Friday, 8 February 2013
ANNABI MUHAMMAD (SAW), YACE; KAFADI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU...Yan'uwa a musulunci yana da kyau kwarai da gaske mu dinga fadin alkhairi a dukkan harkokinmu, kuma ina dada tunatar damu cewa duk abin da zamu furta akwai Mala'iku guda biyu suna rubutuwa, ranar gobe kiyama Allah zai tambayemu, sannan akwai masu raddi idan wasu sunyi magana marar dadi a gareni, ina dada tunatar daku cewa duk inda mai da'...awa yake tun lokacin Annabawa idan kun duba zaku ga yana fama da abokan gaba, a cikin musulmi ko wadanda ba musulmi ba, ni daku duka in an zagi Annabi nasan sai inda karfinmu ya kare, amma duk lokacin da aka zagi mai da'awa babu ruwan ahlus sunnah da yin raddi, dan haka mu kula da wannan, shi ahlus sunnah baya yin fushi, shi kullum fatan shi a fahimci kiran da yakeyi, Allah yasa mu gane amin.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment