DAWAINIYAR DA MACE YA KAMATA TA YIWA MIJINTA.
Matar aure ta zamanto mai mutunta aure saboda zaman gidan miji shine rufin asiri da cikar daraja gareta. Kula da hakkokin aure ga mace shine asirin jin dadin rayuwar aure da zaman lafiya a tsakanin ma'aurata saboda haka wajibi ne mace ta kula da hakkokin da kanta dan dan ingantuwar zaman aure.
1- Ya zamo mace na yiwa miji biyayya sau da kafa cikin abin da bai sabawa dokar Allah ba.
Wajibi ne Mace tabi umurnin mijinta ta hanyar Aikata abin da ya sata da barin abin da ya hanata cikin girmamawa da nuna yarda.
Kamar yadda zaki yiwa mahaifinki biyayya cikin abin da suka umarceki, hakama wajibi ne kiwa mijinki biyayya, koma fiye da haka.
Ankarbo Hadithi daga Aisha tace. Na tambayi manzon Allah mai tsira da aminci wane mutum ne yafi (girma) Hakki akan mace? Sai manzon Allah mai tsira da aminci yace Mijinta (Bazzar).
2-Mace tilas ne ta lura da dukiyar mijinta ta hanyar tattalin abin daya bata da kiyaye abubuwan daya tanada dan rayuwar yau da kullum.
Yin almobazzaranci ko wulakanta dukiyar miji na jawo bacin rai ga mai gida sannan ga tsoron hushin Allah. Domin Allah madaukakin sarki yana cewa "Lallai ne mubazzirai sun kasance 'yan uwan Shaidan, kuma shi shaidan ya kasance mai yawan kafirci ne (Suratul Isra'i :27)
3-Mace ta zauna a gidan mijinta baza ta fita ba sai da izinin sa, koda gidan mahaifinta ne. Ta kare kanta daga mazajen da ba nata ba ta hanyar gujewa magana dasu ko matsanan cin kallo da dai sauran abubuwan da ya saba da shari'a. Mace ta guji fidda halittar ta ko caba ado da turare mai kamshi lokacin da lalura ya sanya zata fita daga gidanta. Mafi yawan mata basu tashi ado da sa kaya masu dauke hankali sai zasu fita unguwa. Wannan mummunan dabi'a ne da yake yada alfasha a bayan kasa. Allah madaukkin Sarki yana cewa "Kuma kuce wa muminai mata su runtse daga ganin su, kuma su tsare farjojinsu, kuma kada su bayyana daga gareta, kuma su doka da mayafansu akan wuyan rigunan su, kuma kada su nuna kawarsu face ga mazansu ko ubanninsu...............Suratu
4-Mace ta zamo mai tsoron Allah ta yadda zata kaunaci rahaman Allah a lahira maimakon bin tafarkin bokanci ko sihiri don a mallake miji; ko korar kishiya. Zuwa wurin boka, tare da gaskata shi masiba ce mai tsanani dake halakar da mai yinta.
Annabi mai tsira da amincin Allah yace "Wanda yazo ga boka, kuma ya gaskata shi game da abinda yake fada, hakika ya kafircewa abin da aka saukarwa Annabi Muhammad mai tsira da aminci. (Muslim).
Hakika Nana Safiyya RA (Matar Annabi mai tsira da aminci) tace: Annabi Mai tsira da aminci yace; "Wanda yazo ga mai duba, kuma ya tambaya daga wani abu, to ba'a karba masa sallar sa ba har kwana arba'in 40 (Muslim).
"Yan uwa mata ku nisanci bin wannan kazamin hanya mai tabarwa don gujewa azabar Allah da kwadayin rahamar sa.
Hakuri Biyayya kyautatawa, soyayya, tsafta, soyayya agazawa da sauran dabi'u masu kyawu suke kawo zaman lafiya tsakanin ma'aurata ko kishiyoyi ba shaidanin boka ba. (Allah ya b
No comments:
Post a Comment