ssalamu
Alaikum! Malam shin ya halaTta a cikin tahiyar farko mutum ya karanta
salatin Annabi (saww) ko kuwa sai a tahiya ta biyu,daganan sai addua da
sallama.Allah yasaka da alkhairi.
(daga Maharazu Ali)
AMSA
====
Idan mutum yayi haka,
sallarsa tayi kuma bai aikata laifi ba asallarsa. Domin Salatin Annabi
(saww) abu ne mai kyau. Kuma ibada ce tsarkakakkiya.
Amma yadda yazo aSunnah, ana Karanta Salatin Annabi (saww) ne alokacin zaman tahiya na biyu..
Malamai sun bada muhimmanci sosai akan wannan. Domin kuwa akwai wadanda
suke ganin cewar FARILLAH ne daga cikin farillan sallah. Idan mutum ya
qi yin Salatin da gangan to bashi da Sallah. (Wannan shine ra'ayin
Imamush-Shafi'iy).
WALLAHU A'ALAM.
No comments:
Post a Comment