Salamu alaikum malam, Nakasance nabi wani mutum sallar azahar, Araka'ar farko sai ya zauna sai nace "SUB-HANALLAH!!!"
Sai ya mike muka kawo ta 2 mukayi
tahiyaH, muka karo 2 mukayi sallama.
To malam sai ya mike yatafi baiyi sujadar rafkanuwa ba.
To malam yaya sallah ta?
(daga Aminu Shehu).
AMSA
====
Malam Aminu sallarka tayi. Domin kuwa dukkanin Imamai na Mazhabobon nan
hudu sunyi ittifaki akan cewa Duk wanda ya manche sujjadar rafkanuwa
bai yita ba, to Sallarsa tayi.
Amma awajen Imamu Malik in dai ba'adiy ce zai rama ta koda bayan shekara guda ne.
Saboda haka kaima sujjadah Ba'adin zakayi domin kuwa ita ce ta kamaku acikin wannan rafkanuwar da ku kayi..
Wannan zaman da ku kayi, sannan ku ka dawo kuka mike, ya zamanto kamar kunyi Qari ne asallar.
Duk wanda yayi Qari asallah, sujjadah ba'ady zai yi.
WALLAHU A'ALAM.
No comments:
Post a Comment