Friday, 8 February 2013

KWALLIYAR MATA A MAHANGAR MUSULUNCI (female only)

Sakon da Annabi Muhd (S.A.W) ya zo da shi, bai takaitu kan alaka tsakanin bawa da ubangijinsa ba kawai, ya tsallaka har zuwa ga yadda bawa zai kula da gangar jikinsa da kuma yadda zai gudanar da zamantakewa da sauran halittun Duniya.

Mata sune Allah ya bada shaida a kansu cewa: An gina dabi’arsu kan son kawa an kuma tayar da su a cikinta, sannan kuma Musulunci ya karfafi mabiyansa kan cancada ado yayin zuwa masallaci, ya kuma tuhumci wanda yake tsammanin cewa ba dabi’ace ta mumunai ba. Allah yace: “ KA CE:

WANENE YA HARAMTA KAWAR(kwalliya) DA ALLAH YA FITARWA BAYINSA”
Manzon Allah kuma ya karfafi haka cikin Hadisansa yace: ‘’ Allah mai kyau ne, yana son Abu mai kyau”.
Abdullahi dan Abbas ya na cewa: “ Na kasance ina cancada ado wa matata kamar yadda take cancada min”.
Musulunci shine addinin da ya sanya wanka da kawar da kazanta daga jikin musulmi a matsayin ibada, kamar su; yanke kumba, tsige gashin hammata, aske gashin gaba, tsabtace hakora{Aswaki},balle sanya turare, shafa mai dss.

Amma musulunci bai bar wannan Ibada kara zube ba, sai da ya sanyawa ‘yan uwa Mata wassu ka’idoji a matsayin yanda ya kamata su gudanar da ita.
‘Yar uwata, Duk da cewa kwlliya addini ne amma sai a ringa kulawa da wadannan abubuwa:

• Kada kwalliyarki tai kama da na Matan Arna, don Manzon Allah yace:” wanda yai kama da wassu yana tare da su.”
• Kar kiyi kwalliyar da za mai da ke kamar Maza. Manzon Allah yace: “Allah ya tsinewa mai kama da Maza cikin Mata”.
• Kar Kwalliyar ta kunshi canja halittar Allah, kamar kulla gashinki da wani gashi, ko kuma canza fatar jikinki, ko kuma bankare tsakanin hakoranki don fitar da wushirya ko kuma yin zane a fuska ko a wani bangare na jikinki. Amma gyara halittar da Allah yai miki ba Laifi, kamar sa gashi ya yi santsi, ko mikar dashi, ko sa masa abinda zai kara tofar da shi.
• Kada ya zamanto cikinkin kwalliyar akwai barnatar da dukiya, Allah yace: “ ku ci ku sha, kar ku barnatar da dukiya, Allah ba ya son masu Ballagaza”
• Kar ya zamanto akwai bata lokaci, Ta yanda mafi yawan lokacinki zai tafi ne cikin kwalliya.
• Kada wannan kwalliyar ta zamanto tana kunshe da cutarwa wa jikinki, domin jikinki yana da hakki a kanki, wannan cutarwar yanzu yanzu ne ko kuma sai daga baya.
• Kar ya zama cikin kayan da aka kera wannan abin kwalliyar yana kunshe da najasa.
• Wanda kike fatar kwalliyar ta burgeshi ya zamanto mjinki, ba ki ringa rabawa Jama’a kirarki fi sabilil Shaidan ba.

Nana A’sha ta kasance tana da kayayyaki na musamman da take cabawa Manzon Allah ado dashi, kamar yadda Manzon Allah yace cikin ingantaccen hadisi: “ Duk wanda Allah ya bashi gashi ya kula dashi” Tirmizi cikin Shama’ilil Muhammadiyya.

Zan rufe da Hadisin da ke cewa:
“INA JAWO HANKALINKU DA SANYA TOZALIN ISMID LOKACIN BARCI, DOMIN YANA KARA GANI YANA 

No comments: