Friday, 8 February 2013

SOYAYYA A GIDAJEN HAUSA FULANI: Ba wanda ya jahilci cewa aure sunnar Manzon Allah ne tsakanin Musulmai, Amma da yawa ba su san yaya musuluncin ya karantar da morewa rayuwar aure ba, shi ya sa da yawa ake zaman doya da manja tsakanin ma’aurata a gidan malam Bahaushe, har wassu ke cewa : ai aure zaman hakuri ne. Ko da yake, Matsalolin gidajenmu suna da yawa, Amma zan dauki daya daga cikin ginshikan Zamantakewar Ma’aurata, wanda Allah cikin Qur’ani ya ambace shi a mastayin igiyar da ke rike aure tsakanin Miji da mata. So, ko Kauna wassu abubuwa ne da ba dole ne Mutum ya san yanda ya kamu da su ba, shi yasa Annabi yace “ Zuciyoyi Runduna daban daban ne, in wadanda suka dace da juna suka gamu sai su yi kawance, In kuma wadanda ba su dace ba suka gamu sai su yi baran baran” Wannan ya sa Addinin Musulunci ya kula da tabbatuwar kauna tsakanin Ma’aurata gabanin aure, Manzon Allah kuma ya rarraba auren da aka yi ba bisa kauna ba. Allah yace: “ Yana daga cikin alamun samuwarsa, yanda ya halitta muku mata daga danginku (‘Yan Adam), ya kuma sanya kauna da tausayi tsakaninku” Annabi kuma yace:” Ku auri Mata masu baiyana muku kauna masu haihuwa, don zanyi alfahari da yawanku ranar Qiyamah” Manzon Allah ya cewa jabir: “ Idan dayanku na neman aure, in akwai abin da zai kalla wanda zai kara jansa zuwa auren sai ya kalla” Wata mata mai suna Asma’u bnt Khidam ta zo gurin Manzon Allah tana mai cewa : babanta ya aura mata wani dan kaninsa don ya kara matsayinsa cikin dangi, Sai bakin da baya karya yace mata: In kin so In raba tsakaninku. In kuma kin hakura ki zauna da Mijinki. Manzon Allah ya raba aure tsakanin Uthman bn Maz’uun da iyalinsa, kamar yadda ya raba tsakanin Abdullahi dan Umar da Matarsa, duk sakamakon rashin cikekkiyar kauna da soyayya. Duk yanda ka kai wajen tsantseni, Allah ba zai kama Matarka da laifi ba, in ta baiyana rashin amincewarta kanka, saboda kaunarka bata sami gindinzama cikin birnin zuciyarta ba. Domin Kakakin Manzon Allah Thabit bn Qais bn Shammas, Matarsa ta kai kukansa gaban Manzon Allah tace ya Rasulallah: Mijina Thabit, bana aibanta addininsa ko dabi’unsa, amma ina tsoron komawa kafirci bayan na fito daga ciki, In na hangoshi cikin Maza, sai na hango shi ya gaza kowa ginin halittar jiki, Sai Manzon Allah yace: ta maida masa gonar da ya bayar a matsayin Sadaki, sai aka raba auren. ‘Yan uwana makaranta wannan Makalar, ba jigo cikin sakonnin da ta kunsa shine: kada iyayenki su tsoma ba kan wa za ki aura ba? A’a, Ina nufin Iyaye su yi kokarin gamsar da ‘yayansu kan Mazajen da ya dace su aura, domin cikin hadisi Manzon Allah yace: ‘’ Bazawara sai an nemi Izininta, Budurwa kuma za a yi kokarin yardar da ita” . Ko da yake abin da yafi watsuwa a kasarmu maganar Malam mai Risala da ke cewa: “ Uba yana da damar tilasta ‘yarsa karama” Yan uwa a kara nazari kan wannan maganar!!!! Abin takaici shine mafi yawa cikin soyayyar Ma’aurata a kasar Hausa tana tsayawa a kwararo ne, Bayan wajen wanzar da ita na hakika shine cikin gidajenmu. Dan uwana/’yar uwata mai karatun wannan makala ko kun taba koyi da Manzon Allah kan wadannan abubuwa da suka tabbata a hadisi cewa hakan ya faru tsakaninsa da iyalansa: • Yana furta kaunarsa da begensa ga iyalansa, Aka tambayeshi wa yafi so? sai yace Ai’isha. • Taje masa gemu da gashin kansa har a cikin masallaci. • Zama don cin abinci tare tare da bararrajewa tsakanin Matansa, domin Imamun Nasa’I cikin Ishratun Nisa’I ya rawaito cewa: ya dora cinyarsa daya kan cinyar Nana Safiyya dayar kuma kan ta Nana Aisha. • Wasan guje guje. • Zama don hira da tattauna labaran Duniya, kamar yadda ya ke cikin Hadisin Ummu Zarr. • Dora Mijinki a cinya don tarairayarsa da tallafa masa, kamar yadda yake a labarin jinyar Manzon Allah, • Taya iyalinka aiyukan cikin Gida, kamar yadda yazo cikin hadisin Nana A’isha. • Wanka tare har da cudar juna. ‘Yan uwana , Ma’anar Miji ko Mata ta gari ba ya takaita kan Mai tauhidi da Ilimi da Sunnah ba kawai, Shi yasa Manzon Allah da ya fassara Mata ta gari sa yace: “Itace wacce in ka kalle ta, za ta sanya maka farin ciki” Hakan kuwa zai faru ne ta hanyar sanin makamar tarairayar mai gida ta hanyar Tsabta, Baiyana kauna, Made, Tarairaya, Rangwadi, Rishi, Madarar Idanu in an cakudasu da girmama dokokin Allah. Wahayin Shaidan ne ga Matan Hausawa cewa wai Miji ba a mika masa kai bori ya hau, Kai kuma sai ya yaudareka da cewa wai Mata ba a mika musu kai sai su rainaka. A tawa mahangar, da yawa gidajen Hausawa suna talaucin zamantakewa mai armashi saboda duhun kai da jahilcin addini da yayi kanta a kwakwalen wasunmu. ALLAH YA TAIMAKA

SOYAYYA A GIDAJEN HAUSA FULANI:

Ba wanda ya jahilci cewa aure sunnar Manzon Allah ne tsakanin Musulmai, Amma da yawa ba su san yaya musuluncin ya karantar da morewa rayuwar aure ba, shi ya sa da yawa ake zaman doya da manja tsakanin ma’aurata a gidan malam Bahaushe, har wassu ke cewa : ai aure zaman hakuri ne.

Ko da yake, Matsalolin gidajenmu suna da yawa, Amma zan dauki daya daga cikin ginshikan Zamantakewar Ma’aurata, wanda Allah cikin Qur’ani ya ambace shi a mastayin igiyar da ke rike aure tsakanin Miji da mata.

So, ko Kauna wassu abubuwa ne da ba dole ne Mutum ya san yanda ya kamu da su ba, shi yasa Annabi yace “ Zuciyoyi Runduna daban daban ne, in wadanda suka dace da juna suka gamu sai su yi kawance, In kuma wadanda ba su dace ba suka gamu sai su yi baran baran”

Wannan ya sa Addinin Musulunci ya kula da tabbatuwar kauna tsakanin Ma’aurata gabanin aure, Manzon Allah kuma ya rarraba auren da aka yi ba bisa kauna ba.

Allah yace: “ Yana daga cikin alamun samuwarsa, yanda ya halitta muku mata daga danginku (‘Yan Adam), ya kuma sanya kauna da tausayi tsakaninku”

Annabi kuma yace:” Ku auri Mata masu baiyana muku kauna masu haihuwa, don zanyi alfahari da yawanku ranar Qiyamah”

Manzon Allah ya cewa jabir: “ Idan dayanku na neman aure, in akwai abin da zai kalla wanda zai kara jansa zuwa auren sai ya kalla”

Wata mata mai suna Asma’u bnt Khidam ta zo gurin Manzon Allah tana mai cewa : babanta ya aura mata wani dan kaninsa don ya kara matsayinsa cikin dangi, Sai bakin da baya karya yace mata: In kin so In raba tsakaninku. In kuma kin hakura ki zauna da Mijinki.

Manzon Allah ya raba aure tsakanin Uthman bn Maz’uun da iyalinsa, kamar yadda ya raba tsakanin Abdullahi dan Umar da Matarsa, duk sakamakon rashin cikekkiyar kauna da soyayya.

Duk yanda ka kai wajen tsantseni, Allah ba zai kama Matarka da laifi ba, in ta baiyana rashin amincewarta kanka, saboda kaunarka bata sami gindinzama cikin birnin zuciyarta ba.

Domin Kakakin Manzon Allah Thabit bn Qais bn Shammas, Matarsa ta kai kukansa gaban Manzon Allah tace ya Rasulallah: Mijina Thabit, bana aibanta addininsa ko dabi’unsa, amma ina tsoron komawa kafirci bayan na fito daga ciki, In na hangoshi cikin Maza, sai na hango shi ya gaza kowa ginin halittar jiki, Sai Manzon Allah yace: ta maida masa gonar da ya bayar a matsayin Sadaki, sai aka raba auren.

‘Yan uwana makaranta wannan Makalar, ba jigo cikin sakonnin da ta kunsa shine: kada iyayenki su tsoma ba kan wa za ki aura ba? A’a, Ina nufin Iyaye su yi kokarin gamsar da ‘yayansu kan Mazajen da ya dace su aura, domin cikin hadisi Manzon Allah yace: ‘’ Bazawara sai an nemi Izininta, Budurwa kuma za a yi kokarin yardar da ita” .

Ko da yake abin da yafi watsuwa a kasarmu maganar Malam mai Risala da ke cewa: “ Uba yana da damar tilasta ‘yarsa karama” Yan uwa a kara nazari kan wannan maganar!!!!

Abin takaici shine mafi yawa cikin soyayyar Ma’aurata a kasar Hausa tana tsayawa a kwararo ne, Bayan wajen wanzar da ita na hakika shine cikin gidajenmu.

Dan uwana/’yar uwata mai karatun wannan makala ko kun taba koyi da Manzon Allah kan wadannan abubuwa da suka tabbata a hadisi cewa hakan ya faru tsakaninsa da iyalansa:

• Yana furta kaunarsa da begensa ga iyalansa, Aka tambayeshi wa yafi so? sai yace Ai’isha.

• Taje masa gemu da gashin kansa har a cikin masallaci.

• Zama don cin abinci tare tare da bararrajewa tsakanin Matansa, domin Imamun Nasa’I cikin Ishratun Nisa’I ya rawaito cewa: ya dora cinyarsa daya kan cinyar Nana Safiyya dayar kuma kan ta Nana Aisha.

• Wasan guje guje.

• Zama don hira da tattauna labaran Duniya, kamar yadda ya ke cikin Hadisin Ummu Zarr.

• Dora Mijinki a cinya don tarairayarsa da tallafa masa, kamar yadda yake a labarin jinyar Manzon Allah,
• Taya iyalinka aiyukan cikin Gida, kamar yadda yazo cikin hadisin Nana A’isha.

• Wanka tare har da cudar juna.

‘Yan uwana , Ma’anar Miji ko Mata ta gari ba ya takaita kan Mai tauhidi da Ilimi da Sunnah ba kawai, Shi yasa Manzon Allah da ya fassara Mata ta gari sa yace: “Itace wacce in ka kalle ta, za ta sanya maka farin ciki”
Hakan kuwa zai faru ne ta hanyar sanin makamar tarairayar mai gida ta hanyar Tsabta, Baiyana kauna, Made, Tarairaya, Rangwadi, Rishi, Madarar Idanu in an cakudasu da girmama dokokin Allah.

Wahayin Shaidan ne ga Matan Hausawa cewa wai Miji ba a mika masa kai bori ya hau, Kai kuma sai ya yaudareka da cewa wai Mata ba a mika musu kai sai su rainaka.

A tawa mahangar, da yawa gidajen Hausawa suna talaucin zamantakewa mai armashi saboda duhun kai da jahilcin addini da yayi kanta a kwakwalen wasunmu.

ALLAH YA TAIMAKA

No comments: