Salam
alaikum malam idan mutum kaga dan uwanka ya fara alamun ya shiga shi'a
kuma daga baya ka tabbatar cewa hakanne yaya xakayi dashi?Allah ya
taimaki malam ya biya masa bukatunsa na alkhairi.
(Daga wani bawan Allah.).
AMSA
====
Abinda ya wajabta agareka shine ka nuna masa gaskiya.
Ka gaya masa cewa Kaunar Sahabbai wajibi ne. Kuma yana daga cikin alamomin imani.
Kuma Mutum baya cika Masoyin Annabi da Ahlul-Baiti har sai yaso Sahabbai gaba dayansu.
Kuma ka gaya masa zagin Sahabbai fasikanci ne. Wasu Maluman ma sun ce Kafurci ne.
Kuma ka gaya masa cewa Alkur'ani dai guda daya ne. Kuma ya cika. Babu wani abinda ya saura.
Don haka ya guji afkawa cikin mummunar Akidar nan ta Shi'a.
Allah ya karemu. Allah ya Qara mana shiriya abisa tafarkin Manzon Tsira (saww).
No comments:
Post a Comment