su, misali:

Alqunut, Kabbara sau daya, Sami'allahu liman -hamidah sau 1, tasbeehi acikin ruku'u, sau daya. Addu'ar cikin Sujjada, Fa'dar Aameen bayan fatiha,

wadannan duk ba'ayi musu sujjada Qabli ko ba'adi. Duk wanda yayi musu kuma, to sallarsa ta baci.

WALLAHU A'ALAM.,
Allah shi gafarta mallam, tambayata
anan itace, Uba da Dansa da Jikansa ne, tafiya ta hadasu sai suka hadu da hatsari
misali hatsarin mota, gobara ko kuma ache, kolekole ta kife dasu a ruwa. kuma
babu kowa a wurin balle ashaida, wanda ya riga mutuwa. To idan
akasamu labarin rasuwarsu, tayaya za'a raba gado tsakaninsu??

(Abubakar Ja'afaru Yerima, Daga: Jalingo Jihar Taraba, Nigeria.).

AMSA
*****
Kwanakin baya ma mun amsa irin wannan tambayar.

Hukuncin shine: BABU GADO ATSAKANINSU.. Babu wanda zai gaji wani.

Amma kowannensu za'a rabawa Iyalansa gadon dukiyar da ya bari..

WALLAHU A'ALAM.
MAFI ALHERI CIKIN LAMURA SHI NE KARSHE MAI KYAU

Ya Allah Ubangijinmu! Muna rokon Ka kamar yadda muke kan Sunnar Annabinka mai tsira da amincin Allah a yanzu, muke kuma kaunar Sunnar, muke kuma fifita maganar AnnabinKa a kan maganar ko wane mutum a nan duniya, muke gwagwarmayar yada wannan manufa a cikin al'ummarmu, Ya Allah Ubangijin Sammai da Kassai Ka kara tausaya mana Ka dauki rayukanmu a kan wannan Sunnah ta Annabi Muhammad mai tsira da amincin Allah. Ameen.