Assalamu alaikum. malam, shin mutumin da yake da mata hudu Idan ya saki daya daga cikinsu, zai iya kara aure kafin tayi iddah?
(daga Musnah Majadun).
AMSA
====
Idan namiji ya saki matarsa tana cikin iddah, duk da haka akwai sauran alaqah atsakaninsu wacce addini ya shimfida.
Saboda wannan ne ma yasa zata iya gadonsa idan ya rasu kafin ta gama iddarta.
Sai dai idan saki uku yayi mata, ko kuma irin rabuwar nan wacce babu damar mayar da auren.
Abisa wannan dalilin ne Malamai Fuqaha'u suka ce: Idan namiji mai Mata
hudu ya rabu da wata daga cikinsu, mutukar ba saki uku yayi mata ba, to
babu damar ya cike gurbinta har sai ta gama idda..
WALLAHU A'ALAM.,
No comments:
Post a Comment