Akramakallah idan namiji ya ba matarsa takardar saki, taki karba sai ya yaga takardar.
sakin yayi kuwa?
Tambaya ta 2:
Idan mutun sukayi fada da matarsa ransa yabaci ya dauko biro da takarda yafara
rubuta mata saki sai wani ya kwace
takardar ya yaga.saki yatabbata anan kokuwa?.
(daga Bashir Zamfara).
AMSA
*****
TAMBAYAR FARKO: eeh sakin ya yuwu. Domin kuwa ikon yiwuwar sakin ba'a
hannun matar yake ba.. Ahannun mijin ne. Tunda yace ya saketa ko ta
yarda ko bata yarda ba ta saku..
Ko ta karbi takardar ko bata karba ba ta saku. In dai yace mata ga takarda na sake ki shikenan.
Wallahu a'alam.
TAMBAYARKA TA BIYU: Malamai sunce duk lokacin da mutum ya rubuta
takardar saki kuma aka samu koda mutum daya ya shaidar da hakan, to saki
ya yiwu babu damar janyewa.
Don haka In dai har ya riga ya
rubuta kalmar saki acikin takardar, kuma shi wannan mutumin ya karanta
kafin ya yaga, shikenan sakin yayiwu.
Amma idan ya dauko kenan
ya fara rubuta Kwanan wata (date) kenan sai wannan mutumin ya karbe ya
yaga, (Tun bai rubuta kalamar saki acikin takardar ba) to shikenan BATA
SAKU BA. Aurensu yana nan..
Irin abin nan da iyaye suke yi wani
lokacin idan Dansu ya saki matarsa, sai suje gun matar su karbe
takardar su yaga, suce mata yi zamanki, wannan ma bai kamata adauki
cewar wannan sakin bai yiwu ba. Saki ya yiwu.. In dai wannan 'Dan nasu
ya balaga, kuma yana da hankali ba mahaukaci bane..
Wallahu a'alam.
No comments:
Post a Comment