Monday, 25 February 2013

TA TUHUME NI DA CUTAR DA KE CIKIN JIKINTA SANNAN SAI TA KOMA GEFE 

20/4/2013

Akwai karin magana da Larabawa ke amfani da shi a lokacin da suka ga cewa wani mai aibi a jikinsa ya zargi abokin husumarsa da wannan aibin alhalin babu wannan aibin a cikin shi abokin husumar nasa. Suna cewa:-
((رمتني بدائها وانسلت))
Watau: ((Ta jefe ni da cutarta sannan ta koma gefe)).

Asalin wannan karin maganar shi ne: Akwai wani mutum da ake kira Sa'ad Dan Yazidu Manah, yana auren wata mata mai suna Ruhm Yar Khazraj ita mace ce mai kyawun gaske har ma ta haifa wa wannan miji nata wani yaro mai suna Malik, to ita Ruhm tana da kishiyoyi wadanda suke yawan aibanta ta da wani aibi da take da shi a bakin mahaifarta mai kama da gwaiwa saboda haka sai suna aibanta ta da wannan aibin suna kiran ta: "Ya Aflaa"! Watau Ya ke mai gwaiwar bakin mahaifa!!

To sai uwarta ta koya mata wata dabarar karya ta ce da ita: Ke Ruhm ga mafita nan: da zarar kin yi fada da wata kishiya daga cikin shiyoyinki, toh ki yi maza ki riga ta magana nan da nan ki ce da ita: Ya Aflaa!! Watau ja mani daga nan, mai gwaiwar bakin mahaifa kawai!!

Shi ke nan sai Ruhm ta riki wannan tarbiyyar karaya da uwarta ta koya mata, saboda haka da zarar ta bata da daya daga cikin kshiyoyin nan nata nan sai ta yi wuf ta ce da ita:- Ke! Bani wuri nan mai gwaiwar bakin mahaifa kawai!!! Sai ita kuma kishiyar ta tsaya tana mamakin wannan tsaurin ido na Ruhm tana cewa: Ta zage ni ta hanyar aibin da yake jikinta -ni kuwa babu shi a jikina saboda nuna tsaurin ido- sannan kuma ta yi mirsisi tamkar wata lafiyayya, mai kuma gaskiya cikin abin da ta fada!!
((رمتني بدائها وانسلت)).
Daga nan ne fa hakan ya zama karin magan a cikin Larabawa, ya zamanto dukkan wani mai wani aibi amma kuma sai ya zagi abokin husumarsa da wannan aibin to sai su ambaci wannan jumla:-
((رمتني بدائها وانسلت)).

SUN ZARGE MU DA SABA ALKAWARI, SUN KUMA ZARGE MU DA RASHIN SON HADUWAR KUNGIYAR IZALA!!!

Malam Sani Yahya Jingir da jama'arsa sun cutar da mu matuka, sun mana yarfe da jumhuri iri-iri, sun yi kokarin bata mana suna a idanun duniya ta hanyar daukan laifuffukansu suna dora mana. Zan dan ba ku misali kadan a wannan dan takaitaccen rubutu nawa domin lamarin cutarsu ya kara fita fili ga dukkan mai son gaskiya, da kuma kyamatar karya.

1. Sun zarge mu da cewa mu ba ma son hadin kan kungiyar izala!!
Alhali hakika tana bayyanar da cewa su din ne ba sa son hadin kan kungiyar izala ba wai mu ba, domin kuwa abin da ya faru shi ne: Yan kungiyar izala sun hadu a Masallacin Sultan Bello a karkashin jagorancin mutum 24 mutum 12 daga ko wane bangare a ranar 26/1/1433 H wanda ya yi daidai da 21/122011 M sannan suka zabi Sheik Abdullahi Bala Lau a matsayin shugaban kungiyar izala na kasa baki daya, suka kuma zabi Sheik Kabiru Haruna Gombe a matsayin babban sakataren kungiyar izala, suka kuma zabi Sheik Sani Yahya Jingir a matsayin shugaban majalisar malamai na kungiyar izala, suka kuma zabi M. Isa Waziri a matsayin darajtan yan agajin kungiyar izala. 

To amma sai daga baya wasu mutane suka koma gefe suka ce: Su kam shugabansu na kungiyar izala ba shi ne Sheik Abdullahi Bala Lau ba, a'a su shugabansu na kungiyar izala shi ne shugaban majalisar malaman kungiyar izalan watau Sheik Sani Yahya Jingir!!

Sannan kuma suka dinga yada cewa dukkn mutumin da ya yadda da cewa shi Sheik Abdullahi Bala Lau shi ne shugaban kungiyar izala, ko ya halarci taron da ya kira to lallai wannan ba ya son hadin kan kungiyar izalah, lalle wannan ya zama mai raba kan Al'ummah, lalle wannan ya zama munafuki cikin Al'ummah, lalle wannan ya zama mai yi wa shugabancin izala tawaye!!!

Alhali kuwa a wurin dukkan masu hankali su din nan su ne suke cikin wadannan siffofi dumu-dumu, ba wai wadanda suka bi ka'ida suka ce Sheik Abdullahi Bala Lau shi shugaban kungiyar izala ba.

2. Sun zargi Shugaban kungiyar izalah na kasa Sheik Abdullahi Bala Lau tare wadanda suka yadda da shugabancinsa da cewa su masu saba alkawari ne!!
Alhali kuwa su din nan su ne masu halin saba alkawari cikin kusan dukkan wani ittifaki da ya gudana tsakaninmu da su, abubuwan da suka saba alkawari a cikinsu suna da yawan gske, amma zan ambaci daya kawai daga cikinsu a matsayin misali:-

A zaman karshe da membobin kwamitin shuran nan mai mutum 24 suka yi a Kaduna a Masallacin Sultan Bello wanda shugaban kungiyar izala ya ke ciki, kuma shi ma shugaban majalisar malamai na kungiyar izala yake ciki an yi matsayar cewa: kada wani ya sake kiran shugaban Kungiyar izala da sunan "shugaban gudanarwa". Sannan lokacin da aka je wa'azin kasa a garin Lafiya, shi shugaban kungiyar izala na kasa Sheik Abdullahi Bala Lau, da kuma shi shugaban majalisar malamai ta kungiyar izala ko wanne daga cikinsu ya kara tabbatar da wannan matsaya da aka cimma a Kaduna a kan mimbarin kungiyar izala. 

To amma abin mamaki sai ga shi a kan mimbarin wa'azi a garin Kano shi shugaban majalisar malamai M. Sani Yahya ya warware wannan yerjejeniya, ya yi watsi da wannan alkawari, da wannan matsaya da aka cimma a garin Kaduna cikin Masallacin Sultan Bello, babu tsoron Allah babu kunyar jama'a ya fito fili ya kira shugaban kungiyar kungiyar izala da sunan shugaban gudanarwa!!!

Mun yi wannan rubutun ne saboda yakar karya da bazu a cikin mutane, da kuma tabbatar da gaskiya, domin kowa ya kasance a bisa basira cikin lamarinsa. Wannan kuwa dama shi ne aikin Kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunnah.

Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da ya hada kan al'ummarmu a kan gaskiya, ya kuma tsare mu daga sharrin masu yaudarar jama'a, ya kuma tabbatar da dugaduganmu a kan riko da sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah cikin dukkan aqiidarmu, da dukkan ibadarmu, da dukkan mu'amalarmu. Amee

WANE NE BAZAIGA ANNABI saw RANAR KIYAMA BA?
Daga Nana Aisha
(ra) tace:
nakasance acikin daki na ina dinke wani tufafi nawa sai fitila (aci
balbal) ta mutu kuma dakin yayi duhu sannan alluran ta fadi kasa ina
cikin wannan hali ina laluben alluran sai ga manzon Allah (saw) ya bullo
da fuskarshi daga kofar daki...
Ya daga labulen kofar sannan ya bullo da fuskarshi,

nana Aisha tace: na rantse da Allah wanda babu abin bautawa da gaskiya
sai shi hakika sassan dakin ya haskaka daga hasken fuskarshi sai na
waigo zuwa gareshi kuma nace:
mahaifina fansa agareka ya manzon Allah
BABU ABIN DA YAKAI FUSKARKA HASKE!
sai Annabi saw yace:
"ya Aisha, kwarin azaba ya tabbata ga wanda bazai ganni ba ranar
alkiyama!
Sai nana Aisha (ra) tace: wanene bazai ganka ranar alkiyama ba ya manzon
Allah? Ta maimata sau biyu
sai Annabi saw yace: "wanda aka ambaceni agurinshi sai bai yi SALATI
agareni ba.


Bismillahir Rahmanr Rahim
Ya ku bayin Allah!
Ba wata da'a ko ibada ko aikin lada da Allah madaukakin sarki ya ba shi muhimmanci a cikin Alkur'ani - bayan kadaita Allah - kamar yadda ya bada muhimmanci ga da'ar iyaye.
قال تعالى: (واعبدوا الله ولا تشركوا به شيئاً وبالوالدين إحساناً).النساء­:36
Da'ar iyaye na nufin bayyana son su, da darajanta su, da kiyaye alfarmarsu, da kauce ma fushinsu da biyan bukatarsu.
Idan mutum ya yi nazarin wahalar da iyaye suka sha wajen tashinsa da daure ma kuruciyarsa har zuwa sadda zai yi hankali shi kadai ya isa ya nuna masa girman hakkensu a kan sa. To, ina ga kuma an duba alhakin uwa na daukar ciki wata tara tsakanin lafiya da ciwo, laulayi da haraswa, da kyamar abinci da raunin jiki da nauyin ciki har zuwa ga nakuda wadda wata 'yar karamar lahira ce mata suke zuwa a mafi yawan lokuta!
Annabawa sun kasance masu tsananin biyayya ga iyayensu:
- Isma'il da mahaifinsa Ibrahim sun gina ka'aba
فلما بلغ معه السعي ..
وإذ يرفع إبراهيم القواعد
- Isa (AS):
وبرا بوالدتي ولم يجعلني جبارا شقيا
- Ibrahim (AS):
يا أبت إني أخاف أن يمسك عذاب من الرحمن... يا أبت ... يا أبت
- Nuhu (AS):
رب اغفر لي ولوالدي ولمن دخل بيتي مؤمنا...
Annabi SAWW ya nuna mana muhimmancin uwaye da da'arsu a cikin hadisai da dama:
1. Yardar Allah tana tare da yardar iyaye:
عن عبد الله بن عمرو رضي الله عنه قال صلى الله عليه وسلم ( رضا الرب في رضا الوالدين وسخطه في سخطهما ) رواه الطبراني وصححه الألباني. رقم: 3507 في صحيح الجامع.
2. Da'ar iyaye na daukaka matsayin mutum a aljanna:
عن عائشة أم المؤمنين رضي الله عنه قال رسول الله صلى الله عليه وسلم
( دخلت الجنة فسمعت فيها قراءة قلت من هذا ؟ فقالوا : حارثة بن النعمان ) فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم ( كذلكم البر كذلكم البر [ وكان أبر الناس بأمه ] )
صححه الحاكم ووافه الذهبي والألباني. راجع: السلسلة الصحيحة برقم 913 ، صحيح الجامع برقم 3371 ، مشكاة المصابيح برقم 4854
3. Da'ar iyaye tana gaba da jihadi in ba ya zama fardu aini ba.
عن عبد الله بن مسعود رضي الله عنه قال: سألت النبي صلى الله عليه وسلم أي العمل أحب إلى الله عز وجل؟ قال: ( الصلاة على وقتها) قال: ثم أي؟ قال: ( بر الوالدين ) قال ثم أي؟ قال: ( الجهاد في سبيل الله ) رواه البخاري ــ كتاب مواقيت الصلاة برقم 496
4. Uwa tana da wani karin fifiko saboda karin wahalarta wajen ciki da nakuda da shayarwa da reno.
روى البخاري ومسلم عن أبي هريرة – رضي الله عنه – أن رجلا قال : يا رسول الله من أحق الناس بحسن صحابتي ؟ قال : " أمك " قال : ثم من ؟ قال : " أمك " قال : ثم من ؟ قال : " أمك " قال : ثم من ؟ قال : " ثم أبوك " .
Ya ku bayin Allah!
Addinin musulunci ya wajabta mana kyautata ma iyayenmu a matsayin wani dan tukuici ga kokarin da suka yi mana sadda babu wanda zai yi mana in ba su ba. Ba a matsayin biyan hakki ba. Wani mutum ya hadu da sayyidina Umar a lokacin shi mutumin yana dauke da mahaifiyarsa yana dawafi da ita. Sai ya ce ma Umar: kana ganin ban bata hakkinta ba? Sai sayyidina Umar ya kalle shi, ya ce: a lokacin da take daukar ka fatar take yi ka rayu. A yanzu kai kuma jira kake yi ta mutu!!
Hakken iyaye bai kadaita kawai ga iyaye musulmi ba.
فعن أسماء بنت أبي بكر الصديق رضي الله عنهما ، قالت: قَدِمَتْ عليّ أمي وهي مشركة في عهد رسول الله صلى الله عليه وسلم، فاستفتيت رسول الله صلى الله عليه وسلم قلت: قَدِمَتْ عليّ أمي وهي راغبة أفأصل أمي؟ قال: ((نعم، صلي أمك)) متفق عليه.
Kai, ba wai zaman su kafirai ba, koda suna iya kokarinsu don su kafirtar da kai. Hakken da'a da kyautatawa gare su yana nan in ji Allah:
(وإن جاهداك على أن تشرك بي ما ليس لك به علم فلا تطعهما وصاحبهما في الدنيا معروفا واتبع سبيل من أناب إلي ثم إلي مرجعكم فأنبئكم بما كنتم تعملون) لقمان 14-15

Ya ku al'ummar musulmi! mu gode ma Allah da ya sa mu cikin inwar addinin musulunci da karantarwarsa mikakkiya. Daga cikin abinda bature ke fama da shi a yau mai tada hankali akwai tanadin da kowane mutum yake bukatar yi a can don tsufansa. Dole ne mutum ya tara wasu makudan kudade da zasu amfane shi idan ya tsufa. Don me? Don babu wanda zai kula da shi a wannan lokaci. In ba haka ba kuwa lalle ne zai kare rayuwarsa a gidan nakasassu da gajiyayyu wanda gwamnati ta tanada wanda kuma ba shi da banbanci da zaman fursuna a kurkuku. A lokacin 'ya'yansa maza da mata na can suna soyayya da abokai da kawayensu ba wanda ya damu da shi.
A kasashen turawa akwai kowace doka har da ta hakken karnuka amma babu wata doka akan hakken uwaye. Don me? Don wai kada a takura ma 'ya'ya! Za a shiga cikin 'yancinsu!!
Musulunci ya banbantar da 'ya'yansa da irin wannan karantarwa ta Alkur'ani da Sunnah da muka gabatar. Wata likita ta bada labarin biyayya mai ban mamaki. Tsohuwa ce wawiya da ba a haife ta ma da hankali ba. Danta ya zo da ita yana mai tsananin kula da ita. Ba ya son kome ya same ta. Saboda mamakin irin kulawarsa gare ta wannan likita ta tambaye shi, kuma ya sanar da ita cewa tun a tashin ta tana da tabuwar hankali kuma bata san abinda take yi ba. An aurar da ita ga mahaifinsa bayan ta samu cikinsa sai mahaifin ya kasa hakura da zama da ita. Tashin hankalin da wannan matar ta shiga shine, shi wannan ya kula da uwar da cikinsa kawai ta dauka bata san wahalarsa kowace iri ba yana ta tarainiya da ita haka.. To, mu da iyayenmu suka sha kowace irin wahala a kanmu ya zamu yi kenan?!
A cikin tarihin magabata akwai labarai masu kayatarwa game da bin wannan umurni na ubangiji.
1. Mis'ar bin Kidam (RH) ya taba kawo ma mahaifiyarsa ruwa bayan ta nemi haka amma ko da ya zo ta yi bacci. Sai ya tsaya har gari ya waye bai tashe ta ba kuma bai tafiyarsa ba.
2. Muhammad bin Al-Munkadir ya ce, na kwana ina murza kafar mahaifiyata don ta ji dadin bacci, kanena kuma ya kwana yana sallah. Ba zan yi fatar ayi mana musayar lada ni da shi ba.
3. Sayyidina Abu Huraira (RA) ya ga wani mutum yana tafiya bayan wani dattijo. Sai ya tambaye shi, wane ne? Ya ce, mahaifina. Sai ya ce: kada ka kira shi da sunansa, kada ka zauna kafin sa, kuma kada kayi tafiya a gabansa.
Bayan haka ya kai dan uwa musulmi! Ka sani ba wani laifi a wurin Allah wanda yake gaggauta kama mai yinsa, ya debe masa albarka, ya barkata masa rayuwa tun a nan duniya kamar cuta ma iyaye.
Sai ka ga mutum ya damu da matarsa, ya kula da 'ya'yansa amma bai ko san halin da mahaifiyarsa take ciki ba. Wani kuma yana cikin ni'ima da jin dadin duniya iri-iri amma yana nan birni yana ma-sha'a mahaifinsa ko na can kauye yana fama da nikar gero da dawa. Ko ka tarar da ya gina babban gida, yana hawan manyan ababen hawa amma mahaifiyarsa na cikin rubabben wuri kuma N100 suna ba ta shawa.
Mu gyara ya ku al'ummar musulmi.
Ga wasu shawarwari guda (20), duk mutumin da Allah ya albarkace shi da rayuwa tare da dayan mahaifansa ko dukansu ya kamata ya rike su:
1. Ka yi masu biyayya da da'a ga duk abinda suke so in bai saba ma Allah ba. Kuma duk abinda kake idan sun kira ka ka karba.
2. Ka nisanci duk abinda zai husata su ko ya tunzura su
3. Ka tsare mutuncinsu da girmansu a idon jama'a.
4. Yi kokari kayi duk abinda ka san yana faranta ransu koda ba su sa ka ba.
5. Ka karba kiransu cikin murmushi, ka je zuwa aikin da suka sa ka cikin nashadi.
6. Kada ka yi jayayya da su koda a cikin maganarsu ba su da gaskiya. A maimakon haka ka samu wani lokaci daban na lurar da su kuskurensu a cikin ladabi da hikima.
7. Ka saurare su idan suna magana kuma kada ka daga musu murya.
8. Ka tanye su aiki koda ba su neme ka ba.
9. Idan dayansu ba shi da lafiya ka himmatu wajen jinyarsa da kanka. Kome kake yi ka tabbata ka ware masu lokaci a cikin wannan hali. Kada ka ce aiki ya yi min yawa. Ka kaddara ciwon a kanka ne ya fada. Zaka ba shi lokaci ko shagali zai dauke ka?!
10. Bayyana ladabi gare su ko a wurin zama ko wurin tafiya. Kada ka saki jiki ko ka mike kafafu ko ka haura sama da su ko ka yi tafiya gabansu ta yadda zasu ji lalle ba su da wani matsayi na girmamawa gurin ka.
11. Kada ka taba damuwa ko jin ciwon bayyana cewa uwayenka ne. Kayi alfahari da su koda ba su da wata daukaka wadda ake kuri da ita.
12. Kada ka bari bukata ta kama su har su kai ga rokonka. Ka wadata su gwargwado da abinda zasu ji dadin rayuwa har su taimaki wani matukar kana da iko.
13. Nuna kulawa da su ta fuskar ziyara koda a wuri daya kuke. Idan kuma ba a wuri daya kuke ba to ka ware wani lokaci da zaka rinka tuntubar su, kana ziyartar su, kana samun lokacin fira da su, kana sauraren kokensu da biyan bukatarsu.
14. Rinka nuna masu godiya, da cewa duk abinda ka yi masu ba ka biya su ba a kan renonka da suka yi. Allah Ta'ala ya ce:
((أَنِ اشْكُرْ لِي وَلِوَالِدَيْكَ إِلَيّ الْمَصِيرُ)) لقمان:14
15. Kada ka bukace su da abinda ba su son ba ka. Idan kuma sun ba ka kayi godiya kamar ba a taba ba ka abinda ka ji dadi kamar nasu ba.
16. Kada ka fifita iyalanka ko 'ya'yanka a kan su.
17. ka boye masu mafi yawan kyautatawar da ke tsakaninka da iyalanka domin gudun shedan ya sa masu kishi a kan wannan.
18. Idan rashin jituwa ta shiga tsakanin su da iyalinka kada ka taba goyon bayan iyalinka a fili koda su ke da gaskiya. Sai dai ka lurar da su a asirce cewa, suna da gaskiya amma matsayin mahaifa abu ne ba na wasa ba.
19. Rinka neman addua a gurinsu kana fada masu bukatunka tare da sanar da su cewa, addu'arsu ta fi ta kowa kima da saurin karbuwa a wurin Allah.
عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال النبي صلى الله عليه وسلم: "ثلاث دعوات مستجابات لهن، لا شك فيهن، دعوة المظلوم، ودعوة المسافر، ودعوة الوالدين على ولديهما".
20. Kada ka taba yarda ka ja ma su zagi. Annabi SAWW yana cewa: "Yana daga cikin mafi girman kaba'irai mutum ya la'anci iyayensa. Aka ce, ya manzon Allah! Ya haka zata faru? Ya ce, zai zagi uban wani sai a zagi nasa. Ko ya zagi uwar wani sai a zagi tasa".
Bayan haka. Ya kai wanda Allah bai nufe shi da rayuwa da uwa ko uba ba. Ko kuma ka riga ka yi sakaci har sun wuce ba ka ba su hakkensu ba. Kada ka samu damuwa. Ko yanzu akwai yadda zaka yi:
1. Yawaita yin addu'a gare su da neman gafarar Allah. Babu laifi ka yi sadaka don neman masu gafara da sassauci daga ubangiji. Haka kuma ya halalta ka ziyarci kabarinsu don kayi masu addu'a ta fatar samun dausayi a cikin kabarinsu.
2. Ka zartar da duk wani abinda suka yi wasici da shi. Idan babu ka duba abinda suke sha'awa da duk wani abin da ka san suna jin dadin aikata shi na alheri musamman wanda ya shafi kyautata ma mutane, sai ka aikata shi.
3. Ka sada zumunci da yan uwansu da danginsu da masoyansu, kuma ka bi su gaba daya da kyautatawa.
Daga karshe..
Ka sani, duk yadda ka yi haka za ayi ma. "Kama tadinu tudanu.."
Uwaye kuma zasu iya taimakon dansu wajen yi masu da'a idan suna lallabawa da shi, suna tausaya masa, suna sa masa albarka. Kuma babu shakka addu'ar iyaye tana da babban tasiri ga shiriyar 'ya'ya da sa suyi albarka wadda iyayen su ne farkon masu cin moriyarta.
Allah ya yi mana albarka. Ya gafarta ma iyayenmu da suka riga mu. Wadanda muke tare da su Allah ya bamu ikon yin biyayya da kyautatawa gare su. Allah ya yi ma 'ya'yanmu albarka, ya sa su zama masu biyayya gare mu.
عباد الله،
-(إِنَّ اللَّهَ وَمَلَائِكَـتَهُ يُصَلُّونَ عَلَى النَّبِيِّ يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا صَلُّوا عَلَيْهِ وَسَـلِّمُوا تَسْـلِيمًا)- [الأحزاب/56].
وأكثروا عليه من الصلاة يعظم لكم ربكم بها أجـرا. فقد قال صلى الله عليه وسـلم : «مَنْ صَلَّى عَلَىَّ صَلاَةً صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ بِهَا عَشْـرًا».
اللهم صل وسـلم وبارك على عبدك ورسـولك نبينا محـمد صاحب الوجـه الأنور والجبين الأزهر، وارض اللهم عن الأربعة الخـلفاء أبي بكـر وعـمر وعـثمان وعـلي وعن سـائر أصحـاب نبيك أجمـعين، وعن التابعين ومن تبعهم بإحـسان إلى يوم الدين، وعنا معهم بعفوك ومنك وكرمك وإحـسانك يا أرحم الراحمـين.
اللهم أعز الإسـلام والمسـلمين، وأذل الشـرك والمشـركين، ودمر أعدائك أعداء الدين، وانصر عبادك الموحـدين، واحمي حـوزة الدين.
اللهم إنا نعوذ بك من شر اليهود والنصارى والرافضة، اللهم إنا نعوذ بك من شرورهم وندرأ بك اللهم في نحـورهم.
اللهم وآمنا في دورنا وأوطاننا وأصلح ووفق ولاة أمورنا، اللهم وأصلح قلوبهم وأعمالهم وسـددهم في أقوالهم وأفعالهم، واجمع شمـلهم وشمـل المسـلمين على الهدى يا رب العالمين.
ربنا آتنا في الدنيا حـسنة وفي آخـرة حـسنة وقنا عذاب النار.
اللهم اغـفر لنا، ولآبائنا ولأمهاتنا، ولأولادنا ولأزواجـنا، ولجـميع المسـلمين والمسـلمات، والمؤمنـين والمؤمنات الأحـياء منهم والأموات.
-(سُـبْحَانَ رَبِّكَ رَبِّ الْعِزَّةِ عَمَّا يَصِفُونَ (180) وَسَـلَامٌ عَلَى الْمُرْسَلِـينَ­(181)وَالْحَـمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِـينَ)- [الصافات/­180-182].
 — with Aliyu Said Gamawa and 4 others.

Yana daga cikin abinda ke karawa al'ummar mu ta yau kangara, lalacewa, da bijirewa dokokin addini, yadda ake fitinuwa da Jin kade kade da wake wake na soyayya, ko na zuga wadansu ko dai kowanne irin salon zamani na kida da waqa.
Hakika Jin kida rashin addini ne, damuwa da shaidanci ne, daukawa Kai zunubi ne, koyi ne da fajirai, dabi'ar marasa Imani ne, sanadin bushewar zuciya ne, kuma tsaurin kaine na bijirewa hanin addinin mu.
Duk Wanda ya fitinu da Jin kida da waka za kaga sauraron wa'azi da Jin karatun alkur'ani zai yi sauki gareshi, kuma zai gadar da wannan fitina ga iyalan sa, kuma su jawo masa zubewar mutumci da raunin addini.
Babban abin ki, mai ban takaici shine jingina wannan abin da addini, gashi ba Wanda ya isa yace Annabi saw, da sahabbansa sune suka doramu a wannan turba ta Kidan ganguna, jita, badujala da sauran na music da akeyi a yau da sunan addini ko yabon Annabi saw.
Pls kowa ya fara da Kansa da iyalan sa da duk Inda zai iya kaiwa sakon shiriyar Annabi saw cewa yawaitar kida da wake waken batsa da fululu, da wargi da sunan nishadi ba alheri bane garemu duka.
Hakika akwai narkon azaba ga masu wadannan kida a lahira, kuma kida abin kyama ne a musulumci, sannan tabbas Jin su yana rage Imani, kuma gabobin kunne da zuciya zasu bada shaida kan shagaltuwa da wassun mu keyi da kida da wake waken banza.
Dubi yadda ake tiqar kida da rawa a bukukuwan mu na aure da suna, sannan har ga tarurruka, yanzu har wuraren Ibada. Ga shaidanci cikin kida da waqe waqe a radio, Tv, wayar hannu, da sauran naurorin zamani ta ko Ina Ana ta halakar da Kai wajen yawan sauraron kida da waka.
Mu sani duk Wanda ya tuba ya Bari zai samu lada da Karin shiriya daga Allah, kuma Allah zai yi masa albarka, wanda kuwa ya rudu da rai da lafiya yayi watsi da hanin da addini yayi to ya shirya, kuma ya jira gamuwar sa da Allah gobe kiyamah.
Yana daga cikin abinda ke karawa al'ummar mu ta yau kangara, lalacewa, da bijirewa dokokin addini, yadda ake fitinuwa da Jin kade kade da wake wake na soyayya, ko na zuga wadansu ko dai kowanne irin salon zamani na kida da waqa.
Hakika Jin kida rashin addini ne, damuwa da shaidanci ne, daukawa Kai zunubi ne, koyi ne da fajirai, dabi'ar marasa Imani ne, sanadin bushewar zuciya ne, kuma tsaurin kaine na bijirewa hanin addinin mu.
Duk Wanda ya fitinu da Jin kida da waka za kaga sauraron wa'azi da Jin karatun alkur'ani zai yi sauki gareshi, kuma zai gadar da wannan fitina ga iyalan sa, kuma su jawo masa zubewar mutumci da raunin addini.
Babban abin ki, mai ban takaici shine jingina wannan abin da addini, gashi ba Wanda ya isa yace Annabi saw, da sahabbansa sune suka doramu a wannan turba ta Kidan ganguna, jita, badujala da sauran na music da akeyi a yau da sunan addini ko yabon Annabi saw.
Pls kowa ya fara da Kansa da iyalan sa da duk Inda zai iya kaiwa sakon shiriyar Annabi saw cewa yawaitar kida da wake waken batsa da fululu, da wargi da sunan nishadi ba alheri bane garemu duka.
Hakika akwai narkon azaba ga masu wadannan kida a lahira, kuma kida abin kyama ne a musulumci, sannan tabbas Jin su yana rage Imani, kuma gabobin kunne da zuciya zasu bada shaida kan shagaltuwa da wassun mu keyi da kida da wake waken banza.
Dubi yadda ake tiqar kida da rawa a bukukuwan mu na aure da suna, sannan har ga tarurruka, yanzu har wuraren Ibada. Ga shaidanci cikin kida da waqe waqe a radio, Tv, wayar hannu, da sauran naurorin zamani ta ko Ina Ana ta halakar da Kai wajen yawan sauraron kida da waka.
Mu sani duk Wanda ya tuba ya Bari zai samu lada da Karin shiriya daga Allah, kuma Allah zai yi masa albarka, wanda kuwa ya rudu da rai da lafiya yayi watsi da hanin da addini yayi to ya shirya, kuma ya jira gamuwar sa da Allah gobe kiyamah.

Sunday, 24 February 2013

ladabin zama

Manzon Allah s.a.w yace: ((abunda ke tsakanin imani da kafirci shine sallah. muslim: 82, Nasai: 460, Tirmizi:2618.
yasake cewa: tsakanin bawa da shirka ko kafirci shine barin yin sallah. Tirmizi
yasake cewa: abunda tsakanin bawa da kafirci shine barin yin sallah. Abu Dawud:876, Ibin Majaa:1078, Nasa'i:463.
daga Abdullahi bin Buraidata daga babansa yace: Manzon Allah s.a.w yace: Alqawarin dake tsakaninmu da bayi itace sallah, duk wanda ya barta haqiqa ya kafirta. Nasa'i:62, Ibn Majah:1097.
Al-Uqailiy yace: sahabban manzon Allah s.a.w sun kasance basa ganin wani aiki da barinsa kafircine in banda sallah.
Abu Isa yace: naji abu Musaiyib almadany yana cewa: duk wanda yace: imani aikine kadai to ya gaggauta tuba, inya tuba shikenan in bai tubaba a cire kansa.
ya Allah muna roqonka ka azurtamu dayin sallah ka karba mana daga kyawa-wanmu ka yafe mana kura kuranmu
 KADAN DAGA CIKIN LADDUBAN WURIN ZAMA GASUNAM KAMAR HAKA : (1) IDAN KAZO MAJALISA KAYI SALLAMA AKAN YAN UWANKA MUSULMAI, KAMAR FADIN MANZON ALLAH (S.A.W) YACE (IDAN DAYANKU YAZO MAJALISA TO YAYI SALLAMA, IDAN YANUFI TASHI TO YAYI SALLAMA,DAN SALLAMAN KASHE NADA HAKKI KAMAR NA FARKO. (2) IDAN KUNZO MAJALISA TO KUZAUNA A KARSHE, KAMAR FADIN JAFAR ALLAH YA YARDA DASHI YANACEWA: (MUNKASANCE IDAN MUNA WURIN MANZO ALLAH(S.A.W) A MAJALISA KOWANNE DAYANMU INYAZO YANA ZAMA AKARSHEN MAJALISA). (3) KADA A TASHI ATASHI WANI MUTUM AWURIN ZAMANSA DON WANI yazauna, kAMAR FADIN MANZON ALLAH (S.A.W) (BAI HALATTA KUTASHI WANI AGUN ZAMANSABA SANNAM WANI YAZAUNA AGUN, SAI DAI KU YALWATA KUMA KUBUDA). (4) KAR KA RABA TSAKANIN MUTUM BIYU KAZAUNA, KAMAR FADIN MANZON ALLAH (S.A.W) (BAI HALATTA GA WANI YA SHIGA TSAKANIN MUTUM BIYU BA HAR SAI SUN AMINCE). (5) KUNISANCI ZAMA A TSAKIYAN TARO (IN AN ZAUNA ANYI KEWAYE KASHIGA TSAKIYA) KAMAR FADIN MANZO ALLAH (S.A.W) (ANTSINEWA DUK WANDA YAZAUNA A TSAKIYAR MUTANE
Nine idan nayi fitsari kafin nayi alwala kenan bayan nayi, bayan na tabbatar komai ya gama fita kuma nayi tsarki sai na fara sallah nayi kamar raka a biyu ko fiye sai naji wani abu ya taho min kamar fitsari idan na yanke sallah na duba sai naga ba komai daya fito
daga gaba na,
Kuma nasha dobawa sau tari da yawa amma
bana tadda komai.
Shine nake buqatan a qara fahintar dani game da wannan matsalar. dama makamancin
irin wannan. ka huta lfy malam.

(daga Halilu Bello).

AMSA
*****
MALAM HALILU BA KOMAI NE YAKE SANYA KA IRIN WANNAN TUNANI BA ILLA WAS-WASI (SHARRIN SHAYTAN).

Saboda haka ka dena damuwa.. Kuma ka ci gaba da kokarin dena wannan waswasin.

Ka yawaita addu'ah da kuma karanta Azkar irin na Annabi (saww).

Ko acikin Litattafan fiqhu ma, Malamai sunyi umurni da cewar mutum yayi kokarin jefar da duk wani waswasi, yayi aiki abisa yakini.

WALLAHU A'AL
Amma idan a Sallar farillah ne, kuma mutum shine yake limanci, to anaso ya saukaka. Saboda zai iya yiwuwa acikn Mamunsa akwai tsofaffi da raunana, da kuma mabukata.

Yazo ackin hadisai da dama kuma ingantattu, cewar Manzon Allah (saww) ya kan tsawaita sujjadar asallar dare, ko kuma Sujadar-Godiya ga Allah (swt).

Dangane da halaccin yin addu'a da hausa kuwa, Eh ya halatta. Amma anfi son yayi ta da larabci in har zai iya. Ya dauko dag cikin addu'o'in Annabi (saww).
Idan kuwa ba zai iya ba, to babu wani laifi akansa don yayi da hausa.

Kuma lallai Lokacon da mukayi sujjada, lokacine na amsawar bukatunmu. Saboda haka ya dace muyi ta addu'a ga kanmu da kuma Lyan uwanmu musulmai aduk inda suke.

(wallahu a'alam)
Malam menene hukuncin mutum yasa matar da zai aura ta kwabe hijabinta don yaga kwalliyarta??

(daga Murtala Y.D. kazaure)

AMSA
*****
A'A BAI HALATTA BA. Domin kuwa ya zarce iyaka.

Wajen da aka yarda mutum ya kalla ajikin matar da zai aura sune : FUSKA DA KUMA TAFIN HANNU.
Sune guraren da Annabi (saww) yayi umurnin mu kalla ajikinsu.

Amma sanyata ta kwabe Hijabi, wannan ya sabawa shari'a domin kuwa ba ya halatta mutum ya kalli duk wata kwalliya da mace zata yi sai dai in yana cikin muharraman ta. (kamar yazo acikin Suratun-Nuur).

Sannan kuma kallonta haka tsura ba tare da Hijabi ba, daga shi sai ita, zai iya haifar da fitina atsakaninsu.

Domin kuwa idan sha'awarsu ta motsa, komai zai iya faruwa. Kuma ayoyi da hadisai da dama sunzo akan umurnin cewar mu rintse idanuwanmu daga Kallo irin na haram.

(Wallahu A'alam)
Malam menene matsayin mutumin da yace shi bai yarda da hadisan Annabi {saww} ba? kuma yace bai yarda dukkan litattafan musulunci ba??

<daga Aisha milo>

AMSA
=====
IRIN WANNAN MUMMUNAR AQEEDAH CE TA 'YAN QALA-QATO DA KUMA GULATU SHI'A. Duk mai yinta ba za'a kirashi musulmi ba.

AMMA DUKKANIN MALUMAN MUSULUNCI SUNYI ITTIFAQIN CEWAR WAJIBI NE MUYI IMANI KUMA MUBI DUKKAN ABINDA ANNABI {SAWW} YAZO MANA DASHI.

DOMIN KUWA ALLAH (SWT) YANA CEWA: "KUBI (DUKKAN) ABINDA MANZO YAZO MUKU DASHI, KUMA KU HANU DAGA DUKKAN ABINDA YA HANEKU DASHI"
(surat alhashri)

Duk mai irin wannan akidar kafuri ne domin kuwa ALLAH (SWT) yana cewa "NA RANTSE DA UBANGIJINKA BA ZASU YI IMANI BA, HAR SAI SUN SANYAKA KA ZAMA MAI HUKUNBCI ACIKIN ABINDA YAKE FARUWA ATSAKANINSU,KUMA SUN SALLAMA MAKA CIKAKKIYAR SALLAMAWA"

Bai halatta ayi koyi da irin wadannan mutane ba.

Kuma ya kamata hukuma ta dauki mataki akansu. Domin kuwa Sayyiduna Umar (ra) ya kashe wani mutum yayinda yaki yarda da hukuncin Annabi {saww}.
Malam menene hukuncin wanda yayi amfani
da matar da take idda bata cika ba??? (daga Yakubu Adamu) AMSA
*****
Salam.. To Mal  ba ka bambance ba.
(baka fito da tambayar taka afili ba). Shin matarsa ce wacce ya saki, sannan yaje
ya sadu da ita kafin cikar iddar ta?? Shin ba shine ya sake ta ba, amma Saduwar
da yayi da ita, ahalin aure aka daura musu
kafin iddarta ta cika?? Ko kuwa kawai yaje yayi zina da ita ne?? * idan ta hanyar Aure ne wanda aka daura
alhali matar tana cikin idda,To nan ma akwai
maganganu guda biyu. * Shin ya san cewa iddar tata bata Qare ba? * ko kuwa be sani ba?? Idan da saninsa ya auri matar da take cikin
idda, to za'a 'bata auren. Sannan a ladabtar
dashi.
Amma babu haddi akansa. * idan kuwa acikin rashin sani ne, duk da
haka za'a raba auren. Kuma laifin yana kan ita
matar da kuma waliyyanta.
Idan kuwa ya sadu da ita ne ba ta hanyar
aure ba, to ai bashi da bambanci da sauran
mazinata. Idan saurayi ne, kuma shaidu sun tabbata, ko
kuma yayi Iqiqrari da kansa, to shari'a za'tayi
masa bulala Dari chif. Idan kuwa ya taba yin aure, kuma shaidu sun
tabbata, ko kuma yayi Iqrari da kansa, to
hukuncin rajamu ne. (wato jefe shi za'ayi). Ita ma matar haka.. Amma duk wannan fa hukuma ce take da
dama da kuma ikon aiwatarwa. Sannan kuma
akwai Qarin bayanai masu yawa.. * Idan kuwa matarsa ce, shi ya saketa,
Sannan kuma yaje ya sadu da ita kafin cikar
iddarta, to shikenan ya maida ita kenan
Automatically. (ta sake komawa matarsa
kenan) don karin bayani aduba Subulus-Salam
sharhin bulughul-Maram, Kitabut-Talaaq.
Wallahu a'alam

Salam malam meye najasa? Kuma meye babancin
najasa da janaba ??
(daga Dogon Yaro Bassa).

AMSA
*****
Atakaice dai Najasa ita ce duk wani abinda yake fitowa ta Al'aurar Dan Adam, ko kuma ta duburarsa. misali:

Ba haya, Fitsari, Maziyyi, Wadiyyi. Jinin haidha, da Jinin biqi.
Shi kuwa Maniyyi akwai sabanin malamai dangane da cewa najasa ne, ko kuwa ba najasa bane.

Malikiyyah da Hanafiyya sunce najasa ne. Amma sauran Maz-habobi sunce A'a ba najasa bane. Duk da cewar fitarsa yakan wajabta wanka.

Sannan Mushe ma Najasa ne. Jini ma Najasa ne.

Ita kuwa janaba ita ce yanayin da mutum yake shiga Bayan Fitar maniyyi daga jikinsa abarci ko afarke. Ta hanyar Jima'i ne, ko waninsa.

Sannan shigewar al'aura ma acikin Farji yana sanya janaba..

Ita najasa ana samun tsarki idan aka wanke ta.

Amma ita kuwa janaba dole sai anyi wanka da ruwa mai tsarki. (kamar jinin haila dana Biqi shima haka sai anyi wanka idan ya dauke.

Wallahu a'alamu
Assalamu alaikum malam tam bayata itace
wani lokacin dan wani abun yasa sha'awata
ta motsa SAI INJI Wani abu ya digo kalarsa
kamarta fitsari amma da danyauki ba kamar maniyyi ba. to malam shi wannan meye sunanshi?
kuma in ya fito ya'ake tsarkakeshi ?? 

<daga ibrahim S ala>.

AMSA
*****
SUNANSA MAZIYYI. Kuma ana wankewa al'aura ne gaba dayanta. (ba wanka ake yiba).

Wallahu a'alam.

Amma munsha yin nasiha ga matasa cewar su kiyayi sanya sha'awarsu aguraren da basu dace ba.

Kalle-kalle haramun ne a Musulunci..

Allah ya hana, Annabin Allah ma ya hana (saww
menene hukuncin mutumin da ke runguman pilo idan matan sa ko kuma mijin ta bai tare dashe/ita dun ya/ta isar da sha'awan sa har yayi inzali, ya halatta mallam??

(daga wata baiwar Allah).

AMSA
*****
MUN AMSA IRIN WADANNAN TAMBAYOYIN ABAYA. Amma dai Bai halatta mutum ya fitarwa kansa maniyyi ba.. Ko ta wacce hanya ce, in ba ta hanyar da Allah ya yarje mana ba.

Saboda Takhsisin nassi na Al-Qur'ani "ILLA 'ALA AZWAJIKUM AU MA MALAKAT AIMANIKUM".

Don haka akiyaye.

Amma babu laifi miji ya rungumi matarsa yayin da take cikin al'ada. Har yayi inzali.

Sannan babu laifi idan mace tayi wasa da al'aurar mijinta har yayi inzali. Ko kuma shi yayi mata haka.

Amma kuma haramun ne mutum ya fitarwa kansa maniyyi da kansa da gangan...

Wallahu a'alam,
Malam mutum ne ya sha nonon matar sa.
Yanzu minene matsayin auren su ??

(Usman Isa Dawa)

AMSA
*****
AURENSU YANA NAN. Kuma babu komai akansa.

Insha Allah nan gaba zamu yi cikakken bayani akan wannan.

Wallahu a'alam
MALAM NI MIJINA NE YAKE BATA MIN RAI. Kullum idan mun sadu a jima'i sai yaje yana gaya wa abokansa yadda mukayi... Ba qarya nake masa ba domin watarana har najishi da kunne na..
kuma sau da yawa, muma matan nakan ji wadansu suna irin wannan zancen idan an hadu agidan biki. Suna fadar sirrin mazajensu.

Malam.. Shin yin hakan babu laifi ne?? Idan kuma akwai, to don Allah ayi musu wa'azi ko zasu dena.

(daga wata baiwar Allah).

AMSA
--------
Gaskiya yin hakan ko kadan bai dace ba. Kuma ba ya daga cikin Halaye na mutanen kirki.

Kuma yin hakan zai iya janyowa mutum fushin Ubangiji. Domin Kuwa Manzon Allah (saww) cewa yayi:

"YANA DAGA CIKIN MAFIYA SAMUN MUMMUNAR MAKOMA AWAJEN ALLAH, MUTUMIN YAKE BIYAN BUKATARSA AWAJEN MATARSA, ITA MA TA BIYA BUKATARTA AWAJENSA, SANNAN YAJE YANA WATSAR (KO KUMA BAYYANAR) DA SIRRIN TA"

(Hadisi ne Sahihi. Imamu muslim ne ya ruwaito shi. Hadisi mai lamba 1437. Abu Dawud ma ya ruwaito shi, aduba Sunan nasa, hadisi mai lamba 4870. Imamu Ahmad ma ya ruwaito shi acikin Musnad nashi. Acikin Juzu'i na 6 shafi na 69).

Kuma shi irin wadannan abubuwan suna daga cikin rashin kunya. Duk mutumin da yake da kunya, to ba zai aikata haka ba.

Domin Musulunci kullum yana umartar mu ne da kyawawan Dabi'u kamar su Kunya, rikon gaskiya da kiyaye sirri.
Harma Manzon Allah (saww) yana cewa:

"KUNYA TANA DAGA CIKIN IMANI. KUMA BABU IMANI GA MUTUMIN DA BASHI DA KUNYA".

(bukhary da muslim).

Saboda haka ya zama wajibi ga Mazaje da kuma matayen da suke aikata irin wannan suji tsoron Allah su dena.

Akwai wata mata, kullum suka hadu da Qawarta sai ta bata labarin yadda suke kwanciya da mijinta.. Rannan sai suka rabu da mijin, akayi sa'a itama waccan ashe sun rabu da nata mijin, Kafin wani lokaci sai gashi ta aure mijin Abokiyar tata.
Ashe daman ta dade tana sha'awarsa ta dalilin labarin da take ji agun Qawarta.

Hakanan mu ma mazan irin hakan yana faruwa sosai. Shi yasa sau da yawa zaka ga aboki ya lallaba yaje ya aure matar abokinsa bayan sun rabu.
Awasu lokutan ma, irin wannan bayyana sirrin ne yake kawowa yawaitar Kwartanci atsakanin al'aummah.

Sai kaji miji yana zina da matar abokinsa, ko kuma mace tana zina da mijin Qawarta..

Allah ya tsare mu da ikonsa.

Wallahu A'alam
Allah gafarta malam, menene hukuncin exclusive breast feeding a musulunci? Wato
shayar da jariri ruwan nono zalla ba a bada ruwa har tsawon wata shida? 
Urgent please.

ZAUREN FIQHU 
*************
Yana da kyau sosai mutukar dai za'ayi abisa
tsarin da ya dace da shawarar likitocin Islama. Domin sunyi bincike sun gano cewar hakan yana Qarawa jaririn lafiya. Kuma ba ya cutarwa ko kadan.

Na saurari wani babban Malami kuma Dokta yana magana akan wannan. Yana cewa shi wanda ya halicci Jaririn (Allah kenan) ya sanya masa dukkan abinda jikinsa yake bukata acikin wannan ruwan nonon.
Har su ruwan sha din da dukkan Vitamins da Nutrients da minerals wadanda suka dace da lafiyar jaririn.

Sai dai abnda za'a kula anan shine: akyautata
niyyah.

Kar ayi domin wata manufa marar amfani.

Abinda Musulunci yake kyama kuma yake hani akai shine:
shayar da jariri Nono dan kanti wanda ba'a san ko na wacce mata bane. (irin yadda turawa suke yi).
Domin kuma Manzon Allah (saww) yace "ITA
SHAYARWA TANA CHANZA DABI'AH".

Kinga kenan idan kika sayo dan kanti, watakil ma na wata Kafirar ce, ko kuma karuwa, kuma kika shayar da Jaririn da kika haifa, to yaron ba zai dauki halayenki ba.

Sai dai ya dauki na waccan shu'umar Matar.

Idan kuma nonon Musulma ce, to duk da haka dai baLa kubuta ba. Domin kuwa baki san ta ba, kuma daga ranar da kika shayar da jaririnki nononta, to ta zama Uwarsa kenan. 'ya'yanta gaba daya sun zama Muharramansa kenan. Babu damar ya auresu.

Kuma idan ba'a sani ba, ba za'a iya kiyayewa ba.

Allah ya kiyaye mu.

Wallahu A'alam

MALAM MENENE HUKUNCIN MUTUMIN DA YA TA'BA/YA SHAFI JIKIN MATARSA ALHALI SHI YANA DA ALWALA??
Malam shin alwalarsa tana nan? Ko ta karye??

AMSA
*****
Mazhabar Malikiyyah da Hambaliyyah da Kuma Imamul-Auza'iy sun tafi akan cewar in har mai alwala ya shafi jikin mace da niyyar jin dadi, da sha'awa, ko yaji dadin ko bai jiba, To alwalarsa ta karye.

Idan ma bai nufi jin dadin ba, amma kuma ya samu jin dadin, nan ma alwalarsa ta karye.
Idan kuwa bai nufi jin dadin ba, kuma bai ji dadin ba, to alwalarsa tana nan.

Amma Maz-habar Imam Abu Haneefah sunce alwalarsa ba ta Karye ba, sai dai in har wannan shafar ta sanya masa motsawar Sha'awarsa.

Amma Muhammad ibnul-Hasan (daga maluman Hanafiyya) yace alwalarsa tana nan koda Wannan shafar ta sanya mikewar azzakarin shi mai yin shafar.

Imam Sufyanuth thaury da kuma mutanen Kufah sunce KISS (SUMBA) ba ya karya alwala.

Sai dai Maz-habar Imamush-Shafi'iy sunce: alwalarsa ta karye abisa kowanne yanayi, sai dai idan muharramarsa ce, to alwalarsa tana nan..

ITA KUMA MATAR DA AKA SHAFA DIN MENENE HUKUNCINTA???

Imam Malik da Imamush-Shafi'iy da Imam Ahmad (Allah ya qara musu yardarsa) sunce Hukuncinta daya ne da mai yin shafar.

Hadisin da wasu suke kafa hujja dashi akan halascin shafar mace, ko kuma yi mata KISS BAI INGANTA BA.

Imam Ahmad ya fitar da Hadisin daga Nana A'isha (rta) cewar "MANZON ALLAH (SAW) YA SUMBANCI WATA DAGA CIKIN MATANSA, SANNAN YA FITA WAJEN SALLAH BA TARE DA YA SAKE ALWALA BA"..

"Imamul-Bukhary ya Raunana hadisin.. Yace bai inganta ba. Sannan Imamul baihaqiy ya fitar da hadisin ta hanyoyi guda goma. Amma yace dukkansu basu inganta ba.

Imam Ibnu Hazmin (yana daga cikin manyan maluman ilimin hadisi) shima yace Babu wani hadisi ingantacce dangane da wannan maganar. Yace idan ma an samu wani abu ya inganta, sai dai mudauke shi amatsayin anyi aikin ne kafin saukar ayar nan data yi magana akan sake alwala bayan shafar mace.

Shima Abu Dawud ya ruwaito shi.. Amma shima yace bai inganta ba.

Amma dangane da wani Hadisin kuma na Nana A'ishatu (rta) Na cikin Bukhary Wanda take cewa TA KASANCE TAKAN MIKE KAFARTA AWAJEN DA MANZO (SAWW) ZAI YI SUJJADA, IDAN YAZO SUJJADAR, YAKAN TA'BA TA SANNAN SAI TA NA'DE KAFAFUNTA IDAN YA GAMA SUJJADARSA KUMA SAI TA SAKE MIKEWA KAFAFUNTA"

Imam Ibnu Hajar ya fada acikin "FAT-HUL-BARY" sharhin Sahihul Bukhary, akan wannan hadisin cewar "WANNAN ZA'A IYA DAUKAR CEWAR AKWAI WANI ABUNDA YA RUFE QAFAFUNTA, KO KUMA KHUSUSIYYAH CE IRINTA MANZON ALLAH (SAWW).
Shi yasa shi alwalarsa ba zata karye ba. Koda yayi hakan.

Don karin bayani aduba:

1. Rahmatul-Ummah na Imamud-Damashqee (shafi na 13-14)

2. Subulus-Salam, Juzu'i na farko, Shafi na 101-103.

3. Tuhfatul-Ashraf Juzu'i na 13, shafi na 234.

4. MUSNAD na Imamu Ahmad bn Hambal, juzu'i na 1 shafi na 168 da kuma na 216.

5. Abu Dawud juzu'i na 1 shafi na 178-179.

6. SUNANUT-TIRMIDHY, Juzu'i na daya shafi na 86.

Wallahu A'alam.

*************
SLM SHIN YA HALATTA GA MUTUM YAYI TSATSUBA DAN KARE KANSA.?MISALI KAMAR MASU YIN LAYAR ZANA DA SUKE AMFANI DA ITA DAN SU KUBUTA.

(daga Rukayyah N. shu'aibu)

AMSA
*****
Gaskiya bai halatta ba. Ba ma shi ba, babu wani nau'i na sihiri wanda ya halatta musulmi ya yishi.

Ko da niyyar kare kai, ko kuma da wata niyyar ta daban..

Domin kuwa Allah (saww) yana cewa "ALLAH BA YA GAFARTAWA IDAN ANYI SHIRKA DASHI, AMMA YANA GAFARTA ABINDA YAKE KOMA-BAYAN WANNAN GA WANDA YASO".

Sannan Manzon (saww) yana cewa "KU KIYAYI ABUBUWA GUDA 7 MASU HALAKARWA: sai ya fara da cewa "AL-ISHRAAKU BILLAH".. (hada wani da Allah wajen bauta).

Domin duk wani sihiri da kike jin labarinsa, ko qarami ko babba, ko na alheri ko na mugunta, to ba ya ci sai da sa hannun shaitanun aljannu. Su kuma basu yarda su biya bukatar dan adam, har sai sun tabbatar ya riga ya zama bawansu mai yi musu hidima. Kamar yanke-yanke, ko kuma su sanya shi ya aikata wani Qaton zununbin wanda zai iya kaishi zuwa Kafirci.

Kamar su sanyashi ya rika Fitsari akan Alqur'ani, ko su sanya shi ya dena yin wasu salloli, ko su sanya shi yayi zina da Mahaifiyarsa, ko 'yarsa, ko Qanwarsa. (wal iyazu billah.).

Ya kamata musulmi mu san cewar Manzon Allah (saww) ya gama mana komai tunda ya bar mana Alkur'ani da Sunnoninsa, wadanda suke cike da addu'o'i da azkarai masu fa'idantarwa ako wanne yanayi.

Sannan ga Sunayen Allah nan kyawawa guda 99. Duk wanda mutum ya dauka yake karantawa domin neman biyan wata bukata, to Insha Allah Allah zai amsa masa.

Don haka aguji zuwa wajen 'yan duba da 'yan bori da masu tsatsuba.

Domin yin hakan zai iya kai mutum izuwa rasa imaninsa.

Idan mutum tsari yake nema, gasu Ayatul-Kursiyyi nan da falaki da nasi.

Idan mutum biyan bukata yake nema, ga fatiha nan.

Wallahu A'alam.

Mallam dan allah ya halatta idan mutum ya mutu kaninsa zai iya aurar matarsa???


Mallam dan allah ya halatta idan mutum ya mutu kaninsa zai iya aurar matarsa???

AMSA
*****
EH YA HALATTA QANI YA AURI MATAR DA WANSA YA SAKI.. Ko kuma wa' ya auri matar da kaninsa ya saki.

Ko da ran dan uwan ko babu ransa.

Ko da bayan ta gama takaba ne, ko kuma bayan ta auri wani ta fito.

Domin irin haka ya faru azamanin Manzon Allah (saww).

Akwai Sayyidah Asma'u Bintu Umais. Matar Sayyiduna Ja'afar ne, Wan Sayyiduna Aliy (kw). Bayan Sayyiduna Ja'afar yayi shahada ayakin Mu'utah, sai ta Auri Sayyiduna Abubakar. Sannan bayan Sayyiduna Abubakar din (ra) ya rasu, sai kuma Sayyiduna Aliy (ra) ya aureta. Kuma dukkansu ta haihu dasu.

da Ja'afar da Aliyyu duk mahifinsu daya, mahaifiyarsu ma daya. Shakikai ne. (rta).

Sannan kuma Sayyiduna Aliyu (ra) ya aurar da 'yarsa Sayyidah Zainab Alkubra ga Sayyiduna Abdullahi bn Ja'afar. Bayan ya rasu sai kuma Qaninsa shakiki ya aureta da amincewar Sayyiduna Aliyu. (kw).

Sannan kuma koda dukkan 'yan uwan suna da rai, shari'a bata hana ba.

Sai dai kuma saboda yanayi na zaman tare.

Domin idan irin hakan tana faruwa alhali suna raye dukkansu kuma a gari daya, dangantakarsu ta zumunci zata iya lalacewa.

WALLAHU A'ALAM.

Friday, 8 February 2013

MUSULUNCI>>
< MUSULUNCI>>>
Musulunci shine addinin da mafiya yawan Hausawa suke bi. Kimanin kaso 90 cikin 100 ne na Hausawa suke bin addinin musulunci. Ma'anar Musulunci shine "Mika wuya ga kadaituwan Allah (SWT) cikin abubuwan da ya kebantu dasu, da mika wuya ga umarnin Allah Ubangijin talikai, tare da tsarkaka daga kafirci (sanya kishiya wa Allah) da kafirai." Allah (SWT) shi ya aiko Annabi Muhammadu (Yabo da Amincin Allah su Tabbata a gare shi)da Al Kur'ani Mai Girma. Yanzu haka, akwai fiye da Musulmai Biliyan Daya da Miliyan dubudari biyar a fadin duniya.
Allah ka dawwabar damu a musulunci, Ameen

Daga Abi Hurairah Allah ya yarda da shi: yaji Annabi mai tsira da aminci yana cewa: "Hakika akwai mutane uku daga cikin bani isra'ila: kuturu da maikora da makaho, Allah yayi nufin ya jarrabesu, sai ya aika musu da mala'ika. Sai yaje wajen kuturu yace: Wane abu ne mafi soyuwa a gareka?sai yace: launi mai kyau, da fata mai kyau ya kuma tafiyar min da abinda mutane suka kazantani da shi. Sai Mala'ika ya shafe shi, kazantar tasa ta tafi, kuma aka bashi launi mai kyau da kuma fata mai kyau. Sai Mala'ika yace: wace dukiya ce mafi soyuwa a gareka? Yace rakuma, ko kuma yace saniya-Mai ruwayar yayi kokwanto. Sai dai cewa kuturu ko mai kora baya daga cikin su yace: Rakuma, dayan kuma yace shanu, sai aka bashi taguwa da mai ciki- Yace: Allah yayi maka albarka a cikinta.

Sai kuma yajewa mai kora yace: Menene mafi soyuwa a gareka? Yace gashi mai kyau, kuma abinnan da mutane suka kazantani da shi ya tafi sai ya shafa shi, kazantar ta tafi daga gare shi. Kuma aka bashi gashi mai kyau, yace: wace dukiya kafi so? Yace: saniya, sai aka bashi saniya mai ciki. Yace Allah yayi maka albarka a cikinta.

Sannan yajewa mai Makaho yace: wane abu kafi so? Yace: Allah ya dawo min da ganina, na dinga ganin mutane da shi, sai ya shafe shi Allah ya dawo masa da ganinsa, yace: wane dukiya kafi so? Yace Dabbobi, sai aka bashi akuya mai haihuwa. Sai wadancan suka haifu wannan ma ta haihu. Ya zama wannan yana da shinge na rakuma, wannan yana shinge na shanu wannan kuma yana da shinge na dabbobi.

Sannan yaje wajen kuturu a irin tsohuwar-siffarsa-ta kuturta da kuma kamar sa yace: mutum ne miskini, guzuri ya yanke min a tafiya ta. Yau bani da isuwa sai dai ga Allah sannan kuma kai. Ina rokon ka dan wanda ya baka launi mai kyau da kuma fata mai kyau da kuma dukiya, ka bani rakumi da zanyi guzuri da shi a cikin tafiyata. Sai yace: Ai hakkoki suna da yawa. Sai mala'ikan yace: kamar na sanka, ba kaine kuturu ba da mutane suke kazantaka saboda talauci ba? Sai Allah ya baka? Sai yace A'a na gaji wannan dukiya ne iyaye da kakanni, sai mala'ikan yace: idan karya kake Allah ya mayar da kai yadda kake da.

Sai yaje wajen mai kora a cikin surarsa da kuma kamarsa, ya fada masa irin abin da ya fadawa wancan, shima ya mayar masa irin abin da dayan ya mayar masa, sai mala'ikan yace: idan karya kake Allah ya mayar da kai yadda kake da.

Sai yaje wajen makaho, a surarsa da kamarsa yace: Mutum ne miskini, kuma dan tafarki, guzuri ya yanke min a cikin tafiya, yau bani da isuwa idan bada Allah ba sai kuma kai. Ina rokonka dan wanda ya dawo maka da ganinka, ka bani akuya nayi guzuri da ita a cikin tafiya ta? Sai makaho yace: Hakika na kasance makaho sai Allah ya dawo mini da ganina, dauki abun da kaso daga akuyoyin nan ka bar abin da kaso. Na rantse da Allah yau bazan takura maka ba a cikin abin da ka dauka don zatin Allah ta'ala. sai Mala'ikan yace: Rike dukiyarka, hakika Allah ya jarrabeku ne, kuma Allah ya yarda da kai, ya kuma yi fushi da abokanka, (Bukhari/Muslim).

Mai Karatu wane darasi ka koya a cikin wannan Hadith din