Monday, 17 June 2013

Assalamu Alaikum mallam mainene
hukuncin wanda yake yawan mantuwa acikin sallah?

(Daga Rahmatu Ladidi).

AMSA
*****
Wanda yake yawan yin mantuwa ko kokwanto acikin Sallarsa, harma abin ya zame masa jiki, to anan Malamai suka ce "DUK WANDA KOKWANTO YA AURESHI, ZAI RIKA YIN SUJJADAH BA'ADI NE.

Kamar yadda Shaykh Abdurrahman Al'akhdhary ya fada acikin littafinsa.

Amma idan kuma ba ko yaushe yake yin mantuwar ba, ko kuma kokwanton bai riga ya aureshi ba, To anan sai ya duba ya gani:

idan ya manche Farillah, to wajibi ne sai ya kawota, sannan yayi Sujjada ba'ady.

Idan kuma ya manche Sunnoni guda biyu ko fiye da haka, to zai yi sujjadah Qably ne. (Kamar wanda ya manche zaman tahiyar farko, ko kuma ya manta fadar Sami'allahu liman-hamidahu sau 2, ko fiye da haka, ko kuma ya manche kabbarori guda biyu ko fiye da haka (amma banda kabbarar harama). Ko kuma wanda ya manche karatun sura bayan fatiha, To wadannan dukka sujjada Qabaliy zaki yi.

Sannan akwai abubuwan (Mustahabbai) wadanda ba'ayin Sujjada Qabali ko Ba'ady saboda su, misali:

Alqunut, Kabbara sau daya, Sami'allahu liman -hamidah sau 1, tasbeehi acikin ruku'u, sau daya. Addu'ar cikin Sujjada, Fa'dar Aameen bayan fatiha,

wadannan duk ba'ayi musu sujjada Qabli ko ba'adi. Duk wanda yayi musu kuma, to sallarsa ta baci.

WALLAHU A'ALAM.,

No comments: