ATA MASU GOYO DA MASU LAULAYIN CIKIN SUNA IYA AJIYE AZIMIN RAMADANA?
AMSA:
Game da wannan tambayar akwai maganganun malamai guda uku. Akwai daga
cikin malamai masu cewa. Ta ajiye aziminta, amma kuma ta ciyar, sannan
kuma ta rama wannan azimin a bayan sallah. Wannan shine fahimtar wasu
malamai kamar shekh takiyyuddin da Turmizi. Su kuma mutanen mazhabar
malikiyya da ta Hanafiyya cewa sukayi: Mata masu ciki da masu shayarwa
ba su ciyarwa saboda sun sha azimi, sai dai kawai bayan sallah sai su
rama azimin da ba suyi ba, saboda wannan larurar kawai. Su kuma mutanen
mazhabar imamu shafi’i da Ahmad bini Hambali sunce mata masu ciki da
masu shayarwa hukuncin su ]aya dana tsohon da ba ya iya yin azimi saboda
tsufa. Don haka sai suka ce mace mai ciki ko mai shayarwa idan har tana
tsoron kada wani abu ya sami ]an da ke cikin cikinta, ko kuma jaririn
ta wanda take shayarwa, ko kuma ita kanta. To tana iya ajiye azimin
Ramadana. Sai ta dinga ciyarwa kullum a maimakon azimin ta, sannan kuma
bayan sallah ba za ta rama ba. Kuma ciyarwar da za tayi shi ne, taba
miskini abincin da zai ci ya koshi sau daya kawai a cikin ko wane yini
daya. Kullum idan tayi hakan, to kamar tayi azumi daya kenan. Wannan
shine abin da muka sani Allah shi ne mafi sani.
No comments:
Post a Comment