Friday, 8 February 2013

MATSAYIN MATA DA MIJI A RAYUWAR AURE!

Mace itace jigon kyakkyawan gida, ita ke kula da jin dadin mijinta da renon yayansu da kuma tattalin dukiya da mutuncin mijinta, Aure baya yiwuwa sai da miji da mata, saboda haka matsayin mata a gidan miji yana da matukar muhimmanci. Kowa daga cikin su kuwa yana da irin aikin da Allah ya dora masa. An karbo Hadithi daga Dan Umar, daga Manzon Allah mai tsira da aminci yace " Dukkaninku masu kiwa ne, kuma za'a tambayi kowannen ku bisa abin da aka bashi kiwo. Shugaba mai kiwo ne (Bisa abin da yake kiwatawa)
Namiji mai kiwo ne bisa mutanen gidansa, mace mai kiwo ne bisa gidan mijinta da yaran su.
Dan haka dukkan ku masu kiwo ne kuma za'a tambayi ko wannen ku bisa abin da aka dorawa kiwon sa. (BUKHARI/MUSLIM).
Wannan Hadithi ya nuna muhimmancin abin da maigida ya tanada a cikin gida da kuma yaran su bisa ga mata

No comments: