Monday, 25 February 2013



Bismillahir Rahmanr Rahim
Ya ku bayin Allah!
Ba wata da'a ko ibada ko aikin lada da Allah madaukakin sarki ya ba shi muhimmanci a cikin Alkur'ani - bayan kadaita Allah - kamar yadda ya bada muhimmanci ga da'ar iyaye.
قال تعالى: (واعبدوا الله ولا تشركوا به شيئاً وبالوالدين إحساناً).النساء­:36
Da'ar iyaye na nufin bayyana son su, da darajanta su, da kiyaye alfarmarsu, da kauce ma fushinsu da biyan bukatarsu.
Idan mutum ya yi nazarin wahalar da iyaye suka sha wajen tashinsa da daure ma kuruciyarsa har zuwa sadda zai yi hankali shi kadai ya isa ya nuna masa girman hakkensu a kan sa. To, ina ga kuma an duba alhakin uwa na daukar ciki wata tara tsakanin lafiya da ciwo, laulayi da haraswa, da kyamar abinci da raunin jiki da nauyin ciki har zuwa ga nakuda wadda wata 'yar karamar lahira ce mata suke zuwa a mafi yawan lokuta!
Annabawa sun kasance masu tsananin biyayya ga iyayensu:
- Isma'il da mahaifinsa Ibrahim sun gina ka'aba
فلما بلغ معه السعي ..
وإذ يرفع إبراهيم القواعد
- Isa (AS):
وبرا بوالدتي ولم يجعلني جبارا شقيا
- Ibrahim (AS):
يا أبت إني أخاف أن يمسك عذاب من الرحمن... يا أبت ... يا أبت
- Nuhu (AS):
رب اغفر لي ولوالدي ولمن دخل بيتي مؤمنا...
Annabi SAWW ya nuna mana muhimmancin uwaye da da'arsu a cikin hadisai da dama:
1. Yardar Allah tana tare da yardar iyaye:
عن عبد الله بن عمرو رضي الله عنه قال صلى الله عليه وسلم ( رضا الرب في رضا الوالدين وسخطه في سخطهما ) رواه الطبراني وصححه الألباني. رقم: 3507 في صحيح الجامع.
2. Da'ar iyaye na daukaka matsayin mutum a aljanna:
عن عائشة أم المؤمنين رضي الله عنه قال رسول الله صلى الله عليه وسلم
( دخلت الجنة فسمعت فيها قراءة قلت من هذا ؟ فقالوا : حارثة بن النعمان ) فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم ( كذلكم البر كذلكم البر [ وكان أبر الناس بأمه ] )
صححه الحاكم ووافه الذهبي والألباني. راجع: السلسلة الصحيحة برقم 913 ، صحيح الجامع برقم 3371 ، مشكاة المصابيح برقم 4854
3. Da'ar iyaye tana gaba da jihadi in ba ya zama fardu aini ba.
عن عبد الله بن مسعود رضي الله عنه قال: سألت النبي صلى الله عليه وسلم أي العمل أحب إلى الله عز وجل؟ قال: ( الصلاة على وقتها) قال: ثم أي؟ قال: ( بر الوالدين ) قال ثم أي؟ قال: ( الجهاد في سبيل الله ) رواه البخاري ــ كتاب مواقيت الصلاة برقم 496
4. Uwa tana da wani karin fifiko saboda karin wahalarta wajen ciki da nakuda da shayarwa da reno.
روى البخاري ومسلم عن أبي هريرة – رضي الله عنه – أن رجلا قال : يا رسول الله من أحق الناس بحسن صحابتي ؟ قال : " أمك " قال : ثم من ؟ قال : " أمك " قال : ثم من ؟ قال : " أمك " قال : ثم من ؟ قال : " ثم أبوك " .
Ya ku bayin Allah!
Addinin musulunci ya wajabta mana kyautata ma iyayenmu a matsayin wani dan tukuici ga kokarin da suka yi mana sadda babu wanda zai yi mana in ba su ba. Ba a matsayin biyan hakki ba. Wani mutum ya hadu da sayyidina Umar a lokacin shi mutumin yana dauke da mahaifiyarsa yana dawafi da ita. Sai ya ce ma Umar: kana ganin ban bata hakkinta ba? Sai sayyidina Umar ya kalle shi, ya ce: a lokacin da take daukar ka fatar take yi ka rayu. A yanzu kai kuma jira kake yi ta mutu!!
Hakken iyaye bai kadaita kawai ga iyaye musulmi ba.
فعن أسماء بنت أبي بكر الصديق رضي الله عنهما ، قالت: قَدِمَتْ عليّ أمي وهي مشركة في عهد رسول الله صلى الله عليه وسلم، فاستفتيت رسول الله صلى الله عليه وسلم قلت: قَدِمَتْ عليّ أمي وهي راغبة أفأصل أمي؟ قال: ((نعم، صلي أمك)) متفق عليه.
Kai, ba wai zaman su kafirai ba, koda suna iya kokarinsu don su kafirtar da kai. Hakken da'a da kyautatawa gare su yana nan in ji Allah:
(وإن جاهداك على أن تشرك بي ما ليس لك به علم فلا تطعهما وصاحبهما في الدنيا معروفا واتبع سبيل من أناب إلي ثم إلي مرجعكم فأنبئكم بما كنتم تعملون) لقمان 14-15

Ya ku al'ummar musulmi! mu gode ma Allah da ya sa mu cikin inwar addinin musulunci da karantarwarsa mikakkiya. Daga cikin abinda bature ke fama da shi a yau mai tada hankali akwai tanadin da kowane mutum yake bukatar yi a can don tsufansa. Dole ne mutum ya tara wasu makudan kudade da zasu amfane shi idan ya tsufa. Don me? Don babu wanda zai kula da shi a wannan lokaci. In ba haka ba kuwa lalle ne zai kare rayuwarsa a gidan nakasassu da gajiyayyu wanda gwamnati ta tanada wanda kuma ba shi da banbanci da zaman fursuna a kurkuku. A lokacin 'ya'yansa maza da mata na can suna soyayya da abokai da kawayensu ba wanda ya damu da shi.
A kasashen turawa akwai kowace doka har da ta hakken karnuka amma babu wata doka akan hakken uwaye. Don me? Don wai kada a takura ma 'ya'ya! Za a shiga cikin 'yancinsu!!
Musulunci ya banbantar da 'ya'yansa da irin wannan karantarwa ta Alkur'ani da Sunnah da muka gabatar. Wata likita ta bada labarin biyayya mai ban mamaki. Tsohuwa ce wawiya da ba a haife ta ma da hankali ba. Danta ya zo da ita yana mai tsananin kula da ita. Ba ya son kome ya same ta. Saboda mamakin irin kulawarsa gare ta wannan likita ta tambaye shi, kuma ya sanar da ita cewa tun a tashin ta tana da tabuwar hankali kuma bata san abinda take yi ba. An aurar da ita ga mahaifinsa bayan ta samu cikinsa sai mahaifin ya kasa hakura da zama da ita. Tashin hankalin da wannan matar ta shiga shine, shi wannan ya kula da uwar da cikinsa kawai ta dauka bata san wahalarsa kowace iri ba yana ta tarainiya da ita haka.. To, mu da iyayenmu suka sha kowace irin wahala a kanmu ya zamu yi kenan?!
A cikin tarihin magabata akwai labarai masu kayatarwa game da bin wannan umurni na ubangiji.
1. Mis'ar bin Kidam (RH) ya taba kawo ma mahaifiyarsa ruwa bayan ta nemi haka amma ko da ya zo ta yi bacci. Sai ya tsaya har gari ya waye bai tashe ta ba kuma bai tafiyarsa ba.
2. Muhammad bin Al-Munkadir ya ce, na kwana ina murza kafar mahaifiyata don ta ji dadin bacci, kanena kuma ya kwana yana sallah. Ba zan yi fatar ayi mana musayar lada ni da shi ba.
3. Sayyidina Abu Huraira (RA) ya ga wani mutum yana tafiya bayan wani dattijo. Sai ya tambaye shi, wane ne? Ya ce, mahaifina. Sai ya ce: kada ka kira shi da sunansa, kada ka zauna kafin sa, kuma kada kayi tafiya a gabansa.
Bayan haka ya kai dan uwa musulmi! Ka sani ba wani laifi a wurin Allah wanda yake gaggauta kama mai yinsa, ya debe masa albarka, ya barkata masa rayuwa tun a nan duniya kamar cuta ma iyaye.
Sai ka ga mutum ya damu da matarsa, ya kula da 'ya'yansa amma bai ko san halin da mahaifiyarsa take ciki ba. Wani kuma yana cikin ni'ima da jin dadin duniya iri-iri amma yana nan birni yana ma-sha'a mahaifinsa ko na can kauye yana fama da nikar gero da dawa. Ko ka tarar da ya gina babban gida, yana hawan manyan ababen hawa amma mahaifiyarsa na cikin rubabben wuri kuma N100 suna ba ta shawa.
Mu gyara ya ku al'ummar musulmi.
Ga wasu shawarwari guda (20), duk mutumin da Allah ya albarkace shi da rayuwa tare da dayan mahaifansa ko dukansu ya kamata ya rike su:
1. Ka yi masu biyayya da da'a ga duk abinda suke so in bai saba ma Allah ba. Kuma duk abinda kake idan sun kira ka ka karba.
2. Ka nisanci duk abinda zai husata su ko ya tunzura su
3. Ka tsare mutuncinsu da girmansu a idon jama'a.
4. Yi kokari kayi duk abinda ka san yana faranta ransu koda ba su sa ka ba.
5. Ka karba kiransu cikin murmushi, ka je zuwa aikin da suka sa ka cikin nashadi.
6. Kada ka yi jayayya da su koda a cikin maganarsu ba su da gaskiya. A maimakon haka ka samu wani lokaci daban na lurar da su kuskurensu a cikin ladabi da hikima.
7. Ka saurare su idan suna magana kuma kada ka daga musu murya.
8. Ka tanye su aiki koda ba su neme ka ba.
9. Idan dayansu ba shi da lafiya ka himmatu wajen jinyarsa da kanka. Kome kake yi ka tabbata ka ware masu lokaci a cikin wannan hali. Kada ka ce aiki ya yi min yawa. Ka kaddara ciwon a kanka ne ya fada. Zaka ba shi lokaci ko shagali zai dauke ka?!
10. Bayyana ladabi gare su ko a wurin zama ko wurin tafiya. Kada ka saki jiki ko ka mike kafafu ko ka haura sama da su ko ka yi tafiya gabansu ta yadda zasu ji lalle ba su da wani matsayi na girmamawa gurin ka.
11. Kada ka taba damuwa ko jin ciwon bayyana cewa uwayenka ne. Kayi alfahari da su koda ba su da wata daukaka wadda ake kuri da ita.
12. Kada ka bari bukata ta kama su har su kai ga rokonka. Ka wadata su gwargwado da abinda zasu ji dadin rayuwa har su taimaki wani matukar kana da iko.
13. Nuna kulawa da su ta fuskar ziyara koda a wuri daya kuke. Idan kuma ba a wuri daya kuke ba to ka ware wani lokaci da zaka rinka tuntubar su, kana ziyartar su, kana samun lokacin fira da su, kana sauraren kokensu da biyan bukatarsu.
14. Rinka nuna masu godiya, da cewa duk abinda ka yi masu ba ka biya su ba a kan renonka da suka yi. Allah Ta'ala ya ce:
((أَنِ اشْكُرْ لِي وَلِوَالِدَيْكَ إِلَيّ الْمَصِيرُ)) لقمان:14
15. Kada ka bukace su da abinda ba su son ba ka. Idan kuma sun ba ka kayi godiya kamar ba a taba ba ka abinda ka ji dadi kamar nasu ba.
16. Kada ka fifita iyalanka ko 'ya'yanka a kan su.
17. ka boye masu mafi yawan kyautatawar da ke tsakaninka da iyalanka domin gudun shedan ya sa masu kishi a kan wannan.
18. Idan rashin jituwa ta shiga tsakanin su da iyalinka kada ka taba goyon bayan iyalinka a fili koda su ke da gaskiya. Sai dai ka lurar da su a asirce cewa, suna da gaskiya amma matsayin mahaifa abu ne ba na wasa ba.
19. Rinka neman addua a gurinsu kana fada masu bukatunka tare da sanar da su cewa, addu'arsu ta fi ta kowa kima da saurin karbuwa a wurin Allah.
عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال النبي صلى الله عليه وسلم: "ثلاث دعوات مستجابات لهن، لا شك فيهن، دعوة المظلوم، ودعوة المسافر، ودعوة الوالدين على ولديهما".
20. Kada ka taba yarda ka ja ma su zagi. Annabi SAWW yana cewa: "Yana daga cikin mafi girman kaba'irai mutum ya la'anci iyayensa. Aka ce, ya manzon Allah! Ya haka zata faru? Ya ce, zai zagi uban wani sai a zagi nasa. Ko ya zagi uwar wani sai a zagi tasa".
Bayan haka. Ya kai wanda Allah bai nufe shi da rayuwa da uwa ko uba ba. Ko kuma ka riga ka yi sakaci har sun wuce ba ka ba su hakkensu ba. Kada ka samu damuwa. Ko yanzu akwai yadda zaka yi:
1. Yawaita yin addu'a gare su da neman gafarar Allah. Babu laifi ka yi sadaka don neman masu gafara da sassauci daga ubangiji. Haka kuma ya halalta ka ziyarci kabarinsu don kayi masu addu'a ta fatar samun dausayi a cikin kabarinsu.
2. Ka zartar da duk wani abinda suka yi wasici da shi. Idan babu ka duba abinda suke sha'awa da duk wani abin da ka san suna jin dadin aikata shi na alheri musamman wanda ya shafi kyautata ma mutane, sai ka aikata shi.
3. Ka sada zumunci da yan uwansu da danginsu da masoyansu, kuma ka bi su gaba daya da kyautatawa.
Daga karshe..
Ka sani, duk yadda ka yi haka za ayi ma. "Kama tadinu tudanu.."
Uwaye kuma zasu iya taimakon dansu wajen yi masu da'a idan suna lallabawa da shi, suna tausaya masa, suna sa masa albarka. Kuma babu shakka addu'ar iyaye tana da babban tasiri ga shiriyar 'ya'ya da sa suyi albarka wadda iyayen su ne farkon masu cin moriyarta.
Allah ya yi mana albarka. Ya gafarta ma iyayenmu da suka riga mu. Wadanda muke tare da su Allah ya bamu ikon yin biyayya da kyautatawa gare su. Allah ya yi ma 'ya'yanmu albarka, ya sa su zama masu biyayya gare mu.
عباد الله،
-(إِنَّ اللَّهَ وَمَلَائِكَـتَهُ يُصَلُّونَ عَلَى النَّبِيِّ يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا صَلُّوا عَلَيْهِ وَسَـلِّمُوا تَسْـلِيمًا)- [الأحزاب/56].
وأكثروا عليه من الصلاة يعظم لكم ربكم بها أجـرا. فقد قال صلى الله عليه وسـلم : «مَنْ صَلَّى عَلَىَّ صَلاَةً صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ بِهَا عَشْـرًا».
اللهم صل وسـلم وبارك على عبدك ورسـولك نبينا محـمد صاحب الوجـه الأنور والجبين الأزهر، وارض اللهم عن الأربعة الخـلفاء أبي بكـر وعـمر وعـثمان وعـلي وعن سـائر أصحـاب نبيك أجمـعين، وعن التابعين ومن تبعهم بإحـسان إلى يوم الدين، وعنا معهم بعفوك ومنك وكرمك وإحـسانك يا أرحم الراحمـين.
اللهم أعز الإسـلام والمسـلمين، وأذل الشـرك والمشـركين، ودمر أعدائك أعداء الدين، وانصر عبادك الموحـدين، واحمي حـوزة الدين.
اللهم إنا نعوذ بك من شر اليهود والنصارى والرافضة، اللهم إنا نعوذ بك من شرورهم وندرأ بك اللهم في نحـورهم.
اللهم وآمنا في دورنا وأوطاننا وأصلح ووفق ولاة أمورنا، اللهم وأصلح قلوبهم وأعمالهم وسـددهم في أقوالهم وأفعالهم، واجمع شمـلهم وشمـل المسـلمين على الهدى يا رب العالمين.
ربنا آتنا في الدنيا حـسنة وفي آخـرة حـسنة وقنا عذاب النار.
اللهم اغـفر لنا، ولآبائنا ولأمهاتنا، ولأولادنا ولأزواجـنا، ولجـميع المسـلمين والمسـلمات، والمؤمنـين والمؤمنات الأحـياء منهم والأموات.
-(سُـبْحَانَ رَبِّكَ رَبِّ الْعِزَّةِ عَمَّا يَصِفُونَ (180) وَسَـلَامٌ عَلَى الْمُرْسَلِـينَ­(181)وَالْحَـمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِـينَ)- [الصافات/­180-182].
 — with Aliyu Said Gamawa and 4 others.

No comments: