Malam menene hukuncin mutum yasa matar da zai aura ta kwabe hijabinta don yaga kwalliyarta??
(daga Murtala Y.D. kazaure)
AMSA
*****
A'A BAI HALATTA BA. Domin kuwa ya zarce iyaka.
Wajen da aka yarda mutum ya kalla ajikin matar da zai aura sune : FUSKA DA KUMA TAFIN HANNU.
Sune guraren da Annabi (saww) yayi umurnin mu kalla ajikinsu.
Amma sanyata ta kwabe Hijabi, wannan ya sabawa shari'a domin kuwa ba ya halatta mutum ya kalli duk wata kwalliya da mace zata yi sai dai in yana cikin muharraman ta. (kamar yazo acikin Suratun-Nuur).
Sannan kuma kallonta haka tsura ba tare da Hijabi ba, daga shi sai ita, zai iya haifar da fitina atsakaninsu.
Domin kuwa idan sha'awarsu ta motsa, komai zai iya faruwa. Kuma ayoyi da hadisai da dama sunzo akan umurnin cewar mu rintse idanuwanmu daga Kallo irin na haram.
(Wallahu A'alam)
No comments:
Post a Comment