Friday, 8 February 2013


Daga Abi Hurairah Allah ya yarda da shi: yaji Annabi mai tsira da aminci yana cewa: "Hakika akwai mutane uku daga cikin bani isra'ila: kuturu da maikora da makaho, Allah yayi nufin ya jarrabesu, sai ya aika musu da mala'ika. Sai yaje wajen kuturu yace: Wane abu ne mafi soyuwa a gareka?sai yace: launi mai kyau, da fata mai kyau ya kuma tafiyar min da abinda mutane suka kazantani da shi. Sai Mala'ika ya shafe shi, kazantar tasa ta tafi, kuma aka bashi launi mai kyau da kuma fata mai kyau. Sai Mala'ika yace: wace dukiya ce mafi soyuwa a gareka? Yace rakuma, ko kuma yace saniya-Mai ruwayar yayi kokwanto. Sai dai cewa kuturu ko mai kora baya daga cikin su yace: Rakuma, dayan kuma yace shanu, sai aka bashi taguwa da mai ciki- Yace: Allah yayi maka albarka a cikinta.

Sai kuma yajewa mai kora yace: Menene mafi soyuwa a gareka? Yace gashi mai kyau, kuma abinnan da mutane suka kazantani da shi ya tafi sai ya shafa shi, kazantar ta tafi daga gare shi. Kuma aka bashi gashi mai kyau, yace: wace dukiya kafi so? Yace: saniya, sai aka bashi saniya mai ciki. Yace Allah yayi maka albarka a cikinta.

Sannan yajewa mai Makaho yace: wane abu kafi so? Yace: Allah ya dawo min da ganina, na dinga ganin mutane da shi, sai ya shafe shi Allah ya dawo masa da ganinsa, yace: wane dukiya kafi so? Yace Dabbobi, sai aka bashi akuya mai haihuwa. Sai wadancan suka haifu wannan ma ta haihu. Ya zama wannan yana da shinge na rakuma, wannan yana shinge na shanu wannan kuma yana da shinge na dabbobi.

Sannan yaje wajen kuturu a irin tsohuwar-siffarsa-ta kuturta da kuma kamar sa yace: mutum ne miskini, guzuri ya yanke min a tafiya ta. Yau bani da isuwa sai dai ga Allah sannan kuma kai. Ina rokon ka dan wanda ya baka launi mai kyau da kuma fata mai kyau da kuma dukiya, ka bani rakumi da zanyi guzuri da shi a cikin tafiyata. Sai yace: Ai hakkoki suna da yawa. Sai mala'ikan yace: kamar na sanka, ba kaine kuturu ba da mutane suke kazantaka saboda talauci ba? Sai Allah ya baka? Sai yace A'a na gaji wannan dukiya ne iyaye da kakanni, sai mala'ikan yace: idan karya kake Allah ya mayar da kai yadda kake da.

Sai yaje wajen mai kora a cikin surarsa da kuma kamarsa, ya fada masa irin abin da ya fadawa wancan, shima ya mayar masa irin abin da dayan ya mayar masa, sai mala'ikan yace: idan karya kake Allah ya mayar da kai yadda kake da.

Sai yaje wajen makaho, a surarsa da kamarsa yace: Mutum ne miskini, kuma dan tafarki, guzuri ya yanke min a cikin tafiya, yau bani da isuwa idan bada Allah ba sai kuma kai. Ina rokonka dan wanda ya dawo maka da ganinka, ka bani akuya nayi guzuri da ita a cikin tafiya ta? Sai makaho yace: Hakika na kasance makaho sai Allah ya dawo mini da ganina, dauki abun da kaso daga akuyoyin nan ka bar abin da kaso. Na rantse da Allah yau bazan takura maka ba a cikin abin da ka dauka don zatin Allah ta'ala. sai Mala'ikan yace: Rike dukiyarka, hakika Allah ya jarrabeku ne, kuma Allah ya yarda da kai, ya kuma yi fushi da abokanka, (Bukhari/Muslim).

Mai Karatu wane darasi ka koya a cikin wannan Hadith din

No comments: