Sunday, 24 February 2013


MALAM MENENE HUKUNCIN MUTUMIN DA YA TA'BA/YA SHAFI JIKIN MATARSA ALHALI SHI YANA DA ALWALA??
Malam shin alwalarsa tana nan? Ko ta karye??

AMSA
*****
Mazhabar Malikiyyah da Hambaliyyah da Kuma Imamul-Auza'iy sun tafi akan cewar in har mai alwala ya shafi jikin mace da niyyar jin dadi, da sha'awa, ko yaji dadin ko bai jiba, To alwalarsa ta karye.

Idan ma bai nufi jin dadin ba, amma kuma ya samu jin dadin, nan ma alwalarsa ta karye.
Idan kuwa bai nufi jin dadin ba, kuma bai ji dadin ba, to alwalarsa tana nan.

Amma Maz-habar Imam Abu Haneefah sunce alwalarsa ba ta Karye ba, sai dai in har wannan shafar ta sanya masa motsawar Sha'awarsa.

Amma Muhammad ibnul-Hasan (daga maluman Hanafiyya) yace alwalarsa tana nan koda Wannan shafar ta sanya mikewar azzakarin shi mai yin shafar.

Imam Sufyanuth thaury da kuma mutanen Kufah sunce KISS (SUMBA) ba ya karya alwala.

Sai dai Maz-habar Imamush-Shafi'iy sunce: alwalarsa ta karye abisa kowanne yanayi, sai dai idan muharramarsa ce, to alwalarsa tana nan..

ITA KUMA MATAR DA AKA SHAFA DIN MENENE HUKUNCINTA???

Imam Malik da Imamush-Shafi'iy da Imam Ahmad (Allah ya qara musu yardarsa) sunce Hukuncinta daya ne da mai yin shafar.

Hadisin da wasu suke kafa hujja dashi akan halascin shafar mace, ko kuma yi mata KISS BAI INGANTA BA.

Imam Ahmad ya fitar da Hadisin daga Nana A'isha (rta) cewar "MANZON ALLAH (SAW) YA SUMBANCI WATA DAGA CIKIN MATANSA, SANNAN YA FITA WAJEN SALLAH BA TARE DA YA SAKE ALWALA BA"..

"Imamul-Bukhary ya Raunana hadisin.. Yace bai inganta ba. Sannan Imamul baihaqiy ya fitar da hadisin ta hanyoyi guda goma. Amma yace dukkansu basu inganta ba.

Imam Ibnu Hazmin (yana daga cikin manyan maluman ilimin hadisi) shima yace Babu wani hadisi ingantacce dangane da wannan maganar. Yace idan ma an samu wani abu ya inganta, sai dai mudauke shi amatsayin anyi aikin ne kafin saukar ayar nan data yi magana akan sake alwala bayan shafar mace.

Shima Abu Dawud ya ruwaito shi.. Amma shima yace bai inganta ba.

Amma dangane da wani Hadisin kuma na Nana A'ishatu (rta) Na cikin Bukhary Wanda take cewa TA KASANCE TAKAN MIKE KAFARTA AWAJEN DA MANZO (SAWW) ZAI YI SUJJADA, IDAN YAZO SUJJADAR, YAKAN TA'BA TA SANNAN SAI TA NA'DE KAFAFUNTA IDAN YA GAMA SUJJADARSA KUMA SAI TA SAKE MIKEWA KAFAFUNTA"

Imam Ibnu Hajar ya fada acikin "FAT-HUL-BARY" sharhin Sahihul Bukhary, akan wannan hadisin cewar "WANNAN ZA'A IYA DAUKAR CEWAR AKWAI WANI ABUNDA YA RUFE QAFAFUNTA, KO KUMA KHUSUSIYYAH CE IRINTA MANZON ALLAH (SAWW).
Shi yasa shi alwalarsa ba zata karye ba. Koda yayi hakan.

Don karin bayani aduba:

1. Rahmatul-Ummah na Imamud-Damashqee (shafi na 13-14)

2. Subulus-Salam, Juzu'i na farko, Shafi na 101-103.

3. Tuhfatul-Ashraf Juzu'i na 13, shafi na 234.

4. MUSNAD na Imamu Ahmad bn Hambal, juzu'i na 1 shafi na 168 da kuma na 216.

5. Abu Dawud juzu'i na 1 shafi na 178-179.

6. SUNANUT-TIRMIDHY, Juzu'i na daya shafi na 86.

Wallahu A'alam.

No comments: