Friday, 8 February 2013

YAN MATAN FACEBOOK
Hausawa suna cewa ‘Yammata adon gari, In ba ku ba gida, In kun yi yawa….. .Annabi (S.A.W) ya na cewa: “ Mata warin takalmin ‘ya’ya Maza ne” Alqur’ani mai girma kuma yace: “Su sutura ne gareku(maza) kuma sutura ne gare su(mata)”

Lalle Allah ya halitta Mata cikin son kawa da kwalliya, kamar yadda hakan ba haramun ba ne, matukar ana cancada adon ne cikin iyakar Musulunci.

Daga cikin abubuwan da suke ba ni mamaki a wannan dandali akwai yadda na ke ganin ‘yan mata ke saka hotunansu tsirara don Mutane su kalla suji dadi ba tare da sun biya sadaki ba, abin ban mamakin ma har da wasuu daga cikin matan aure. Amma abin tambaya anan shine: wai me ke jawo wannan hali na rashin kunya da yakamata ne?. Tsammani na, abubuwan da ke jawo hakan:
• Wassu ba su san cewa hakan Harmun ba ne.
• Wassu kuma tallen kai ne.
• Wassu kuma fitsara ce zalla!!
• Wassu kuma gaurin gwauranta ne.
• Wassu kuma wasa da Nishadi ne.
• Wassu kuma ban sani ba!!

Allah madaukakin sarki a cikin Littafinsa ya umarci Mata su rufe jikkunansu da tufafi, ka da su baiyyana adonsu sai ga Mazajensu ko Muharramansu. Kamar yadda Allah ya kira irin wadannan shiga da sunnan fita irin ta Jahilyyar farko. Me wannan hali inji Allah Jahila ce!!!

In ka tambayi Maza, ko za ku iya aurar irin wadannan matan? Sai ka ji sun ce maka: Allah sauwaka!! Dalilinsu wai bayan kowa ya san komai nata!!!

Manzon Allah yace: “ Wanda ba ya damuwa da wa zai shiga kan Matarsa, ba zai shiga Aljanna ba” Tirkashi!! Ina ga wadda ta ke tallata kanta wa duniya baki daya???

Wadanda su ke ganin saboda kirar da Allah yai musu, ba wanda zai gani bai hadiyi yawu ba, sai muce: Manzon Allah yace: “ Akwai wassu ‘yan Wutan da babu su a zamanina, cikinsu akwai: “Mata ma su shigar tsirara, ko sun sa tufafi jikinsu a baiyyane ya ke, sun karkace suna kokarin karkatar da mutane, Ba za su shiga Aljanna ba, kamshin ta ma, ba za su ji ba” Allah ka raba mu da wannan rashin rabo!! Ameen

Rashin Aure ya ke sa Wassu shiga wannan sana’a, don ragewa kai gauri da gaunin Tuzurunta ka, Maganin wannan karbar Sunnar Manzo ta hanyar Aure. Wanda ya sanki ‘ya mace ba zai aure ki ba, in kuma ya aura. Ba za ki yi kima a idanunsa ba,har Abada. Tsalle daya shi ke jefa mutum Rijiya.

Ya ‘Yar uwata ki rasa abin wasa da shi, sai Mutuncinki da na ‘yayanki, Allah ya halasta wassu wasanni, ya kuma sanya cikekkiyar nutsuwa cikin karatun Alqur’ani. Balle uwa Uba wasan miji da mata, Ki sumbace shi, a baki lada, ki fada masa magana mai dadi ki samu lada, Dukkan abin da zakiyiwa mijinki na kyautatawa lada, Balle uwa uba…

Cikin Mata akwai kamammu ko nan cikin Facebook, adadinsu kuma kara yawa ya ke, Wannan yasa na rubuta wannan makala don ‘Yar uwa kada jirgin Annabi nuhu ya ta shi ban da ke ciki.
Annabi Mai tsira da aminci yace: ‘’WANDA YA TUBA DAGA LAIFI KAMAR WANDA BAI TABA YIN LEFIN NE BA”
‘Ya Allah ka tsare mana Kannanmu da Yayan Musulmai. AMEEEEEEEEEEEEEEEEEEEEEEEEEEEN

No comments: