Malam menene hukuncin wanda yayi amfani
da matar da take idda bata cika ba??? (daga Yakubu Adamu) AMSA
*****
Salam.. To Mal ba ka bambance ba.
(baka fito da tambayar taka afili ba). Shin matarsa ce wacce ya saki, sannan yaje
ya sadu da ita kafin cikar iddar ta?? Shin ba shine ya sake ta ba, amma Saduwar
da yayi da ita, ahalin aure aka daura musu
kafin iddarta ta cika?? Ko kuwa kawai yaje yayi zina da ita ne?? * idan ta hanyar Aure ne wanda aka daura
alhali matar tana cikin idda,To nan ma akwai
maganganu guda biyu. * Shin ya san cewa iddar tata bata Qare ba? * ko kuwa be sani ba?? Idan da saninsa ya auri matar da take cikin
idda, to za'a 'bata auren. Sannan a ladabtar
dashi.
Amma babu haddi akansa. * idan kuwa acikin rashin sani ne, duk da
haka za'a raba auren. Kuma laifin yana kan ita
matar da kuma waliyyanta.
Idan kuwa ya sadu da ita ne ba ta hanyar
aure ba, to ai bashi da bambanci da sauran
mazinata. Idan saurayi ne, kuma shaidu sun tabbata, ko
kuma yayi Iqiqrari da kansa, to shari'a za'tayi
masa bulala Dari chif. Idan kuwa ya taba yin aure, kuma shaidu sun
tabbata, ko kuma yayi Iqrari da kansa, to
hukuncin rajamu ne. (wato jefe shi za'ayi). Ita ma matar haka.. Amma duk wannan fa hukuma ce take da
dama da kuma ikon aiwatarwa. Sannan kuma
akwai Qarin bayanai masu yawa.. * Idan kuwa matarsa ce, shi ya saketa,
Sannan kuma yaje ya sadu da ita kafin cikar
iddarta, to shikenan ya maida ita kenan
Automatically. (ta sake komawa matarsa
kenan) don karin bayani aduba Subulus-Salam
sharhin bulughul-Maram, Kitabut-Talaaq.
Wallahu a'alam
No comments:
Post a Comment